Sashe 97
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ƙn buɗa idanun tayi sai hannun da ta ji yana ci gaba da yi mata zugi take ta yarfa shi tana addu'a kala kala. Jabir na daf da shiga ɗakin gen ɗin ya ji wannan sautin da ya saka gaban shi faɗuwa kuma tsigar jikin shi ta tashi, tabbas daga madafa ne ƙarar, kuma ba ihun Kuwailat bane wannan, ihun Maama ne, *Maaman shi* ce wannan, to amma me ya sa tayi ihun? Sanin da ya ma mata ko kyankyaso zai iya saka su wannan ihun bare fiye da haka, dan ya sha jin haka daga matar Baban shi, sai ya zaburo ta ce ƙadangare ne ko ɓera, ya so share abun kawai. Amma sai yake jin sautin addu'o'i ƙasa ƙasa haka, sai ya aje jarkar da ɗan sauri kawai ya leƙa kan shi da niyyar ya nemi izinin shiga, hannun da take yarfawa tana safa da marwa idanun ta rufe ta siririn hasken wayar ta da bai gama zagaye madafar ba ya gani, sai ya ji abu mai kama da tashin zuciya... Um um! Tashin hankali, gushewar lissafi haka, da dai rasa nutsuwa gba ɗaya sun ziyarce shi, Maama, me ya same ta?
Shiga kawai yayi ƙarewa madafar kallo da son ganin me ye ya tsorata ta? Sai kuma hannun nata da shima yake kallo, bai taɓa sanin zai iya yin magana cikin irin muryar dake nuni da tashin hankali ba sai yau, yadda ya ji bakin shi ya furta "Maama, me ya same ki?"
A firgice ta buɗa idanun ta ta kalli fuskar Jabir, kafin tayi wani tunani ita tsiraicin ta ne a gaban ta, da mugun sauri ta durƙushe ƙasa duka guiwoyin ta a ƙasa tare da saka hannu ɗaya taa rufe kafaɗar ta dan kar ya kalar mata ƙirji tace" Me ya haka Jabir? Ya za ka..."
Kalmar _" Subhanallah!"_ Kawai ta ji ya ambata, kafin ta ankara da me ya sa yayi sai ganin shi tayi durƙushe gaban shi shima, ba wannan ba... Ba wannan ne ya ɗaga mata hankali ba, ba shine ya tsayar mata da tunani ba sai ganin Jabir ya damƙi hannun ta da ita kan ta bata san danshin jinin da yake yi har yaa kai yana ɗasa ƙasa ba ya riƙo shi da kyau tare da tattara hankalin shi yna kallon hannun.
Har ga Allahn da ya halicce shi shi kallon mahaifiya yake mata, har zuciyar shi bai riƙo hannun ta da wata manufa ba, sai dai ya yarda kawai sharrin sheɗaan ne da ya saka shi jin gaban shi ya yanke ya faɗi har yake masa raɗa a kunne da cewa _"Hannun Maaman ka taushi, ga kuma ɗumi."_
A zuciyar shi yayi a'uziyya tare da zura hannu aljihu ya ciro hancki ya warware shi, da sauri ya ɗora shi a hannun nata ya fara kiciniyar ɗaure mata ko jinin ya daina zuba. Har cikin ranta take jin wannan haɗa hannun d sukayi, wataƙila yanayin da take ciki ne ya yi tasiri har kan ƙanin bayan ta wanda ke kiran ta da sunan Maama? In ba haka ba me zai sa ta dinga jin wannan abubuwan game da shi dan ya taɓa hannun ta, daga tafin ƙafar ta fa ta fara jin an tsikare ta har zuwa wurin d ya jima yana mata Ƙaiƙayi an kasa sosa mata, ga fuskar shi da take kallo a razane sai sheɗaan ya fara faɗa mata _"Dubi fuskar shi kyakyawa kamar ta jaruman da kike kall..."_
A rikice Ummu ta miƙe tsaye bayan ta fincike hannun ta daga na Jabir, rintse idanu tayi, ranta ya gama ɓacewa, hankalin ta ya ƙarasa tashi, idanun ta sun gama rufewa da wannan abu da ke faruwa da ita.
Cikin ɗimuwa da zautuwa Ummu da ta miƙe tsaye cikin ɗaga murya tace "Bana so, bana son taimakon kowa, me yasa baku da tausayi? Duk halin ku ɗaya, ba kwa taɓa zama da mace kusan me ce ce matsalar ta, burin ku kawai mace ta halaka a sanadiyar ku, to ƙarya ne wallahi, duk da ina jin shauƙi akan haka, Jabir ko waye ma ba zan taɓa yarda na aikata abinda bai dace ba, kayi nesa dani tun kafin mu faɗa halaka, ka gane mana, matsalata babba ce, kuma..."
Sai kuma ta dafe kan ta kawai da mugun sauri ta juya ta kama hanyar barin madafar, ɗimuwa ya sa ta manta rigar dake jikin ta, bayan ƙarama ce ta fito mata da surar jikin ta. Jabir da duk abinda take faɗa tsaf yake riƙe shi akan shi, albarkar haddar Alƙur'ani tasa komai ma yana riƙe shi da gaggawa sannan ya jima bai manta shi ba, ya la kowace kalma muhallinta na musamman, wuri kawai yake jira ya samu ya aje équations sannan ya tantance su da kyau, to amma da ta juya a fusace, shi kuma ya juya a mamakance ya bita da kallo, sai kawai la'anannen Allahn nan ya tilasta masa duban ƙasa kaɗan daga bayan ta, hakan yasa idanun shi sauka tsaf kan wani irin nagartaccen ƙugu da ya iya hango wasu irin duwatsu duwatsu dake nuni da jigidar ce nan tari guda kenan. Kai jama'a, anya kuwa Maama lamarin ta ba shafar iskokai? To abu take irin na ƴan iska fa gaban shi, wannan saboda Allah tafiyar da ta dce tayi ce ko da dai ranta na ɓace?
Da ƙyar ya muskuta ya kashe mata wutar da bai san me za ta yi da ita ba, juyawa yayi jikin shi duk a kasalance ce ya bar madafar, har ya fara zuba man sannan Alhaji ya same shi, suna zubawa aka tayar da shi gaba ɗaya unguwa ta ɗauki haske.
*Tana* kwance ta kifa kanta tana rizgar kuka na bara bara ta ga haske ya mamaye É—akin inda sanyi ya daki fatar jikin ta, tashi tayi zaune ta kalli É—akin sannan ta kalli inda madubi yake, sai kawai ta share hawayen ta tare da gyara zaman ta kan gadon tana mai É—aura niyyar _"In sha Allah gobe zan je gidan Alhaji Sagir, zan faÉ—a masa duk dan ya sama min mafita, nasan shi zai fahimce ni sannan ya taimaka min, amma ba zan halakar da kai na ba."_
Da wannan ƙudurin ta kwanta duk da kuma ba tayi bacci ba a daren, amma dai ta wayi gari da shi. A shekaru goma sha uku zuwa sha huɗu da suka ɗauka tare na rayuwar su, ko maƙwabta bata taɓa shiga ba da izinin sa ba, shi kan shi ya yi mamaki sosai da Kuwailat ta ce wai Maman ta ta riga ta fita, ta fita ta je ina? Ba ta gyay masa ba kuma? To me take nufi? Matsalar tasu har ta fara kai wa haka? Bai da matsala dan ta fita bai sani ba, ya san duk inda Ummu za ta je ba z atpa je inda ba zai ji daɗi ba, to amma kuma me yasa sai yanzu kwatsam kuma da safe haka? Sannan Kuwailat ma bata san ina taje ba.
*Ummu* dake gaban amaryar Alhaji Sagir suna hira bayan tabbatar mata yana zuwa yanzu dan ta faɗa masa yana da baƙuwa, cikin raha Hajia Zeinabu ke sake mitar "Wallahi Ummu ba kya da kirki, yanzu yaushe rabon ki da gidan nan?"
Ummu da ƙyar take murmushi, kuma ita Hajia Zeinabu ta fahimci haka, dan tunda ta ganta a wannan lokacin kuma ta ce Alhaji take son gani, amma dai tana son jan ta da hira dan fa kullum suna tare a waya, suna gane ma juna kasancewar sune amaren gidajen mazajen nasu dake aminai. Cikin taushin muryar Ummu dake yaƙe tace "Wallahi Maman Na'ima ba kya rabo da tsokana? Na ga ko ban zo ba kullum fa muna manne da juna ta waya."
Cike da neman rigima ko Hajia Zeinabu tace "E na sani, amma ai waya daban zumuncin gida kuma daban."
Murmushi Ummu ta sake yi ta muskuta za ta yi magana kenan Alhaji Sagir ya sallamo falon, da kulawa suka amsa mishi inda suka gaisa sosai da Ummu, miƙewa Hajia Zeinabu tayi tana faɗin "Bari in baku wuri, idan kun gama zamu zauna."
Wuri ya samu ya zauna yana faÉ—in "Maman auta , ya gida? Ina autar tamu?"
Da Æ´ar fara'a tace "Lafiya lau."
Hankalin shi ya mayar kan ta kacokam tare da faɗin "Hajia Ummu, lafiya dai ko? Na ji hankalina ya nemi tashi duba da irin haka bai taɓa faruwa ba."
Kan ta na ƙasa sosai tana ta wasa da makullayen ɗakin ta da na mota, cikin shasheƙa da fargaba ta fara faɗin "Dama...dama Alhaj... Shine yak..."
Nauyi, kunya, kara suka saka Ummu yin shiru hawaye na neman ɓalle mata, cike da kulawa Alhaji Sagir dake kallon ta ya kuma gane komai yace "Ummu, faɗa min naji menene matsalar? Me Alhaji Kabir ɗin ya miki? Ki faɗa min mana, na ɗauka kin zo ne dan kin san na isa da shi kuma zan iya yi miki maganin matsalar ki, sannan ina ɗaya daga cikin waɗanda suka je nema masa auren ki, kuma aka duba girma da kimar mu aka bashi."
Sai kuma ya tausasa murya sosai yace" FaÉ—a min Hajia Ummu, ina sauraren ki."
Ɗan ɗaga kan ta tayi da niyyar tayi ƙarfin halin faɗa, amma sai ta sake kasawa, zuciyar ta nuna mata take a'a, da kunya ai, ba tare da ta shirya ba ta miƙe tsaye, dama komai nata yana hannun ta, bare rikicewa ta saka ta manta wani abu a wurin, dan haka ko juyowa ba ta yi ba tace "Ba komai, nagode, sai anjima."
Da kallo ya bita bayan ya yinƙura da niyyar ya mata magana, amma nauyin jiki ya sa dole ya dakata ya bita da kallo har ta fice, yana nan zaune har ya ji fitar motar ta a gidan, koma menene ya san akwai matsala kawai, tunda ba ta taɓa masa irin haka ba, dalilin ma da ya sa kenan ya ji tausayin ta ya kama shi, dan ya san ta rasa mafita ne kawai ta tunkaro shi.
*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:14 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
*Tallah, tallah, tallah*
*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*