Sashe 32
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Bai taɓa jin nadaman neman mata da yake yi ba sai yau, dan kuwa ganin hakan yake ba matsayin maganin matsalar shi dan kar ya halaka, ruwa ne suka cika idanun shi taf yana duban Hajian da ita ma ke kallon shi yace" Hajia... Ta ya? Ta ya zan iya aikata wannan aikin da yarinyar da ba ta fi tsarar Leila ba? Hajia ko auren ta nayi a wannan shekarun nata ni mai kawar da kaine daga gareta har sai ta zama cikakkiyar mace, amma a haka...yarinyar da ke kirana da *Abbu*? Hajia kallon fa uba take min, ta ya to zan yarda sheɗan yayi galaba a kaina game da lamarin ta? Bayan kuma ita ɗin *ƴata ce*."
Hajia ma saida ta ji ƙwlla a idanun ta, dan haka ta sa hannu ta ta share tana jan majina tace" Shikenan Sa'ad, na yarda da kai ɗari bisa ɗari, kuje Allah ya tsare."
Har ta juya za ta koma ya riƙo hannun ta ta juyo, cikin kallon idanun ta yace" Na miki alƙawarin sanar dake komai Kaka idan muka dawo daga asibitin, in sha Allah, kuma Hajia zan sanar da ke ne saboda ban da abokiyar hira a gidan nan bayan ke, kuma bana so ki yi hushi da ni ko kema ki aje ni gefe, dan Allah kakata?"
Zuba mishi idanu tayi tana kallo tace" Sa'ad, ba dai wani mummunan abu bane ko?"
Girgiza kai yayi yace" Zan sanar dake Kakata, kar kiyi hushi dani."
Jinjina kai tayi tace" Shikenan Sa'ad, ba zanyi hushi ba."
Murmushi yayi ya saki hannun ta, juyawa tayi tana cewa" Bari na turo maka ita."
Yana kallo ta shiga falon, sai dai labulen daya rufe ɗakin ya sa bai iya ganin komai sai fitowar Aisha tana ƙara gyara gyalenta a saman kai, juyawa yayi ya nufi inda motar shi take dan ya san za ta ƙaraso.
Yana buɗe ƙofar mota zai shiga muryar Alhajin Ibrahim ta daki kunnuwan shi wanda ya jima da shogowa gidan wata muhimmiyar waya ta tsayar da shi nan yana faɗin "Ina wuni Baba *Usmanu*?"
Dakatawa Sa'ad yayi ba dan yasan da shi ake ba, amma da yaga mahaifin sa ne ke tahowa kuma tabbas shi yake nufi sai ya fahimci wai Gatse ne yake mi shi? Gani yake ya gan shi ƙyale shi ne yayi? Duba da Aisha dake tahowa kuma baya so ta san komai dake faruwa a gidan nan har sanda zai sa a mata aiki a rabata da cutar da ke cikin ta sai ya tausasa murya har ma da kanshi a ladabce yace "Ina wuni Ibu?"
Alhajin dake tahowa da yanayin ɓacin rai saida ya zo kusa da shi sannan yace "Sa'ad, yanzu dan rainin wayo ni ina gidan nan amma ka ganni ba za ka iya gaishe da ni ba? Saboda kawai ka nuna ni banza ne a wurin ka?"
Ɗan waigawa yayi kaɗan ya ga Aisha na tahowa ƙiris ya rage ta ƙaraso, da sauri ya kalle shi yace "Ku yi haƙuri, ban kula da mutum a wurin bane."
Kamar mai neman shi da faɗa sai kuwa ya ɗaga murya yace "Ƙarya kake, ban san ka bane da zaka gaya min haka? Zan iya yin tafiya na kwashe watanni bana garin nan, faɗa min rana ɗaya da idan na zo kake shiga sahun masu zuwa gaishe ni."
Ƙyaƙyabta idanu yayi alamar ba komai ɗin nan sannan ya sake cewa "Ka yi haƙuri, zan kiyaye."
Aisha da ta ƙaraso da ladabi da kuma fara'a duba da duk gidan bayan Hajia da Leila shine mutum na uku dake sakar mata fuska, cikin taushin murya tace "Ina wuni Papi, sannu da dawowa?"
Kallon ta yayi yana murmushi sosai cikin kulawa yace "Yawwa Aisha, kina lafiya?"
Da rusunawa ta amsa da "Lafiya lau."
Da kulawa ya sake cewa "Ina na za ki je na ganki da lulluɓi haka?"
Cike da kunya ta ɗan kalli Sa'ad da ya shiga mota yana ƙoƙarin rufe ƙofar tace "Abbu ne ya ce na raka shi asibiti."
Take ya haɗe walwalar dake fuskar shi saboda jin wani bahagon zance, ganin Aisha ta zagaya ta buɗe mota yasa shi saurin buɗe ƙofar da Sa'ad yake, a zafafe ya damƙo hannun shi ya fito da shi daga cikin motar yana kallon shi yace" Wace asibiti za ku je? Wa ye ba lafiya? Me kake shirin aikatawa?"
Hawa masa kai yake! Hassala shi fa yake! Ƙoƙarin kai shi bango fa yake? Duk a kan me? A kan me ne? Da fari fizge hannun shi yayi yana mishi wani kallo tare da faɗin" Dukan mu ne ba lafiya, shikenan?"
Cikin ɓacin rai ya sake kama murfin zai shiga Alhaji ya jawo wuyan rigar sa ya dawo da shi baya yana cewa" Kai dakata bana son ƙananan iskanci, me za ka je ka yi wa ƴar mutane? Ka san da tana zaune gidan nan ne dan kace bata da kowa."
Cikin wani irin tafasar zuci da ɓacin rai Sa'ad ya sake fizge wuyan rigar sa yana faɗin" Sai me to? Zan fita da ita Ibu kuma zan yi abinda na ga dama da ita, kana da matsala da hakan ne? Haba! Haba! Ya kake so da ni ne?"
Girgiza kai Alhajin yayi yana taɓe baki a sanyaye yace" Idan ka yi haka kuwa ka cika cikakken marar martaba mata, dubeta fa yarinyar?"
Irin kallon nan na raini da murmushi a fuskar Sa'ad ya dinga yi yana kallon Alhajin da saida ya ji ya tsargu ya kuma yi dana sanin faÉ—in wannan maganar, hakan yasa shi kawar da kai irin yana so a basar É—in nan, Sa'ad kuma ba tare da tsoro ko shakka ba yace "Ibu, kai ne za ka wa wani magana akan sanin martabar mace?"
Sai kuma ya sake yin murmushi har da sauti yana girgiza kai, maida ƙofar motar yayi ya rufe ya sake matsawa daf da shi yace "Idan ma haka nake, to ina ga ai sawun baya nake takawa, kasan kuma an ce Barewa ba zata yi gudu ba ɗan ta yayi rarrafe, kar ka manta Ibu a gaban idanu na kake ɗauke fuskar mahaifiyata da tafin da har jini ke ɓalle mata a hanci, Ibu, da wayona casss ka sakar min uwata saki ɗaya saboda kawai budurwar ka ta kira ka ita kuma ta ɗauka har sukayi cacar baki, Ibu, ka daina taƙala dan bana so ina tuna abubuwan da suka gabata wanda ni da kai duk hakan baya mana daɗi."
Da ƙarfi ya jawo murfin motar ya buɗe ya shiga ya bar shi nan tsaye yana kallon shi, har suka fita daga gidan bai gusa ba sai da ya gaji da tsayawa da Takaicin baya da irin abubuwan da ya aikata.
*Suna* ɗaukar hanya ta ɗan saci kallon shi ganin sai huci yake yana dantse leɓe alamar ɓacin rai ƙarara, gabanta ta kalla cikin son mantar da shi abinda ya ɓata masa rai tace "Abbu, ni kuwa yaushe za ka yi aure ne? Na ga burin Hajia kenan."
Æacin ran da yake ciki ba zai bar shi ya Æ™yaleta ba, dan haka a tafashe ya amsa mata da "Ki min, tunda kin gaji da yawon da nake a gaban ki."
Cike da shashantar da abun tace "Lahhh! Abbu, ni fa ba haka nake nufi ba."
Da yanayi irin na mata ya koyi muryar ta cikin masifa yace "Lahhhh! Abbu..." Sai kuma ya koma muryar shi ta maza yace "Kika sake kirana Abbu sai na taka wuyan ki, tunda ke ba kya fahimtar yaren bakina."
Ya sauke maganar yana ta ci gaba da huci kamar wanda ya haɗiyi kububuwa, a raunane Aisha ta jinjina kai cikin shagwaɓa tace "Allah ya baka haƙuri, amma Abb..."
Birkin da ya taka saboda Abbun da ta sake faɗa ya sa ta dakatawa, kafin ta ankara kuma ya ɗago hannun shi ya nufi fuskar ta da niyyar gaura mata marin da zata gane me yake nufi, to amma rashin sabo da kuma yadda Aisha ta tsorata tayi wuffff! Da hannun da ya ɗaga ta rintse idanu har da ƙwala ƙara sai ya tsaya kamar wata Mage mai bacci yana kallon ta, ganin ta ƙi sakin jikin ta haka ma bata buɗe idanu ba yasa shi furta "Sake min hannu?"
A hankali ta saki hannun ta manne a jikin ƙofar motar tana satar kallon shi, saida ta ji ya tayar da motar sun ci gaba da tafiya sannan ta saki jikin ta, ba ta ƙara cewa komai ba dan gaskiya ba ta son duka, sam ba ta son haɗa hanya da duka, ta ga kuma a yadda yake din nan yau so yake ƙarfi da ya ji sai ya taɓa mata lafiyar jikin ta.
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*15*
Kai tsaye ya ga likitan da dama da shi suka shirya ana kawo Aisha shi zai mata aiki, yanzu haka suna zaune yana kallon Aisha har ya zauna kan kujerar shi yana cire safar hannun shi tare da cewa "Ya sunan ki?"
Tana sunkuyarda kanta da tunanin me yasa yake ta kallon ta sannan baya duba Abbu Sa'ad ta bashi amsa a tausashe da "Nana Aisha."
Ba tare da ya É—auke idanun shi daga kanta ba yace "A'isha, shin kina jin wani abu a jikin ki haka?"
Kallon shi tayi da mamaki a fuskar ta na me ya haɗata da wannan tambayar kuma? Sa'ad ta ƙalla da kujerar shi ke fuskantar ta ta kujerar, ya jingina a kujerar nan ya rufe bakin shi da yatsun shi uku kawai ya zubawa fuskar ta idanu yana kallo, turo baki tayi ta bishi da kallo _"Ya haka kuma Abbu?"_
A sanyaye sosai ba tare da ya ɗauke hannayen shi ba yace" Ki bashi amsa, kar ki ɓata min lokaci."
A shagwaɓe ta kalle shi cikin sassauta murya tace" Abbu, me yasa sai kayi ta yi min faɗa? Ni ai ba ni ka ce za ka kawo asibiti ba ko?"
Ƙura mata idanu yayi kawai yana kallo dan yanzu bai shirya yin magana ba, dan haka kallon gargaɗi kawai yake bin ta da shi, da irin jin haushin nan ta kalli likitan tace" Ba na jin komai."