← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 168

Sashe 35

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da takaici Fa'iza dake zaune ta Taɓe bki tace" Ai ko da goma ta lalace ta fi biyar albarka, wanda ya rigaka kwana kuma dole ya rigaka tashi, ki sani *wata kokawar* ba sai kai abokin karawar ka ƙasa bane ya zama kayi nasara, ni kuma na fi ƙarfin taka sawuna bayan naki sawun, hakan yasa nake buga *lissafina a cikin taki ƙwaƙwalwar*, ki kiyaye, dan da alama baki taɓa gani ko a documantary ba cewa barewa na iya daka tsallen ya son ranta a gaban *zaki* ma kuma ta kuɓuta, bare kuwa wata halitta wai *damisa* da ba'a halicceta da jinin *halacci* ba."

Cike da wani irin makirci Abida tayi murmushi tace" Shikenan, zan ga ta inda lissafin ki zai ci na wa lissafi, duba da shekaru nayi ina buga nawa équations ɗin, dan kawai naga na gagari tunanin mai tunani."

Ba tare da ta motsa daga inda take ba ta saki murmushi ita ma tace" Kin manta da ko jami'in sirrin sirrintaka yana kwaɓar da alamar da za'a iya gane shine, bare kuma ke da bana jin kin fita daga ajin da ni na jima da wucewa? Ba komai, muje a haka dan ina so naga mamaki a fuskar ki, amma ki sani sirrin da kika binne shekaru sha bakwai da suka wuce, *ni nan* zan sake busa masa rai sannan na tono shi kowa ya gani."

Gaban ta ya faɗi sosai, kuma ta ji jinin jikin ta ya tsinke, amma saboda kar ta nuna mata wata alama da zata bata ƙofar zargin ta sai kawai tayi dariya ta ɗan taka gaba kaɗan tana faɗin" Zan gani, zan kasance cikin jiran ganin haka ta faru, ko ba komai nasan zan yi dariyar ganin rashin nasarar ki."

Idanu Fa'iza ta zuba mata ta bi ƙeyar ta da kallo tana murmushi tace" Za ki gani kuwa... *ABIDA HAMBALI YA'U*."

Juyowa Abida tayi da murmushin izgilanci tare da" Alhamdulillah, nawa mahaifin shahararre ne har a ƙasar waje ma."

Gyara zama kaɗan Fa'iza tayi da murmushi tace" Hakane kam, tunda shine mammallakin asibitin HY...haka ma gidan marayun HY, gidajen da ba kowa ya san sirrin dake danƙare a ƙarƙashin fondation ɗin ginin ba, sai waɗanda suka kasance maƙura a kusanci da shi gyatumin."

Fa'iza bata fahimci Abida ta shiga halin rudu da ɗimuwa bane? Ko ta fahimta tana so ta sake samun wasu makamai ne a hannun ta na ci gaba da yaƙar Abidar? Ba dan haka ba irin ƙwalalo idanun da Abida tayi, sannan fuskar ta ta rikiɗe har jikin ta ya ɗauki wani ɓari ɓari ko wanda bai san komai ba zai gane akwai matsala... Ta ya tasan asibitin da gidan marayun duk na mahaifin ta? Ta ya kuma tasan akwai wasu sirrika a wannan gidajen? Ita kanta bata san su ba sai ƴan tsirarun shekarun da suka gabata da basu fi biyu zuwa uku ba, shi ma ta sani ne lokacin da Maman ta ta dage sai mahaifin su ya sake ta, da suka sakata gaba da tambaya ne take faɗawa ita Abidar dake mace cewa ga abinda ta gano yana aikatawa a can inda ya fi zama, shiyasa take so ta rabu da shi dan ba zata iya zama da azzalumi ba.

Cike da shaƙiyanci Fa'iza ta miƙe ta kalli matashin nan da sam babu haɗi ta fuska ko fata tsakanin shi da Abida, dan da alama yaron ɗan buzaye ne na gaske, fatar shi jajir take kamar karas, cike da son ƙular da ita tace "Wannan shi kuma ƙanin ki ne? Amma dai uba ne uwa ce ɗaya ko? Ko da yake..."

Sai kawai ta nufi hanyar nata falon tana faÉ—in "Akwai Æ´an uwa na nesa, ba lallai shi wannan na kusa bane."

Suna kallo ta ɓacewa ganin su ba wanda ya iya dakatar da ita, dan ko matashin nan da bai san komai ba akan abinda suka tattauna, sai da ya ji a ran shi lallai akwai ƴar tsama tsakanin matan nan ba kaɗan ba, kuma a yadda ya fahimta kamar waccen matar ta fi Abida salo da iya tako, dan kuwa Abida ko ba komai ai ita ta fara mata magana, gashi yanzu ta sossoka mata magana son ranta ta bar su tsaye.

Fuuuuuu! Abida ta wuce nata falon tana kai da kawo da zazzaro idanu na mamakin ya aka yi Fa'iza ta san batu akan asibitin da kuma gidan marayun? Ya aka yi haka? Hakan na nufin kenan ta san komai ɗin da take shiryawa? Hakan na nufin Fa'iza za ta iya nasara a kan ta kenan? Kai... Kai! Ba zai yiwu ba gaskiya, da ƙarfin gaske ta daki teburin gaban ta har da faɗin "Wallahi ba zai yiwu ba, ba zan bari ta tona min asiri baaaaaa!"

Yadda ta ƙarashe maganar da ɗaga murya yasa matashin tsorata, sai yake ganin kamar wannan ɓacin ran nata ba zai bar shi yayi abinda ya kawo shi gidan ba, shi kuma a kowace safiya mafarkin future rayuwar shi yake, addu'a yake burisu shi da ita ya cika, ita ta samu abinda take so shi ma ya samu nashi abinda yake da buƙatar.

Gudun kar ya koma ba tare da komai ya wakana ba ya sa matashin nan cike da shaƙiyanci da fitsara ba tare da duba shekarun Abida sun ruɓanya nashi ba, ko da yake ita ta ja ma kanta, hasalima ita ta zaɓeshi a haka dan cikaro burin ta, kuma a haka ita ke biyan shi kafin gwagwaɓan biyan da tayi alƙawarin yi masa idan har ta samu abinda take da buƙatar. Cire da ƙwarewa da shashanci ya jawo ta jikin shi tare da ƙoƙarin dawo da kallon ta ga fuskar shi... Cikin ɓacin rai take son fizgewa har tana faɗin "Mtssss! Sake ni dan Allah, kai bak..."

Sanin lagon ta ya sa matashin nan zura harshen shi cikin bakin ta idanun shi na kallon nata idanun a tsatsaye, a hankali ya riƙo hannun ta ya sauko da shi kan abinda ta sha gaya mishi tana so ya fi haka girma, cimma wannan faɗan nata kuma yasa sukayi wata basu haɗu ba sai yanzu da ya tabbatar ya samu yadda take so, dan kuwa shaye shayen duk abinda ya san zai ƙara mishi girman daraja ya dinga yi har yanzu da shi kanshi girman nata da riƙewar ta ke bashi tsoro, dan ga duk mai hankali yana ganin shi yasan ba asalin shi bane kawai dubaru ne.

Jin abinda hannun ta ya taɓa sai kuwa Abida ta zaro idanu tayi saurin jaye bakin ta daga nashi ta kalli ƙasan tace "Kai ne! Da gaske kai ne *Hashim*? Wow ! Ka yi min yadda nake so wallahi, wannan ai..."

Sai kuma ta durƙusa ƙasa jikin ta har rawa yake ta cire mishi zif ɗin wandon cike da jaraba ta jawo shi tana kallo har wani gwale ido take uwa ɗiyar mayya, dariya tayi tace" Wow! Kai kayan nan a haka harka ne wallahi, ka ganka kuwa? Ƙarami sai kayan ladabtar da mace."

Kamar yadda suka saba haka ta ja shi zuwa ɗakin baccin ta inda mijin ta ke shiga yayi tashi wadaƙar suka dinga masha'arsu da ƙaramin ƙanin ta dan kawai ta ga ita ma ta kafa tarihi a Ahalin Ahlan, sannan ta ga tayi fintinkau wa kishiyar ta, sam ba tayi tunanin abinda zai iya biyo wa baya ba, tunanin yanzun kawai take yi.

*A Gurguje*

Yaya Luƙman ta fara haɗewa da shi a ƙofar gidan, da fara'a da shaƙuwa ya tarbe su yana musu sannu da zuwa, Alhaji Kabir ba tare da girman kai ko wani abu ba ya bashi hannu suka gaisa, har yana tambayar shi karatu? Da zolaya ya kai hannu zai karɓi kwanon dake hannun Ummu Kulsum ɗin yana cewa "Kawo na ɗaukar miki ƙanwata, kar Mama ta ga na bar ki da kaya ta dakeni."

Murmushi Ummu tayi, yarinya ce da ke da miskilanci ba ta da hayaniya da yawon surutu, hakane ma ya sa a taƙaice kawai tace mi shi "Yaya kenan."

Alhaji Kabir kuma cike da zolaya da dattako yace "Ai ko Luƙman kayi kyan kai, kaga ni ban yi wannan tunanin ba, ashe da ni za ta sa a ma dukan."

Faɗaɗa murmushin ta tayi cikin shagwaɓa tace "Ni dai ka daina bana so."

Shiga ciki sukayi Alhaji da Luƙman na hirar su suka shiga da sallama, Mama da Mujittafa dake cin abinci suka amsa suna musu maraba, Mujittafa kujera ya ɗauko ma Alhaji ya aje ya zauna suna gaisawa da Mama, inda Ummu ta zauna kan tabarmar da Mama ke zaune da wata yarinya gaban ta ita ma tana cin abinci da bata fi shekara uku ba, har suka gama gaisawa Ummu dake ta duban yarinyar da bata sani ba tace "Mama, wannan kuma ƴar wacece? Ban san ta ba."

Da fara'a cikin sassauta murya Mama ta ƙara tura kwanon abincin gaban yarinyar tace "Jiya aka kawo min ita ta ɓata, ita kaɗai aka samu tana ta kuka, gata nan dai ina jira na ji masu cigiyar ta sai na miƙa musu ita."

Murmushi Ummu tayi tana kallon Maman tace "Allah sarki Mamana, kina ɗaukar kowane yaro dake duniyar nan a naki, ba kya ƙamar ɗan kowa bare ki kasa riƙe shi fiye da yadda zaki riƙe naki."

Murmushi Maman tayi ba tace komai ba, sai Mujittafa dake ta yanka lomar tuwo bakin shi yace "Ki bari kawai aunty, Mama fa ina ga har addu'a take yaro ya ɓace."

Dariya suka kwashe da ita har Alhaji Kabir, sai Ummu da tayi murmushin da ya bayyanar da haƙoranta, hakan yasa Mujittafa yace "Allah kuwa, to yaro na ɓacewa za ta yi ram da shi ta fara raino."

Juyawa Mama tayi ta kalle shi ta mishi daƙuwa, hakan yasa ya kalli kwanukan da Luƙman ya aje gaban Mama yace "Yaya Luƙman, ɗan miƙo min abincin gidan aunty Ummu in ji?"

Cikin jin haushi Mama ta kalleshi, haka ma Luƙman da Ummu da saida ta Harare shi, cikin halin ko in kula yace "Kuyi haƙuri to, naga ai ban taɓa zwa gidan ta ba bare na ci abincin ta, kuma duk zuwan da take bana nan kuma ba'a aje min."
Chapter 35 · 0% Book details