← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 168

Sashe 33

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi likitan yayi ya kalli Sa'ad da yanayin zolaya yace" Boss, da alama ka samu wacce za ta iya tafiya da kai."

Lumshe ido yayi ba tare da ya motsa daga yada yake ba yace" Bar shashanci, kayi aikin ka."

Maida hankalin shi yayi ga Aisha yace" Aisha, ki nutsu ki amsa tambaya ta, shin ba kya jin wani abu da ya shafi haka ciwon ciki? Ciwon mara? Kasala? Ko ciwon kai haka?"

Shiru tayi tana tunanin abubuwan da ya faɗa, to ita za ta iya cewa wataƙila aikin da azzaluman nan suka mata ne, dan haka ta ɗaga kai ta kalle shi tace" Gaskiya dai...watana da ya zo ne nayi ciwon ciki sosai."

Daga likitan har Sa'ad sun fahimci me take nufi, wanda Sa'ad ya ji gabanshi ya faɗi ba gaira ba dalili, ɗaya ɓangaren kuma ya ji daɗin amsar da t bayar har ya ji ya martaba shekarun ta da suka bata damar hangen nesa, kallon ta likitan yayi da kulawa yace "Kuma ba kya jin haka a ɗabi'a?"

Kanta a ƙasa cike da kunya ta girgiza kai tace "Gaskiya bana yi ko kaɗan."

Ta ƙasan idanu Sa'ad ya kalle ta, da wasa wasa sai zuciyar sa ke raya masa anya kuwa? Anya kuwa anyi *jarababbiya* a wurin nan? Yayin da likitan kuma yace "Bayan haka kuma bai sake miki ciwo ba?"

Girgiza kai tayi alamar a'a, dan haka ya kalli Sa'ad yana wasa da hannayen shi yace "Boss, ina ga nan da k..." Aisha da ta taɓe baki jin yana kiran shi da sunan ƴan daba ne tayi saurin cewa "Na tuna, ranar ma ya min ciwo har Mamie ta bani magani, sannan kuma..."

Ta faɗa tana dafe cikin ta tace "Anan inda aka min ɗinki, yana ɗan yi min Ƙaiƙayi wurin wasu lokuta."

Da son É—auke hankalin ta daga wannan aiki da kuma son tabbatar mata ba shi da masaniya akan komai Sa'ad yace "ÆŠinki?"

Jinjina kai tayi har da É—an É—aga mishi gira tace "E, wani likita ne da ban san shi ba ya farke min cikina, kuma ban mishi komai ba."

Miƙewa likitan yayi yana ɗaukar wata sabuwar safar hannu tare da cewa "Zo kwanta nan in duba ki in gani?"

Jiki a sanyaye t miƙe tana kallon Sa'ad ɗin, yanayin shi ya ji yana so ya canza, kamar tashin hankali yake ji na son ziyartar shi, kamar wani abu yake ji mai kama da tsoro ne ko haushi? Shi bai ma sani ba, amma dai a gajerar kalma zai iya cewa *bai ji daɗi ba da likitan nan zai duba cikin ta*, hakan yasa har ya ji kamar yana ɗan jin haushin komai na likitan haka da ma likitan kan shi.

Ba su fi minti uku ba ya dawo ya zauna kujerar shi haka ma Aisha, kallon shi yayi yace "Boss, ina ga a gaggauta yi mata aikin nan dan lafiyar ta kar ta fara salwanta."

Kallon shi yayi a wani daƙile yace "Yaushe kake gani to?"

Cikin nutsuwa yace "Ka fara kawo ta gobe da sassafe zan sa a mata hoto da kuma eco dan na ga mazaunin abinda yake cikin ta, idan ya so sai mu saka lokacin aikin, sai dai ba zai wuce gobe ko jibi ba."

Cike da gamsuwa ya jinjina kai tare da Miƙewa yace "Shikenan, Allah ya kai mu goben." Miƙewa tayi suka tafi, kai tsaye kuma bai zame ko ina da ita ba sai gida, sai dai gaggawa ta sa bai zauna ya ce ma Hajia komai ba, sai dai ya sake mata alƙawarin gobe zai gaya mata idan sakamakon Aisha ya fito na aune-aunen da likitan ya ce zai mata.

*Washe Gari*

Bayan fitowar sakamakon likitan ya tabbatar masa da za'a mata aiki, tsoron abinda zai iya faruwa yasa shi faɗa ma Hajia Kaka cewa "Hajiata, jiya da muka je asibiti yarinyar nan nasa aka duba, ashe tana da ɗinki a cikin ta wanda aka mata bayan an mata wata tiyata, abinda binciken likitan ya ce shine, akwai wani ciwo ne a cikin ta da yake ɗan sakata ciwon ciki, da na tambaye ta kuma ta ce wata asibiti ce da aka satosu ita da wata aka kawo su nan, tana kallo aka kashe ɗayar ita kuma aka barta a raye, ɗazu ma da safe da muka tafi asibiti radio aka mata, kuma likitan yace dole anjima a mata aiki dan kar abu yayi girman da ba zai taɓu ba."

Daidai dire maganar shi Aisha ta fito daga ɗakin Hajia kakan riƙe da carbinta da ta ce ta ɗauko mata, da kallo ta bi Aishan har ta zo tana miƙo mata carbin, karɓa ta yi tare da kamo hannun Aisha ta zaunar da ita kan ƙafafun ta cike da tausayawa tace" Aishatu na, ashe baki da lafiya baki taɓa gaya min ba?"

Sunkuyar da kai Aisha tayi ba tace komai ba, hakan yasa Hajia Kaka ɗaga rigar atamfar Aisha daga ƙasa tana cewa" In gani?"

Ɗan ƙara ɗagawa tayi dan Hajia kakar ta gani da kyau, sai dai ba ita Kaka kawai ta gani ba har da Sa'ad da ya zuba musu idanu yana kallo, amma ganin cibiyar ta irin mai tsinin nan kuma bata da girma sosai sai ya ji kamar bai dace ya kalli al'aurar ta ba, hakan yasa ya shiga sissine kai shi kaɗai kamar mai jin kunya haɗa ido da siriki, da ƙyar ya iya ganin shatin ɗinkin irin na tsayen nan ne tun daga ƙasan cibiyar ta da kaɗan har bai iya hango inda ya tsaya ba, hakan kuma bai rasa nasaba da siket din dake jikin ta.

Kallon shi Hajia tayi tace "Sa'ad, wane lokaci to za'a koma asibitin?"

A sanyaye ba tare da ya kalle su ba yace "Ya ce da ƙarfe 05 mu isa, zuwa 06:00 zai mata aikin."

Jinjina kai Hajia tayi tace "Shikenan to, zan tafi tare da ku sai na ci gaba da kulawa da ita, amma kuma Sa'ad tunda wannan É—inkin bai jima ba, kana ganin ba matsala a sake fasata da gaggawa haka?"

Girgiza mata kai yayi yace "Ya ce ba matsala, kamar ayi aiki ne a samu matsala, ana gaggauta gyara matsalar ko da kuwa sai an sake fasa mutum."

Jinjina kai tayi tace "Allah ya sa ayi à sa'a." Ta faɗa tana jawo kan Aisha ta rumgume a ƙirjin ta, miƙewa Sa'ad yayi ya bar musu ɗakin, inda Hajia kuma ta ɗaga Aisha tace "Miƙo min wayata a can kan teburi na kira tela na gaya mishi zan tafi tare da ke asibiti nayi jinyarki har a sallame mu."

Da sauri Aisha ta miƙe ta je ta kawo mata wayar, bayan ta kira Alhajin ta gay mishi sai da ya ji ba daɗi na zargin da ya ma Sa'ad kan tunanin zai fita da Aisha ne kawai dan ya mata wani abun, amma yanzu da ya ji haka sai ya gano Dalilin fitar shi da ita asibiti jiya kenan, da tabbaci ya ce ma Hajiar zai je asibitin bayan an mata aikin ya duba ta, daga haka sukayi sallama.

*An mata* aiki cikin nasara kuma an ciro wannan bala'i da aka zuba mata a ciki kalar ledar har ta canja kala, duk da ɗaya robar ta bashi wahala wajen cirewa, tayi nesa da inda aka ajiye ta sannan ta yi taushi sosai saboda mugun zafin ciki, hakan ya sa da ya taɓa sai ta huje da ƙyar da dubara ya ciro ta ya sake mata wani sabon ɗinki cike da ƙwarewa irin ɗinkin nan na ciki wanda idan ya warke ba lallai ka gane mutum na da aiki a cikin shi ba.

Gado a ka bata a sashe na musamman na kuÉ—i, inda Hajia Kaka kuma ta zauna da ita na kwana uku a asibitin har aka sallama ta suka koma gida.

*Bayan Kwana Biyu*

Ya so yin sallama, amma tsinkayar Aisha da yayi tana ƙoƙarin duƙowa daga tsaye ta ɗauki jug ɗin ruwa bai san Dalilin jin jikin shi na tsuma ba kawai ya taho a sukwane yana faɗin "Dakata malama..."

Yana ƙarasowa ya duƙa ya ɗauka sannan ya miƙa mata yana kallon yadda take ta tattare zane dan yanzu dole take anfani da su, cikin yanayin masifa yace "Ba ki da hankali ne, ruwan ne ba zaki jira a zo a baki ba? Baki san an hana ki motsa jikin ba bane da har kike shirin duƙawa ?"

A marairaice Aisha dake sanye da t-shirt fara ta tattare ta har ƙrjin ta, sai zanen da gaba ɗayan shi yae hannun ta tana ta riƙo saboda baya ɗauruwa sosai a ƙasan mara. Kafin ta ce wani abu Sa'ad da duk yake jin ya damu da lafiyar ta ya kama hannun ta na dama, hakan yasa ta kalli hannun nashi sannan ta ɗaga idanun ta da suka ƙara shanyewa sakamakon har yanzu ɗan kumburin da tayi bai gama sacewa duka ba ta kalle shi, shi ma kallon ta yayi sai kawai ya basar ta hanyar juya mata kai ya shiga jan ta a hankali tana takawa yana cewa "Ki dinga kula da lafiyar ki mana."

Saida suka zo kan kujerar ya kamata ta zauna da kyau sannan ta kalle shi cike da jin daÉ—in irin kulawar da yake bata tun da aka mata aikin nan tace "Nagode Abbu."

Ba tare da ya kula ta ba ya kalli ƙofar ɗakin Hajia Kaka yace "Ina Hajia?"

Saida ta fara buÉ—e jug É—in ruwan tace "Tana É—akina, kayan wanki da suka taru take cirowa."

Jinjina kai yayi har idanun shi suka sauka kan ƙafafun ta da suka fi komai kumburi, a hankali ya durƙusa gaban ƙafafun nata har ya sa yatsa ya latsasu, sai kuma ya kalli fuskar ta yace "Me yasa ba su daina kumburin nan ba?"

Girgiza kai tayi tana ƙara gyara zanen ta gudun kar ta sakar masa wani abu tace "Ban sani ba nima."

ÆŠan gyara tsugunnon shi yayi yana lalubo waya daga aljihu yace "Bari in kira likitan nan in faÉ—a masa, *bana son ganin haka* gaskiya."

A tausashe sosai Aisha tayi saurin cewa "Abbu, ba sai ka kira shi ba, zan warke fa, haka nayi waccen ma."
Chapter 33 · 0% Book details