← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 168

Sashe 7

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk da tafiya yake, amma haka ya ɗan dakata ya zura ƙafar ɗaya ya sosa ƙafarshi wanda ya tattare Ƙafar wandon har wuce ijiyar-sau, da azama ya ci gaba da tura kurar ruwan da yake ɗaukowa haya dan so yake yayi sauri ko ya gama ya zauna ya huta saboda Ƙafar nan tasa sai ruwa take yi.

Yana karyo kwana kenan ba tare da sanin zai ganta a nan ba sukayi kiciɓis, matar Babanshi ce yau bai san me ya dawo da ita da wuri daga wurin aiki ba, tana kan babur ɗin ta tare da wata mace da alama gaisawa suke yi, cikin rashin jin daɗin ganin ya turo ruwan nan sannan matar da suke gaisawa ma yana kai mata ruwa ya lumshe idanu tare da ci gaba da turawa dan dukansu sun ganshi tunda suna kallon kwanar ne.

Yana kawowa daf da su da ladabi ya kalle ta yace "Sannu da dawowa aunty."

Sai kuma ya kalli matar dan yasan ba amsa masa zata yi ba yace "Ina kwana?"

Da fara'a matar ta amsa mishi da "Lafiya lau Jabir, har an É—auko ruwan?"

Kasa amsa mata yayi sai murmushi kawai, ita sam bata san akwai sanayya tsakanin Jabir ɗin da Bara'atu ba bare wata dangantaka ko alaƙa, dan haka da taga yayi haramar wucewa sakamakon kallo mai ma'anoni da mamakin ganin shi da kurar ruwa da matar Baban nashi ke masa yasa ta cewa "Jabir, idan ka kai ruwa dan Allah ka sake tunawa Firdausi ta kai min niƙa kafin na dawo, dan na barosu suna kallo tana iya mantawa."

Sororo Jabir ya juyo ya kalle ta, sai kawai ya jinjina kai ba dai tare da ya amsa ba, kuma hakan bai dame ta ba ita ma dan a zaman da sukayi ta fahimci yaro ne miskili da bai cika magana ba, dan ko yaran ta suna son janshi da wasa da hira, amma shi sai dai yayi shiru ko murmushi bai cika magana ba.

Har ya wuce Bara'atu na sake juyawa ta kalle shi, sai kuma ta kalli matar nan tace "Maman Firdausi, waccen yaron shi yake kai miki ruwa?"

Da fara'a tace "E wallahi, kin san ruwan nan idan ba tsayayye gareka ba sai ka sha wahalar rashin ruwa, amma Kinga tunda na samu Jabir wallahi hankalina kwance, gashi baya da matsala yaron wallahi komai kika bashi karɓa yake yayi godiya."

Tsura mata idanu kawai tayi tana jinjina kai, a zuciyar ta kuma hangowa take har ta faɗawa ubansa ce wa ya zama ɗan ga-ruwa da yadda zai dakeshi, da haka sukayi sallama matar na ƙorafin Bara'atu bata taɓa leƙawa gidan ta ba, ita kuma tana murmushi tana cewa za ta je, amma a ranta ayyanawa take _"Me zan je na tsinta, ni sam rayuwarku bata min ba."_

Ƙwarai Jabir ya san ya kaɗe, dan haka yana gama kan ruwan ya mayar da kurar, cikin kuɗin da ya samu yau bai kai wajen madame ta aje masa ba kawai ya tafi da su ya siyo su alawa da biscuit da saurensu da niyyar kai wa Uzei, hakan ko zai sa ya zama toshiyar baki ga matar Babanshi.

*Har* zai wuce ta ƙofar gidan samarin nan ya hangi Nabila tana ɗiban ruwa dake ƙofar a buɗe take, yanayin da ya ganta kuma ruwan a bokitin wanka ne ta ɗiba za kuma ta shiga banɗaki sannan da ɗaurin ƙirji yasa shi dakatawa.

Abinda bai taɓa tunanin yi bane ya aikata, dan kuwa tsaf ya tura ƙofar da sauri ya shiga tare da kallon ta sa'ilin da ta ji tsoro ta tsaya turus dan bata ɗauka ƙofar a buɗe take ba, cikin taushin murya amma kuma a kausashe yace "Ke Nabila, wai ba na ji Ummanku tana hanaki zuwa gidan nan ba? Me kike yi hka da zkiyi wanka bayan ga gidan ku?"

Turo baki tayi tna kawar da kai ba tace komai ba, a tsawace ba alamar wasa yace "Maza canza kayan ki ki bar nan ko naje na sanar da Ummanku."

Jiki a sanyaye dan Jabir tsaran Yayanta Mujittafa ne ta aje bokitin ta juya da niyyar komawa ta sako kayan ta ta fita, sai dai saurayin da yayi nasarar ribantar yarinyar yau bayan jimawa yana kwaɗayinta, yau gashi har ta saki jiki dashi sukayi wasa har ta zama silar tsiyayar da ruwan jarabarshi, hakan ba ƙaramin daɗi ya masa ba dan yana hango yadda haɗuwarsu ta gaba zata kasance har ya kai ga zuwa matancinta.

Dake ya fi Jabir shekaru sosai sai kawai ya haÉ—e fuska yace "To kai ina ruwan ka? An gaya maka b'a san ta zo bane? Kaga fita a nan, ruwa ne kake kawo mana ka bar shi daga yau bana so, kuma idan na sake ganin ka saka mata ido wallahi zaneka zanyi."

Da sauri Jabir ya kalli tsakiyar idanun saurayin, sai kawai wani murmushi ya so suɓuce masa amma sai ya dake kawai, tabbas ya girmeshi kuma zai iya wahalar dashi idan dakuwa zasuyi, amma ya zaneshi? Sam abune da ba zai yiwu ba, to ai ko mahaifinshi biyayya da girman haihuwa ne yasa yake yin shiru yake Dukanshi, amma ba duk da haka da yaya yake tanƙwarashi yanzun?

A gadarance tamkar wanda ya taso a gidan sarauta ya kalli Nabila fuskar shi a haÉ—e yace "Na ce ki É—auko kayanki ko?"

Da sauri sauri Nabila ta kama hanyar ɗakin, hakan ya ɓata ran saurayin har ya matso daf da shi yace "Kai! Wai raina mutane ne kayi? Ina ruwan ka da ita? Ka fice min anan nace ko?"

Ba alamar tsoro Jabir yace "Ita nake jira dama, da ta fito ai fita zanyi."

Cike da takaici saurayin yace "OK, haka ka ce? To ina zuwa, dan Allah idan ka isa ka tsaya na same ka a nan."

A fusace ya juya zuwa cikin ɗakin, da kallo Jabir ya bishi sannan ya taɓe baki ko a jikinshi, bai gusa daga nan ba, bai matsa daga inda yake ba har saurayin ya fito tare da Nabila a bayanshi shi kuma yana riƙe da belt ɗinshi.

Saida yayi mamakin sake ganin Jabir É—in tsaye bai tafi ba, hakan yasa har yaji anya kuwa? Karfa a zo ya sha ruwan kunya! Ai kuwa yana zuwa a fusace cike da son birge Nabila ya É—aga belt É—in nan zai zabgawa Jabir yana faÉ—in "Kai marar kun..."

Tun bai ƙarasa faɗa ba Jabir ya riƙe belt ɗin a fusace shi ma yana faɗin "Wallahi ka dakeni ba zan kasa ramawa ba tunda baka haife ni ba."

Da gudu Nabila ta ƙaraso ta shiga tsakiyarsu tana faɗin "Dan Allah Ashir ka ƙyaleshi, ka rufa min asiri kaji? Kai baka san idan kuka yi hayaniya aka shigo ba nan za'a san me ya faru bane?"

Hakan yasa Ashir ɗin dakatawa tare da nuna musu ƙofa dukansu yace "To ku fice min a nan kafin na ji wa wannan yaron ciwo."

Nabila ce ta fara yin gaba tana cewa Jabir "Muje dan Allah."

Bin ta yayi a baya suka fita daga gidan, tunda suka fita kuma bai ce mata ƙala ba, tana dai gaba yana biye da ita a baya kamar mai tsaronta, ganin sun tunkari gidansu wanda kafin ta fito ma ta baro mutanen arziƙi da maƙota ana ta shirye shiryen ɗaurin auren aunty Ummu gobe, ita kuma dama sam auren Alhaji Kabir ɗin bai mata ba Shiyasa ba ruwanta da sabgar, tunanin kar ya je ya tona mata asiri ya sa ta juyowa ta tsaya a marairaice tace " *Yaya* Jabir, dan Allah dan Annabi kar ka faɗawa Mama ka ganni zani wanka a can, dan Allah kaji?"

Yana so ya mata magana, irin maganar nan ta Yaya da ƙanwa, faɗa yake so ya mata mai cike da hargagin da zai iya ɗauke fuskar ta da mari, sai dai kashh! Bakin shi ya masa nauyi, sannan yana ganin ai bai da wata alaƙa da ita da idan ya faɗa zata ɗauka har tayi anfani da shi, dan haka sai kawai ya bita da wani kallo kamar na ki shiga hankalinki sannan ya raɓata ya ci gaba da tafiya. Gadan gadan gidansu ya tunkara, dan haka ta dinga binshi cikin sanyin jiki har suka isa ƙofar gidan.

*ME CE CE DAMUWAKI*?

Rashin ni'ima?
Rashin gamsar da mai gida?
Warin gaba?
Bushewar gaba?
Ƙaiƙayin gaba?
Kurajen gaba?
Zubewar nono?
Cikowar nono ?

*Kina buƙatar...*

Fatarki tayi laushi?
Tayi santsi?
Ta kwanta luf?
Kina walkiya da annuri tamkar amarya?
Sabulu kike so ko haÉ—in shafawa ki wanke ko mai na shafawa?
Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida?
Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba?
Humra da zata tayar da sha'awarsa?
Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi?
Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki?
Turaren wuta irin na asali barebari?
Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi?
Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki?
Turare don yaranki?

_Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki.

Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haÉ—i irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haÉ—in *kayan marmari*.

*Garabasa*

Ga waÉ—anda sukayi nisa kuma haÉ—in kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuÉ—in mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki hada, ba iya guda kawai ba, dama sauran haÉ—i irin na kayan daya shafi na marmari da É—anye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*.

*JANNAT HOUSE.*🧕

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HARUN*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*4*
Chapter 7 · 0% Book details