← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 168

Sashe 69

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Na kusa fara daarasin kayan marmari ƴan uwa, ki garzayo ki yi register akan farashi mai sauƙi zaki koyi abubuwa dayawa har na tsawon kwana biyar* in sha Allah. SAI KUN ZO

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*33*

*11:20* Ummu nufi ɗaki dan kwantawa bayan Kuwailat ta kwanta, tayi mamakin samun shi idanun shi biyu, da mamaki ta ƙarasa tana faɗin "Abban Kuwailat, dama ba bacci kake ba?"

Murmushin yaƙe ya mata yace "Na dai farka."

Kusanshi ta zauna tana faÉ—in "Na haÉ—a maka ruwan wanka ko?"

Jinjina mata kai yayi yace "Um."

Dan haka ta miƙe da azama dan haɗa mishi ruwan, tana gama haɗawa ta dawo tace "An haɗa."

A gajiye ya tashi zaune da ƙyar, sai dai ƙafafun shi da sukayi bala'in nauyi ya kasa ɗagawa, dan haka yace "Taimaka min na tashi?"

Ta yi iya ƙoƙarin ta na taimaka mishi amma gaba ɗaya ne ƙafafun shi suka ƙi takuwa, ga kan shi da ya ce har yanzu bai daina ciwo ba, dan haka tayi saurin zuwa ta samu Hajia babba ta sanar da ita da kuma Khamis wanda duk da ba Alhaji bane ya haife shi amma ya zama babba ɗa na gidan, da taimakon su ne aka ɗauki Alhaji zuwa asibiti, kwantar da shi aka yi tare da bashi kulawar da ta dace sannan aka mishi allurar bacci. Khamis ne ya ɗauki wayar Alhajin ya kashe ya ce saboda ka da a takura mishi, shine Dalilin da ya sa ake kira ba'a samu.

*Yana* kiran lambar Ummu sai kuwa ta shiga, ta jima tana kallon lambar tana tunanin waye ke kiran ta da wannan code É—in? Dan ita sam ba ta da lambar Jabir, ba ta nema ba kuma shima bai neme ta ba, ita a ganinta ai muharramin ta ne, dan haka bai kamata suna waya ba, abinda ya faru ya faru kawai ya wuce, sannan kuma ba lambar Aliyu bace wanda tana da ita, cikin wannan hali na tamtama da rashin sanin waye ta É—aga kiran sannan ta kara a kunne.

Jin ta ɗaga saida ya sauke ajiyar zuciya ta farin cikin a ƙalla zai san ina Abban shi yake? Dan haka shi sam ya ma manta da ya mata sallama bare ya gaisheta, abu na farko da ya furta a nutse sosai kamar mai mata raɗa shine " *Maaama*."

Ya salam! Hasbunallah wani'imal wakil ! Shine abun da ta faÉ—a ita ma a zuciyar ta, dan kuwa wannan yanayi da ya mata magana da shi sosai ya saka gabanta faÉ—uwa tare da jin wani yam yam ! A jikin ta, sarai ta gane wa ke magana, dan a duniyar nan shi kaÉ—ai ke bata girman da ko Kuwailat da ta haifa ba ta bata irin shi, iska ta fara fesowa daga bakinta kafin tace "Barka."

Ɗan ɗaga girar shi yayi irin mamakin kan nan nashi ya kama shi, cikin matuƙar tausasawa yace "Maaama ina Abba? Yana lafiya?"

Saida ta kalli Alhaji dake bacci sannan ta tausasa murya ita ma kamar bata son kowa dake kusa da ita yaji tace "Yana bacci, yana lafiya."

Sai ya ji kamar bai yarda da ita a ba, dan gaskiya muryar ta babu walwala à ciki, hakan yasa shi kasa gasgata ta saida yace "Kun tabbata? Ku bani Abba, ina so nayi magana da shi?"

Ƙurawa Alhaji idanu ta sake yi tana mamakin yadda yake wani kiran ta da *ku* tsabar girmamawa, numfashi ta sauke sannan tace "Muna asibiti ne, bai ji daɗi ba, an mishi allurar bacci yana hutawa, amma jikin shi da sauƙi sosai, kar ku damu."

Ya É—auki kusan minti É—aya bai ce komai ba kafin ya numfasa yace "Shikenan, Allah bashi lafiya, zan sake kira, amma dan Allah Maama..."

Sai kuma ya sake yin ƙasa da murya sosai yace "Na roƙe ku idan ya farka ku sada ni dashi."

Saida ta sauke nauyayyan numfashi sannan tace "In sha Allah."

Tana sauraro har ya yanke kiran sannan ta É—auke wayar da ga kunnen ta, aje wayar tayi sannan ta sake maida hannun ta ga marar ta ta dafe da har yanzu take murÉ—a mata.

*Washe Gari*

Khamis da Hayat ne riƙe da Alhaji da suka dawo daga asibiti, Ummu na bayan su riƙe da wasu kayayyaki a hannayen ta suka nufi shiga falon ta, suna kusan isa ɓangaren Hajia Asiya tayi saurin fitowa daga falon ta wacce ta ga shigowar su tace "A'a, ku dakata malamai, ina ce yau kwanana ne ko?"

Dakatawa sukayi duk suka kalle ta, sai lokacin kaɗai Ummu ta iya tunawa da yau ya kamata ya koma ɗakin ta, dan Hajia babba ta cire kanta a lamarin kwanan nan, a ladabce Ummu tace "Ina kwana Maman Aliyu, kiyi haƙuri wallahi na manta ne."

Ba ta jira me za ta ce ba kawai ta kalli su Khamis tace "Ku raka shi, zan je na aje kayan sai na zo na sake duba shi."

A gatsalce Hajia Asiya ta harare ta tace "Ba buƙata, naga ai ke kika kwana dashi asibiti, sannan kun dawo gida tare, ni ba zan iya kula da shi ɗin bane?"

Murmushi kawai Ummu tayi dan ita yanzu ba ta ga abun rigima a rayuwar gidan nan ba, a tausashe ta sake cewa "Kiyi haƙuri." ba ta sake jiran abinda za ta ce ba kawai ta yi hanyar shigewa, tsaki tayi ta bita da harara tace "Aikin banza, ka ji munafurci wai ta mance."

Su Khamis dai na kallon ikon Allah, haka suka raka shi har falon ta suka zaunar da shi wanda shima ya zuba musu ido kawai bai ce komai ba akan hatsaniyar tasu, shi da zasu ji ta tashi ai da sun bar shi wajen Ummu har ya samu lafiya, dan Hajia Lubabatu dai ta kanta take ita ma bare ta yi jinyar shi, Asiya kuma masifa da tsirfa kala kala zai sha da hayaniya, Atika kuma jaraba da rashin kulawa, dan haka Ummu ce za ta iya kuma sun hana.

*******************

Mamaki ne ya cika Hajia Radiya ganin yau kira ɗaya tak ta ma Fahad amma ya ɗaga, gaisawa sukayi sosai cike da farin cikin to ko dai Allah ya fara karɓan addu'arta ne? Dan ko umra da ta tafi iya Fahad kawai ta ambata gaban ɗakin mai kowa da komai da iko akan komai, cikin kulawa tace mishi "Fahad, yaushe za ka zo gida? Abubuwa da dama suna ta faruwa babu kai, yanzu Faha haka kake so ka ci gaba da rayuwa?"

Da alamar ƙaguwa yace "Mamie, gani nan fa zuwa gidan, ina kan hanya ne, zan zo ai."

Saida ta kalli Alhaji dake kallon farin cikin da take sannan tace "Da gaske? Amma dai idan ka zo ba zaka koma ba ko?"

Da yanayin zafi Alhaji ya figi wayar ya É—ora a kunnen shi yace "Babu inda zai koma, ka ji da kyau idan har ka zo to babu komawa, ka zo kenan, dan aure zan maka."

Wata irin dariya kawai Fahad yayi dan shi ai ya ga zuwan shi da komawar shi, yo Nabilan shi ma ta gudu daga gida bare kuma shi? Shi fa? Ko a haure ba ya haura katanga ba, ba tare da son doguwar magana ba tunda ai gidan zai zo kuma sai ya zo ɗin tunda yana buƙatar kayan abinci da kuɗi yace "Abbu kai dai jira na zo, aure kuma kamar wata mace? Idan ma auren za ka min ka min da Nabila mana, amma ba da wacce bana so ba."

Yana gama faɗin haka ya kashe wayar ba tare da ya ji me Alhaji zai ce ba, hakan yasa Alhaji miƙa mata wayar ta yace "Kina ji? Ki duba min cikin dangi wacce kike ganin za ta dace da shi, yana shigowa gidan nan aure zan ɗaura masa, wataƙila ya yi hankali."

Da tsananin mamaki Hajia tace "Aure? Auren dole fa kenan za ka mishi?"

A kausashe ya kalle ta yace "E É—in, idan bamu mishi auren dolen ba ai shi ya je yana zubar mana da mutumci a dole, to ni dai abinda na faÉ—a kenan, idan za ki duba ki duba ko ni na sa a duba min."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Allah baka haƙuri, amma na ga mu kanmu ya muka iya da Fahad da har za mu yarda a aura masa ƴar mutane ba ya so, zai iya yin komai ba."
Chapter 69 · 0% Book details