← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 168

Sashe 3

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da kallo ta bi shi har ya fice sannan ta sauke ajiyar zuciya, tana jin muryar mahaifin nata na tambayar uwar marayu wai har yanzu Mujittafa bai shigo ba? Da e kawai ta bashi amsa ta ji sun É—auki wata hira. Mujittafa É—a ne ga Æ´ar uwar uwar marayu, bayan rasuwarta ta ce a bata tunda mahaifi shi ba zama yake ba.

Daddaɓa Nabila tayi dake bacci duk tayi gumi saboda zafin dake akwai, tashin da za ta yi cikin magagi tana kama zanenta, Hakan yasa abu faɗowa daga cikin zanen nata, Ummu da ta kula da hakane ta sunkuya ta ɗauka tana dubawa.

Ganin kuɗi ne har jaka biyu yasa ta kalli Nabila da tuni ta fice a ɗakin ta faɗa kan shinfiɗar da uwar marayun ta gama, kuɗin ta sake kalla ta kalli Nabila, sai kawai ta nufi wurin kayan islamiyarta ta buɗa littafin ta na hisnul muslim ta saka kuɗin ciki da tunanin Allah ya kaisu safe lafiya ta tambaye ta ta ji ina ta same su? Duk da ta san Nabilar na wasu halaye da kullum kake jin hayaniyarta da uwar marayu, amma bata so a ce gaske ne abinda ta ji zuciyar ta na raya mata, bata fatan à ce ƙin jin Nabila har ya kai wannan matakin.

*ME CE CE DAMUWAKI*?

Rashin ni'ima?
Rashin gamsar da mai gida?
Warin gaba?
Bushewar gaba?
Ƙaiƙayin gaba?
Kurajen gaba?
Zubewar nono?
Cikowar nono ?

*Kina buƙatar...*

Fatarki tayi laushi?
Tayi santsi?
Ta kwanta luf?
Kina walkiya da annuri tamkar amarya?
Sabulu kike so ko haÉ—in shafawa ki wanke ko mai na shafawa?
Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida?
Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba?
Humra da zata tayar da sha'awarsa?
Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi?
Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki?
Turaren wuta irin na asali barebari?
Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi?
Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki?
Turare don yaranki?

_Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki.

Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haÉ—i irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haÉ—in *kayan marmari*.

*Garabasa*

Ga waÉ—anda sukayi nisa kuma haÉ—in kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuÉ—in mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haÉ—i irin na kayan daya shafi na marmari da É—anye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*.

*JANNAT HOUSE.*🧕

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HARUN*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*2*

Yana kai wannan ruwan ya juye ya fito, kai tsaye bakin titi ya nufa da niyyar siyan magani ya sha sannan ya ci gaba da zuwa ɗaukan ruwan, amma yana zuwa sai ya ji yunwar cikinsa ma ta isheshi, dan haka ya ga ya fi buƙatar abincin fiye da maganin, bredi ya siya na goma da kunu na goma, haka ya dinga cin bredin yana kora shi da kunun da ko sugar babu, Alhamdulillah dake ya ci da sunan Allah ya kuma yi hamdala bayan ya kammala sai ya ji ya dawo hayyacinshi, dan haka ya ɗauki jarkokin ya sake nausawa gidan su Ummu dan ci gaba da ɗauko ruwan.

*Sa'ilin* da ya gama É—auko ruwan gabaÉ—aya ya kwanta a farfajiyar gidan inda ke É—auke da kayan shinfiÉ—arshi da duka kayan da suka shafe shi, dan wannan haka ya taso ya gani, ba wani dalili da ke sa ya shiga É—akin matar Baban nashi, wannan rumfa dake farfajiyar gidan ita ce É—akinshi kuma wurin hutun shi.

Saida ya cire rigar shi saboda zafi ga gumin da ya haɗa sannan ya fara shinfiɗa dan ya kwanta, masifar raɗaɗin da kanshi ke masa duk sanda ya duƙa yasa ya zauna ƙasa ya dafe kan nashi da shi bai ma san ya kumbura ba saida malam Sule ya gaya mishi... *Wani* irin nishi ne ya dinga fitowa daga ɗakin da iyayen nashi suke, rintse idanu yayi da ƙarfi ba tare da ya kalli ɗakin ba ya furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !"

Wannan tashin hankali da me yayi kama? Me yasa mahaifin nashi ke yin haka? Me ya sa suke haka? Me yasa ba zasu yi abun su a sirrince ba? Da sauri ya buɗe idanu shi ya miƙe da sauri ya nufi hanyar fita, ƙofar gida ya je yayi zaune kan dakalin da ruwa ke taruwa na banɗaki, ya gagara sabawa da wannan ɗabi'ar tasu da suke son saba mishi da ita, ya saba da horon yunwa da dukan mahaifinshi, kyara hantara, zagi duk ya saba dasu daga gareta itama, amma wannan abun nasu, tun bai san me ye ba, tun bai san me wannan kururuwar tasu ke nufi ba, tun bai gane menene ke faruwa ba har ya zo a makaranta aka sanar dasu akwai wata alaƙa dake shiga tsakanin ma'aurata, hakan yasa ya fahimci abinda mahaifinshi da matarsa suke aikatawa a irin wannan lokacin, wanda a makaranta malam ya faɗa musu cewa manzo Allah (S. A. W) ya ce kuyi nesa da ko da jariri ne dake bacci daga gare ku, ƙarin bayanin da malamin su ya musu shi ne idan yaro ya kasance hakan na faruwa a kunnuwa shi ko idanu shi, ya kan yi wuya ya manta abun, idan kuma Allah bai shirya maka ba yaro zai yi sha'awar aikata irin wannan abu dan shi ma ya ga ana yi.

Wannan ƙuncin ne yasa zuciyar sa karyewa ya fashe da kuka tare da haɗa kanshi da guiwa, bai san me matar Babansa ke so da shi ba? Bai san me take nufi da rayuwarsa ba? Amma gaskiya ya gaji da ganin tsiraicinta, ya gaji da yawan nuna masa tsiraicinta da take musamman idan mahaifi sa baya nan.

Bacci ne ya ɗaukeshi daga nan har yayi kwance kan dakalin, mahaifinshi kuma bayan sun gama abinda suke ne ya fito dan yin wanka, ganin baya kwance a shinfiɗarshi yasa ya zuro jallabiya ya fita yana mitar wannan yaro ya rainashi. Samun shi kwance a kan dakalin yasa ya dafe ƙugu yana tunanin ta yadda zai fara tashin shi, daga ƙarshe takalmin ƙafarshi silifas ya cire mai nauyin gaske ya ɗaga iya iyawarsa sannan ya kwantara masa shi a ɗuwawu... Wata mahaukaciyar zabura Jabir yayi idanunshi a rufe gam gam yana ƙwalla ihun "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallahu wani'imal wakil !"

Duk yana maganar ne yana sosa É—uwawunshi da ya ji kamar zasu fita, a haukace mahaifin nashi ya sake kashe fuskar shi da gigitaccen mari yana daka masa tsawar "Shiru! Yi min shiru, É—an iska kawai, maza wuce ciki."

Wallahi sai lokacin ma kaɗai ya gane wanene ya dakeshi, dan haka ya dakata daga juyin da yake yana faɗin "Dan Allah Baba kayi haƙuri, kayi haƙuri wallahi ba zan ƙara ba."

Bayar da haƙuri da alƙawarin ba zai ƙara ba ya zama jikin shi ta yadda ko bai san abinda yayi ba zai bayar, tsawa ya sake daka masa yace "Wuce ciki nace, in ba iskanci ba da son ka ja min zagi, ga cikin gida miye na fitowa waje ka kwanta Jabir? Dan kawai kana so ka ga a unguwar nan ana zagina da cewa bana kula da kai."

Da sauri sumui-sumui ya shiga ciki ya bi bayan shi yana ci gaba da masa faÉ—an ya kwanta waje. Suna shiga da sauri ya ma manta da ciwon da kansa ke mishi ya shiga yin shifiÉ—ar, yana gamawa ya kwanta lamo duk da a lokacin baccin ya fita idanunshi, hakan yasa ya jima bai yi bacci ba yana tunanin rayuwarshi da burin dake ran shi.

*DA SAFE*

Shigowarta ɗakin kenan daga wanka tana shirin tafiya islamiyya ta samu Naila ita har ta shirya sai haukan neman kuɗi ta take na jiya duk ta birkice kayan ɗakin, sanin me take nema yasa a tsanake ta ƙarasa shiga tana cire hijabin ta ta aje kan jakar kayan ta tana faɗin "Me kike nema haka?"

Ba tare da juyo ba tace mata "Wani abu."

Taɓe baki tayi tana kallon bayan data bata tace "Wani abu ko kuma jaka biyu?"

Da ƙarfi ta juyo ta sauke dubanta kan Ummu data fara shafa mai, sai kuma ta matso kusanta ta tsuguna da sigar rarrashi tace "Aunty Ummu, idan kin ganta dan Allah ki bani, wallahi ba kuɗina bane Safara'u ta bani ajiyarsu."

Da idanu ta tsare ta sai da ta gama maganar tace "Safara'u? Ita ina ta samu kuÉ—in? Nabila na san ki fa."

Marairaicewa tayi tace "Wallahi aunty na Safara'u ne, ki bani na kai mata kuÉ—nta kar su Mama su ji ma."

Jinjina mata kai tayi cike da gargaÉ—i tace "Na ji zan baki, amma wallahi Nabila idan na sake ganin ki gidan samarin nan dake karatu sai na gaya wa Baba, kin ji ko?"

Da sauri ta jinjina kai tana ma Ummun kallon _"Sam aunty ba zaki gane ba, ban da abin ki zan zauna na rayu cikin talauci ne da rashin kayan more rayuwa?"_

Ummu da taji ba tace komai ba ne tace" Ki ban amsa da baki, kuma ma wai in tambaye ki? Me yake kaiki gidan su tunda kinsan duk maza ne?"

Da fara ƙaguwa da zancen Nabila ta kyaɓe fuska tace" Aunty ba fa wani abu ke kai ni ba, jiya ma da kika Ganni ɗaya daga cikin su ne ya aikeni na siyo masa abu."

Hararenta tayi tace" Ki siyo masa me?"

Da alamar rashin gaskiya tace" Sigari, kuma wallahi da naje ban samo ba na maido masa kuɗinsa, amma ba zan ƙara ba, ni dai dan Allah ki bani kuɗin."
Chapter 3 · 0% Book details