← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 168

Sashe 47

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya shiga ruɗani sosai, amma Wani irin dace da aka yi kasa kawai ya yi gefe da ruɗanin yana wasu tunanin na daban, kenan Hambali ƴar shi na aure a gidan su Eesha? Zai iya yiwuwa ita ma ba ta ƙwarai bace kamar uban? Ko da yake kawu ya faɗa, to ya zaman Aisha a yanzu? Idan kawun shi su suka ɗauke Yayar Eesha, to wa ya ɗauke ita kuma Eesha? Tabbas dai a gidan nan akwai bara-gurbi.

D hanzari Sa'ad ya kalle shi yace "Kawu, ka kwantar da hankalin ka, ka ci gaba da neman gafarar Allah, a yanzu ba abinda kake buƙatar kamar samun yafiyar mutanen nan, idan suka yafe maka zaka samu nutsuwa, bugu da ƙari idan aka ga yarinyar."

Da mamaki mai cike da tsoro kawun yace "Yafiyar su? Ta ina zan gansu? Da wane ido zan kalle su Sa'ad? Ba zan iya ba."

"Zaka iya kawu." Ya faÉ—a yana tsare shi da idanu sannan ya É—ora da "Zaka iya Kawu, yadda ka faÉ—a min komai yanzu haka zaka faÉ—a musu, babu abinda zai faru kawu."

Zuba mishi ido kawai yayi yana kallo kafin yace "Kai kuma a ina kasan Hambali?"

Kallon kawun yayi, sai kawai ya mishi murmushi yace "Karka damu Kawu, zan sanar da kai idan lokacin ya yi, bari na barka ka huta, amma dan Allah ka cire tunanin nan a ranka, na maka alƙawarin komai ya kusa tafiya daidai da izinin Allah."

Jinjina kai kawun yayi yana murmushi yace "Na yarda da kai Sa'ad."

Murmushi ya sake mishi ya juya ya fita da sassarfa da kuma abubuwa dayawa a kan shi yana saƙawa da kuma niyyar sai ya cimma su da yardar Allah.

*A gurguje*: an ƙara shafe watanni kusan biyar da wannan magana tsakanin Sa'ad da kawu Hisham, a wannan lokacin da aka ɗauka Sa'ad ya sake bibiyar abubuwa dayawa da kuma ƙara sanin wasu abubuwan masu mahimmanci, zai iya cewa yayi nasara ta kowane ɓangare, sai dai abu ɗaya da ya kasa samun koda makama ɗaya wato neman Kuwailat da ya saka kan shi, dan haka ya shirya dan zuwa garin da masoyiyar shi take, wanda a bayanan da ya samu Aish ta koma makaranta abun ta sannan tana farin ciki a cikin ahalinta. Yayi sallama da kawu tare da faɗa masa ya zama cikin shiri, idan har abinda ya sa a gaba ya tafi daidai, to zai kira shi ya je dan neman yafiyar Ahalin nan, ya bishi da fatan sa'a da son dacewa dan shi kan shi ya samu salama.

*AHALIN AHLAN*

Cikin rufewar ido da ɓacin rai na kai wa maƙura akan wulaƙancin da Yay Bilal ɗin ke mata ta kalle shi wanda shigowar shi kenan gidan bayan watannin da suka kwashe a ƙasar waje dan haihuwar Abida tace "Na rantse da Allah sai ka sanar dani zaman da nake a gidan nan, haka kawai zaka maidani wata ƴar iska da ban san me nake ba, me na maka Bilal? Dan bana haihuwa ne ni zaka min wannan wulaƙancin? To ka sani wallahi ba'a canzawa tuwo sunan shi."

Kasancewar ya fita sabgar Fa'iza saboda abubuwan da ta aikata, sai ya wurga mata harara yace "Aikin banza, ke baki san Æ´an duniya sun ma tuwo suna iri-iri ba? Wasu da *gagare* suke kiran shi, wasu kuma da girmamawa zaki ji sun ce *Mr. President*, yayin da wasu ke ce mishi *mai gida*, wasu kuma da izgilanci zaki ji sun ce *Mudi*, shine har zaki wani ce wai tuwo sunan shi tuwo."

Malalacin murmushi tayi tace" Na sani, amma ba a kaina nake magana ba, akan ka nake magana Bilal."

Da mamaki ya dube ta yana gyara tsayuwar shi yace" Me kike nufi?"

Nan ma murmushi ta mishi ta gyara tsayuwar ta ita ma har da ɗan gyara ɗan kwalin ta sannan tace" Ka auro Abida ne dan ta zo ta haifa maka yara saboda kana ganin ni na kasa, amma shekara nawa muka ɗauka tare da Abida babu wacce tayi ko ɓatan wata? Sai yanzu ne Abida zata zo maka da rainin hankalin wai tana da ciki har ma ta haihu? Hmmmm! Bilal, Abida anfani take da son ganin kai ma ka zama Baba, shiyasa take rainawa kowa hankali dake gidan nan."

A ɗan fusace kuma a kausashe ya nufe ta yana faɗin" Me kike nufi Fa'iza ? So kike ki ƙalubalanci ubangiji da ya fara bata kafin ke? Ko kuma wani ƙudirin ne a kan ki game da haka?"

Baya ta ja kaɗa dan yayi kamar zai kai mata duka ne tace" Ko ɗaya, ni a wa da zan ƙalubalanci mahaliccina? Ina so ne dai na maka hannun ka mai sanda, kuma ƙiris ya rage ayi walƙiya halin kowa ya fito fili."

Taɓe baki yayi ya bita da wani ƙasƙantaccen kallo yana faɗin" Tabarmar kunya kike so ki naɗe da hauka, Fa'iza kin gama fice min a raina gaba ɗaya."

Sunkuyar da kanta ta fara yi a tausashe tace" Kamar yadda zaman gidan ka ya jima da fice min a raina Bilal, ina zaune ne kawai dan bana so a kirani da butulu, bana so a zargeni da guje maka lokacin da kake buƙatata."

Baya ya ja yana ƙare mata kallo sama da ƙasa yana dariya yace" Ke dai? Ke har kina da bakin da zaki ce zaman gidana ya fita ranki? Me kika nema kika rasa anan? Me ye baki fi ƙarfin shi ba Fa'iza?"

Murmushi ta mishi tace "Hakane, amma ka sani dukiya ba ita ce jin daɗin duniya ba, idan so samuna ne nima a ce ina da yarana, amma indai da kai zan ƙare rayuwa, to bana tunanin zan ga wannan ranar."

Ƙanƙance idanu yayi yana kallon ta da mamaki sosai yace "Me kike nufi?"

Saida ta kalle shi ba alamar tsoro tace "Ina nufin *kaine baka haihuwa*..."

Duk da ta kai ƙarshe saida ya ɗaga hannu ya wanke fuskar ta da zazzafan marin da ya saka ta tangaɗawa baya kamar za ta faɗi, kafin ta samu ta dire kan ƙafafun ta cak tana kallon shi dafe da kumcin ta, cikin hargagi da kaushin murya ya fara faɗin"...

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*
_(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes.

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata.

Sayen na gari mai da kuɗi gida, sai an gwada akan san na ƙwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a ƙasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI- SIRRIN MANYAN MATA)._

_Bismillahir-rahamanir-rahim._

*22*

Cikin hargagi da kaushin murya ya fara faÉ—in "Fa'iza, iskanci da fitsarar ki ta kai haka dama? Ni zaki kalla ki ce wai bana haihuwa? Me kike nufi da maganar ki? Kina so kai tsaye ki ci zarafina ne? Sannan ki aibata É—an da ko suna ban raÉ—a mishi ba daga haihuwar sa, me yasa Fa'iza? Wacece ke? Akan me? Kin aikata babban laifi, amma duka gidan nan muka saka miki ido muna kallon ki, shin kenan ba kara bace muka miki? Shine har zaki gaya min wai bana haihuwa, ko kin san da zan iya shari'a dake akan wannan furucin naki?"

Da maÉ—aukakin mamakin dake neman halaka ta ta dube shi tace" Ni ka mara? Bilal saboda na faÉ—a maka gaskiya?"

A tsaurare yana zaro idanu yace" Kuma zan sake wanka miki wani marin kika sake furta maganar banza a kaina ko iyalina."

Hawayen da suka gangaro mata tasa tafin hannu ta shafe tare da yin murmushin laɓɓa tace" Shikenan, ka sani ban yi auren duka da kai ba, kuma ba zan sake kwana a gidan ka ba dan na lura a makance kake da abubuwan dake faruwa, amma duk ranar da ka gane gaskiya, na san zaka neme ni da kanka, amma ba zan kasa maimaita maka cewa *baka haihuwa ba*, Bilal matsalar daga gareka take, kai ma kuma fargaban hakan yasa ka ƙi yarda shekara da shekaru muje asibiti, amma ni nayi gwajin lafiyata ba da sanin ka ba, kuma ina zaune gidan nan ne dan kawai *ina son rayuwa da kai*."

A hassale ya yarfa mata hannu yana faÉ—in" Ki tafi mana, ki tafi nace Fa'iza, sai me? Zan gagara rayuwa ne idan kika tafi? Kuma in dai nine ki sa ran ki a inuwa, na rana É—aya ba zan sake tunawa dake ba bare har na sake maimaita kuskuren da nayi a baya na sanin ki da nayi a rayuwata, ki tafi, ki fi ruwa gudu."

Ƙwarai kalamanshi suka soke ta, duk son ta da zaman gidan nan ko dan ta kawo ƙarshen Abida abun ya faskara, ba zata sake kwana ba bayan wannan kalamai da suka fito daga bakin Yaya Bilal, dan haka ta tafi a guje zuwa ɗakin ta, shi ma a fusace ya fita daga ɗakin nashi zuwa falon Abida da suka dawo tare ɗauke da santalelen yaron su.
Chapter 47 · 0% Book details