← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 148 OF 168

Sashe 148

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dai ai maaman shi, ba zai bari sheɗan ya dinga saka shi yawan kallon ta ba gaskiya, zama da mace wuri ɗaya ai haɗari ne da shi, sheɗan kuma dama ai la'anannen Allah ne, Maaman ka ma sai ya sa ka ji wani abu a kan ta. Rusunawa yayi ya aje ledar hannun shi kan carfet ɗin da aka shinfiɗa ɗakin wanda shima gadon ɗaya daga cikin ɗakunan baƙi dake cikin gida ne wajen su Hajia aka aza musu, kuma wannan ɗakin kawai aka gyara ban da ɗayan, saboda suna ganin to ai mata da miji ne.

Yana aje ledar ya juya ya fice bai ce mata ƙala ba, ita ma bata kula shi ba har ya fita sannan ta je ta rufe ƙofar tana ayyana _"Ba kaza ba? Za ka ci kaza, marar kunya, dan baka jin kunya har ni zaka kawo ma kaza, to idan na ci me zaka min?"_

Aikin gaban ta ta ci gaba da yi, inda Jabir ma da ya fita yayi mamakin ganin ba komai a É—aya É—akin bayan fitila da fanka sai jakar kayan shi da ya aje tun sanda suka zo, kayan baccin shi ya ciro da zai saka sannan ya cire na jikin shi amma da singlet É—in shi da towel a wuya ya fito ya nufi ban É—aki.

Dama ban ɗakin ita ke kallon ɗakunan, hakane ya sa yana daf da isa ban ɗakin Ummu ma ta fito za ta shiga dan yin wanka ɗaure da towel amma da hijabin ta, suna haɗa idanu da sauri ta maida ƙofar ɗakin ta rufe tana maka masa hararar da ta saka shi ɗan yin tsaye yana tunanin da shi take ko me? Me ya mata to? Kar fa dan yna ce mata maama ta raina shi shima, ba ya son haka fa, shi tsaran ta ne da zata harare shi? Ka ji yarinya kai da iya shege.

*WASHE GARI*

A kujerar sofan dake falo ya kwana dama, da ya dawo daga masallaci ma nan ya sake kwantawa, hakan ya sa ko da Ummu ta fito saboda matsananciyar yunwa za ta shiga madafa ɗauko faranti ta zo ta ci kazar nan ya tashi zaune, wallahi ya ɗauka za ta gaishe shi ne ko ta ce masa dai ko da sannu, amma ƙuruciya irin ta Maama sai tayi kamar ba ta gan shi ba ta fita, jim kaɗan ta dawo ta wuce wqnda dole Jabir ya bi bayan ta da kallo, sai kawai yayi murmushi ya sake komawa ya kwanta.

Saida ta ci ta ƙoshi ta tattare komai ta fito da farantin da leda a hannun ta, saida ta durƙusa gaban fridge ta saka sauran lemukan da ta rage sannan ta ɗauki sauran ta kai madafa ta aje ta wanko hannayen ta ta dawo. Gyaran ɗakin nata tayi ta kunna masa turaren tsintsiya da na wuta bayan ta fesa na ruwa, fitowa tayi ta shiga ban ɗaki nan ma wanke tayi tasss ta saka turare sannan ta dawo falon. Hararen shi tayi duk da ta ga idanun shi a rufe suke, taɓe baki tayi tana ayyana _"Yanzu dan fitsara Jabir ko ina kwana ba zai iya ce mata ba? Ba laifin shi bane ai na iyayen ta ne."_

Dake ba wani gyara d zata ma falon, sai kawai ta fara fesa turaren ruwa, sannan ta jona wayar kaskon turaren wuta mai aiki da lantarki, hayaƙin da ya fara tashi ne ya saka Jabir buɗa idanun shi duk da dama ya ji tana ta feshe ɗakin da wata masifar🤣, zaune yayi yana kallon ta tana kunna wani turaren kuma na tsintsiya, bai so yi mata magana ba saboda shi dai ita yake so ta fara masa magana tunda ai ita ce mata a gidan.

Amma kuma wannan abun idan ya masa yawa mura yake saka shi, dan haka ya mata wani irin natkakken kallo murya ƙasan maƙoshi kamar mai rowar muryar yace "Bana son hayaƙin nan ya min yawa."

Ta san da ita yake, amma sai ta ƙi ko jiyowa bare ya san ta ji shi, ama daga haka ƙusƙus take faɗin "Ɗakina ne ba naka ba, ka fita mana."

Ganin bata saurare shi ba yasa a dake ya sake faÉ—in "Ki barshi haka, bana so ya min yawa."

Ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace "Idan baka so ka canza guri mana."

Kallon ƙeyar ta yayi, sai kawai ya jinjina kai yana miƙewa yace "Ok." Hanyar ɗakin nata ya nufa, da kallo ta bishi, ganin har ya buɗe ya shiga zai rufo ƙofar da sauri tace "Jabir."

Ɗan dakatawa yayi saboda jin yadda ta wani kira shi a wani gatsaltsal haka wai Jabir, amma shi wannan shege ɗan iskan ta iya kwantar da kai idan za ta kira sunan shi ko? Har wani Jibril take faɗi? Wani arnan kallo ya mata da idanun shi nan ƙanana irin _" Ina ji?"_

Ba alamar rusunawa ko taunawa tace" ÆŠakina ne nan."

Cike da shaƙiyanci ya kalle ta sama da ƙasa sai kawai ya ja ƙofar ya rufe, dake nan hayaƙin ya rage sai dai ƙamshin na nan na wannan sanyayyan turaren da mace indai kikayi aiki da shi da wuya ki cigaba da son wani turare bayan su, wato *bakhoor* da kuma *fleur da coton*, turare ne da su basa buƙatar wuta, ƙamshin su ba karamin daɗi gare shi ba, sai dai idan ba ka jaraba ba kawai.

Lafiyayyar shinfiɗar nan ya haye tare da jawo zanin rufar ya rufe jikin shi, cikin wata irin nutsuwa ya fara sauke numfashi a hankali a hankali. Ummu kuma ƙwafa tayi da tunanin zai fito ne ai, dan haka ta ci gaba da gyaran tsakar gidan, amma da ta kamalla ta shigo sai bata gan shi ba, rufe ƙofar falon tayi saboda tana so turaren da tayi ya jima sannan ta nufi ɗakin tana tunanin yau zai gane gaba take da shi, in ba rainin wayo ba ɗakin nata zai shiga ya kwanta?

Bacci har ya fara ɗaukar shi kawai ya ji an bubbuga katifar da ƙarfi, da ƙarfi fa irin za ka tashi wanda ka raina ɗin nan daga bacci, kuma har da kwaroroton kiran sunan "Jabir.. Jabir kai...tashi ka koma ɗakin ka nim..."

A hankali ya tashi yana rintse idanun shi sosai tare da danne leɓen shi na ƙasa, zuro ƙafafun shi yayi ƙasa yana ɗan dafe goshin shi, saida ya ji kan shi ya daina sara mishi saboda hargitsatsen tashin da ta masa sannan ya ɗaga kan shi ya kalli fuskar ta. Ta dafe ƙugu sai wani harare harare take yi, ai ba yarinya bace ita, kuma ta san me ake nufi da miji, shine kawai ta raina? A nutse, cike da dakiya ba alamar wasa yace "Haka ake tashin mutum a bacci?"

Kallon fuskar shi tayi, ka ji yaron nan da rainin wayo? Sai kawai ta taɓe baki ba tare da ta daina kallon shi ba tace "Ka koma ɗakin ka."

Ok! Kenan dai ta kasa fahimtar yaren shi ko? Dan haka ya miƙe a nutse tare da takawa ɗaya a na biyu ya kai gare ta, daf da ita ya tsaya, zai iya cewa kansu ɗaya da ita a tsayi ma, dan da zata saka dogon takalmi tsaf za ta fishi tsayi, hakan ya bashi damar kallon ta ido cikin ido fuskar shi a haɗe yace "Kinga, ba tashin hankali nake so muyi ba a zaman nan da zamiyi na ɗan lokaci, sai dai duk da haka bana so ki na yin abubuwan da zasu hassala ni, kinga jiya da na shigo na miki sallama, amma baki amsa min ba sai kika ce wa ye? Bayan kuma nasan kin san ko wa ye ɗin, na ƙyale ki muka kwana a haka, tunda safiyar nan tayi ba ki ce min komai ba, ko ba komai ki ce min ma antashi lafiya? Amma ba ki yi ba, ni na miki magana kan wannan hayaƙin da kike ta cika ɗaki da shi, amma me kika ce min? Na zo nan kuma shima ba zaki barni ba? Bana so wani abu na rashin ganin girman juna ya shiga tsakanin mu, ko haihuwata kikayi tunda yanzu *igiyoyin ki* na hannuna na cancanci a darajta ni."

Sai kuma ya É—an ja baya kaÉ—an yana ci gaba da kallon fuskar ta yace" Burin da na zo dashi gidan nan shine, idan na ga fuska a wajen *Maama*, to zan ci gba da gaishe ta kamar yadda nake yi lokacin tana gidan Abba, idan gari ya waye na tambayi Maama ko da abin da take so nayi mata, tun daga wanke wanke, shara, girki, komai ma, na yi shiru ne jiya da yau dan naga naki salar kamun ludayin, shin idan ni ban yi ba ke zaki nuna nagartattun halayen babban gidan da kika fito, sai baki yi ba, to ya kike so na miki? Na nuna miki tawa kalar?"

A nutse yake maganar kuma a nutse ya koma ya zauna bakin gadon yana dafe kan shi yace" Nan É—akin zan zauna, waccen ba a gyara yake ba, kuma daga ni har ke ai zaman wucen gadi ne zamuyi."

Komawa yayi ya kwanta yana kallon fuskar ta dake kallon shi idanun ta sun yi ja kuma a cike da hawaye, bai damu da ganin haka ba dan bai ga abinda ya mata na kuka ba ya sake cexa" Dan Allah kar ki sake tashi na, azumi nake."

Zuciya ce ta kawo wa Ummu a wuya, sai kawai ta juya da sauri ta bar falon tna fashewa da kuka, kukan kawai take tana tuna zafin maganganun da auren da aka mata da Jabir ya sa shi ganin damar ta har yake faÉ—a mata... Kamar busar sarewa kukan nata ke cika mishi kunne, tun yana juyi yana gyara kwanciya har dai ya ji shi fa baya son takura, kukan nan nata jin shi yake kamar a cikin zuciyar shi take yi, dan haka ya taso ya fito ya same ta zaune sai goge majina da hawaye take yi da hijabin jikin ta.

Ƙarasowa yayi ya tsaya gefen ta yana kallon ta yace "Wani abu akayi kike kuka?"
Chapter 148 · 0% Book details