← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 168

Sashe 58

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarasawa tayi gaban madubi tana kallon kan ta, Alhamdulillah ba ta rasa ci, sha, sutura kai har ma da kuɗin biyan buƙatu ba, a shekarun nan da suka ƙaru har da jikin ta ma ya sauya, dan yanzu ita ɗin fa uwar dake mallake da shekara *talatin* ce cif a duniya, ta ƙara tsayi, ta ƙara ƙiba sannan fatar ta ta ƙara haske na cima mai kyau da kyakyawan muhalli. Hannu tasa ta shafi kanta dake ɗauke da ƙananan kitso ta shafa tare da faɗin "Ba komai, kawai dai kaina ne yake ɗan ciwo, amma na sha magani."

Cike da kulawa yace "Ayya! Sannu amaryata, to kin ga kwanta ki huta, amma dai ina fata kin ci abinci?"

Yatsina baki tayi dan ita wallahi bata jin daɗin yanayin ta, ina ma Kuwailat ta bar ta ta kai ƙarshen mafarkin ta, ita bata ma san da wa take tare ba, kawai dai ta ga kanta a wata duniya da take fatan ziyarar ta a zahiri, a ƙasan maƙoshi ta amsa da" Um um, gashi can Kuwailat na dafawa."

Murmushi yayi dan yasan Kuwailat É—in ai za ta iya, tunda ta fara zama budurwa, dan haka yace" Shikenan to, idan kin ce sai ki kwanta ki huta, amma kafin nan albishirin ki?"

Da sigar ƙaguwa ta amsa da" Goro."

Da fara'a ya ce mata" Anjima zamu taso, dan haka kiyi shirin tarbata."

Ba ta so yin doguwar magana da shi ba, amma shirin tarban shi da ya faÉ—a yasa mamaki bayyana a fuskar ta har ta maimaita" Shirin tarban ka?"

Dariya yayi wacce har saida ta ji sautin ta yace" E mana, na miki bazata ko? Dama ai haka nake so, ki shirya ke dai, sai na zo in sha Allah."

Yanke kiran yayi Ummu na kallon kan ta a madubi, tsabar takaici yasa har idanun ta suka cika da hawaye, da ƙarfi ta aje wayar gaban madubin tare da shugewa ban ɗaki dan tayi wanka tayi alwala tayi sallah azahar da ake daf da fara kiran ta.

A tsanake tayi wanka ta fito ta shirya cikin kayan da ta fi sha'awa a rayuwarta wato duguwar riga musamman ma abaya, rigar wani tattausan yadi ne jikin ta mai maɗauri a baya, saida tayi sallah ta shafa sahihun turarukan da bata iya rabuwa da su a rayuwar ta wato na *gidan ƙamshi* da Hajia *Fussam* ke siyarwa, abun daɗi ga kayan ta shine hatta turaren da mace zata yi anfani da shi yayin zuwa wajen oga da shafawa dan fita gama-gari tana da, yadda Ummu tayi mugun sabo da turarukan tana ji a jikin ta idan aka ce yau ta kasa samun turaren nan to zata shiga babbar matsala, dan kuwa turaren Hajia Fussam *maƙura* ne, turaren Hajia Fussam *ƙarshe* ne, turaren Hajia Fussam *duniya* ne da duk macen da ta san kanta ya dace ta ƙulla abota da su dan kankaro na ta mutumcin, wani abun sha'awar kuma shine, in dai da turaren ta kike anfani, to da wuya ki haɗu da wata mai irin ƙamshin turaren ki, sai dai idan ita ma a wajen ta take siyayya.

Sallah ta gabatar kafin ta cire hijabin ta ta fita falon, Kuwailat ita kaɗai ta samu zaune tana kallon tashar Manara da kuma littafi a hannun ta tana karatu sannan tana kallo, saida ta ƙarasa ta ɗauki remonte ta kalle ta tace "Kin yi sallah?"

Da raha yarinyat tace "E Ammie, kin fito?"

Saida tayi nufin zama a kujera sannan ta amsa da "Um, kin yi girkin?"

Da fara'a a fuskar ta da sakewa alamar dake nuna ƙawaye ne su ɗin tace "E Ammie, tunda kika ce nayi ai dole nayi, na kawo miki ne?"

Amsar da Kuwailat ɗin ta bata yasa ta yin murmushin da ya fito da haƙoran makkarta duga biyu ta girgiza kai tace "Sai anjima zan ci."

Cikin shagwaɓa Kuwailat ta turo baki tace "Ammieeee..., Abba fa ya ce na kula dake kafin ya dawo, kuma ya ce so yake kiyi ƙiba, amma ba kya cin abinci tunda ya tafi."

Ƴar harara ta aika mata tace "Ke, bana son iskanci."

Dariya Kuwailat tayi tace "Shikenan, amma zan sanar da Abba idan ya dawo."

Girgiza mata kai tayi tare da faÉ—in "ÆŠauko min wayata É—aki."

"To Ammie." Ta faɗa tana miƙewa da sauri, shigar ta ke da wuya Hajia Atika ta shigo ɗakin da wata sallama ciki-ciki cike da raini da wulaƙanci.

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes.

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata.

Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._

_Bismillahir-rahamanir-rahim._

*28*

Ko dan yau bata yanayin farin ciki? Sai kawai take ji a ranta yau ba zata saurarawa Hajia Atika ba, basu taɓa haɗuwa da matar nan ba tare da ta ce ga abinda Ummu ta mata ba, ta nuna mata ƙiyayya tun tana amarya, ta sha masifa da bala'in matar nan har yanzu ma da take shigowa ita tasan ba alkairi bane ya kawo ta, musamman da ta ganta cikin shiri irin na fita sannan sai wani saɓa mayafi take, fuskar nan kuwa tsaf da kwalli har da su hoda, duk da fa shekaru sun ja sosai yanzu, amma ƙarfin guiwa da kwalliyar ta na birge ta sosai, dan bata yarda shekaru, ɗiya da jikoki sun hana ta yin ado da kwalliya ba.

Kamar yadda tayi sallamar ƙasan maƙoshi hkaa ita ma Ummu ta amsa, sai dai da sakin fuska har da faɗin "Aunty, ke ce tafe? Ƙaraso ?"

Ba ta amsa mata ba sai yatsina fuska da take har ta zo gaban ta ta tsaya nesa da ita, ba komai da komai hannu kawai ta tara mata tace "Bani makullin motar Alhaji zan fita."

Da mamakin buƙatar da Hajia Atika ta zo da ita ta kalle ta sosai tace "Motar Alhaji kuma aunty? Ta ki fa?"

Saida ta kawar da kai sannan tace "Ta wa ta samu matsala, na kira za'a zo a duba min, bani sauri nake."

Ba tare da ta tashi daga inda take ba ta kalle ta ita ma tace "To aunty na baki, shine ya ce na baki? Ni gaskiya bana son matsala, haka waccen lokacin kika ce a ba Hayat aki aike shi, ya je ya samu matsala da motar nan, da Alhaji ya zo wallahi ni ya ma faɗa, dan haka ma yanzu da zai bani shi tunda ai ranar girkina ne ya tafi saida ya min gargadin kar a taɓa mishi mota."

Wata irin tsayuwa tayi da yanayin jin bala'i tace" Me kike nufi ? Ba zaki bayar ba ko me?"

Girgiza mata kai tayi sanda Kuwailat ke fitowa ɗauke da wayar ta tace" A'a aunty, ki kira shi dai, idan ya ce a baki wallahi take zan baki, amma idan bai ce ba sai kiyi haƙuri."

A zafafe tace" Ba zan kira shi ɗin ba, kema ai kin san Alhaji ba bari yake ana taɓa mishi mota ba, ki bani kawai zan je in dawo ne sai ya zama matsala, dan kin ga à hannun ki take ? Da ke ce kika buƙata ai sai dai mu ga zaki fita da motar tunda ke ce matar so."

Girgiza kai Ummu tayi ta kalli Kuwailat, suna haÉ—a idanu da ido ta mata alamar ta shiga madafa, da sauri ta nufi madafar tana kallon Hajia Atika, saida ta ga shigar Kuwailat sannan tace" Aunty, ni dai ba rigima nake so muyi ba, ga wayata ma zan iya kira miki Alhajin, idan ya ce na baki ni banda matsala da hakan."

Cikin ɓacin rai Hajia Atika tace "Bana so, karki ki kira shi, ko kin fini sanin lambar shi ne? Ai ni dama nasan za'a rina, ke dai wallahi ki ji tsoron haɗuwar ki da Allah, tunda Alhaji ya aureki duk kin mallake shi, komai nashi ke ce kamar je kaɗai ya mallaka, daga ke sai ƴar ki yanzu kuke yadda kuke so a gidan nan, gaba ɗaya kin susuta ma Tsoho nutsuwar shi, hatta yaran shi idan suna son abu gare shi sai dai su bi ta hannun ki idan suna so su samu, mtssss! Ke da Allahn ki."
Chapter 58 · 0% Book details