← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 168

Sashe 108

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai Ummu tayi ta kama hanyar madafa, amma ƙarar wayar ta yasa ta dakata tare da dawowa ta ɗauki wayar, *Aunty Nur*, shine sunan da ya bayyana, kawar da kai tayi da yanayin an fara takura ta, ƙin ɗagawa tayi sai da kiran ya tsinke sannan tayi saurin buɗe wayar t sauke layukan nata tare da aje wayar ta ƙara nufa madafa...

Sallamar Alhaji da kuma muryar Mama da ta ɗauka yasa ta dakatawa da ɗumbin mamaki tana kallon ƙofar, ai ko sai ta ga suna shigowa da ɗaiɗaya, Mama, malam Adam, da kuma Alhaji Sagir da shi kan shi Alhajin, mamaki dai kam bai barta ba gaskiya, tunda biyun ai basu jima da rabuwa ba, to kuma me ya kawo su yanzu? Musamman ma Mama da gaba ɗaya zuwan da tayi gidan nan nata ƙidayayye ne.

Haka dai ta tarbe su ba tare da ta ɗauko hijabi ba, dan dukan su iyaye ne a wajen ta har shi Alhaji Sagir ɗin, saida dukansu suka zauna ta miƙe tace "Bari a kawo ruwa, amma Mama wani wajen zaku je ko?"

Da sauri Alhaji ya dakatar da ita da cewa "Ki bar ruwan nan, zo ki zauna."

Kallon shi sai taji gaban ta ya faɗi, jiki a sanyaye ta koma ta zauna ƙasa kusan ƙafafun Mama har tana dafa guiwar Maman da tashin hankalin ta ya fi na Ummu, tunanin ta ɗaya shine ko iyayen Ummu sun biyo ta hannun shi ne? Inda Ummu kuma tunanin ta ya fi raya mata matsalar auren Nabila ce, saida duk aka yi shiru kowa yana jiran ya ji daga bakin Alhaji da ya tara taron, sai suka ji yana ce ma Kuwailat "Auta, tashi ki je wajen Hajiar Khamis ina zuwa."

Da ladabi ta miƙe bayan ta amsa mishi da to ta fita, zuba masa idanu Ummu tayi, ta fara hango wani abu na daban yanzu, anya kuwa ba ƙarar t zaiyi wajen Mama ba akan gamin da ta masa wajen Alhaji Sagir? Ya kuwa san Mama? Nan fa tana iya gyara zama ta tsinke ta da mari? Anya Alhaji kuwa tsufa bai fara gigita shi ba?

Kallon su Mama yayi cikin nutsuwa ya fara magana "Kuyi haƙuri da taraku da nayi akan abinda nasan ba zai muku daɗin ji ba, sai dai ya zama dole na sanar da ku dan maslaha muke nema, sannan ina so daga ƙarshe ku min kyakyawar fahimtar da ko kun ji hukuncin da na yanke, to ina so mu ci gaba da zumuncin mu da kuma mutumta junan mu kamar yadda muke a baya, Hajia..."

Ya kira Mama yana kallon fuskar ta, ɗaga kai Mama ta sake yi ta kalle shi da nutsuwa tana sauraren shi, ɗorawa yayi da" Wata matsala ce ta ɗan kunno mana kai zamantakewata da Ummu, lokacin da ta fara min ƙorafi akan rashin samun yadda take so, sai nake kallon ta marar haƙuri ba kamar sauran matan nawa ba, to amma jiya zuwa yau sai na sake yin nazari kan matsalar, sai naga ai shekarun Ummu duk bata wuce ƴa a gurin matan nawa ba, sannan idan ƴata ce a wannan halin gudun kar ta faɗa halaka zan iya neman alƙali a da ya raba auren ta, wannan yasa nayi dogon tunanin kafin na yanke hukuncin da na taraku dan ku ji, kuyi haƙuri dan Allah kuma kar ku ƙullace ni, ban kira ku dan na ci fuskar ku ba, kuma ba na kira ku dan kawai ku shaida bane, amma na kira ku ne saboda girman da kuke da shi a idanuna, sannan ina so ku fahimci abun kamar yadda na fahimceshi nima, duk da sirrin mu ne wanda ban so fitar shi ba, amma dai nasan ku ma kun san daga ganin zamana da yarinya kamar Ummu kun san akwai cutarwa, a yau ɗin nan dana zurfafa tunani, na ji nayi nadamar auren ƙaramar yarinya kamar Ummu, wallahi tallahi na ji ina ma ina iya dawo da hannun agogo baya? Da ban yarda na auri Ummu ba, amma tunda haka ta faru mu bar shi a matsayin rabon haihuwar Kuwailat ne ya haɗa ni da ita, dan haka..."

Sai kuma ya kalli Ummu da ta zuba mishi idanu hawaye har sun fara ɓata kwalliyar da ta caɓa saboda shi, murmushi ya mata ba tare da ya daina kallon ba yace" Kiyi haƙuri Ummu, ke yanzu kamar tsuntsuwa ce, ba zai yiwu na ci gaba da riƙe ki ba, ni ban barki kin tashi ba kuma ni ban tashi tare da ke ba, ina son ki Ummu, zan iya ce miki tsakanin ke da Hajia Luba ban san wacece ta fi yi min alkairi a rayuwata ba, amma dai nasan idan magana ake ta so, to ke ce ƙaramar su a shigowa gidan nan, kuma babbar su a filin zuciyata, ina son ki, kuma ina son zama dake na har abada, burina bai wuce ki zauna tare da ni har ki min takaba ba, sai dai bamu san yaushe hakan za ta faru ba, dan haka nake so na sama miki ƴanci, dan ba zan so kaina dayawa haka ba, Ummu, abu mafi muni da girma da zaki iya zuwa min da shi nan gaba shine zuciyar ki ta ci gaba da ƙawata miki wasu fuskokin, ba zan so haka ba, gwara nasan ko da kinyi haka to ba saɓo kika aikata ba, dan haka Umm..."

Ummu da kuka ya ƙwace mata da sauri ta girgiza mishi kai, ƙafar Mama ta riƙe gam cikin tashin hankalin da bata ɗauka zata samu kan ta a ciki ba wai dan Alhaji Kabir na neman rabuwa da ita, rabuwa mana, tasan abinda yake shirin yi kenan, cikin kuka mai siririn sautin dake ratsa duk mai sauraro Ummu tace "A'a Abban Kuwailat, in dai nice wallahi na haƙura, kar ka mayar da ni *bazawara* dan girman Allah, wallahi tun ranar da naga kayi hushi ma na cire wannan abun a raina, na roƙeka Alhaji kar ka tona min asiri, ka barni na rayu da ƴata a gidan nan a ƙarƙashin kulawar ka, wallahi zan haƙura nima na maka biyayya."

Kawar da duban shi yayi daga gare ta, sadda kan shi ya yi ƙasa sosai yana girgiza kai, cikin nutsuwa yace "Kiyi haƙuri Ummu, adalcin da zan iya yi miki kenan a rayuwa, Ummu, *na sake ki saki ɗaya*, idan kika samu miji kiyi aure, ina miki fatan..."

Wani irin abu zuciyar shi ke yi, ƙarfin hali ne kawai shima ya yi, ga shi yadda ta rushe da kuka tana ƙamƙae jikin Maman ta ya ƙara tsuma zuciyar shi, kamar ya ce su basu wuri ya rarrasheta ta hanyar rumgume ta jikin shi, kasa ɗaga kan shi yayi saboda shima ƙwalla yake ji a idanun shi, Ummu kuma sai cakumar jikin Mama take tana kuka, Mama tayi suman zaune daddaɓata kawai take, ba ta taɓa tunanin zata iya kallon Alhaji Kabir ta mishi maganar da yanzun take ciciyar ta, amma haka ta kalle shi cikin dakakkiyar murya tace "Alhaji, kuma babu wata mafita sai wannan?"

Bai ma ɗaga kan shi ba bare ya kalle ta, gashi kuma yayi shiru bai ce komai ba, Alhaji Sagir ma kunyar iyayen Ummun ta sa ya ƙi ɗaga kai ya kalle su sai girgiza kai da yake yi, hukuncin ya masa daɗi gaskiya, tunda ba zai iya ba idan ya riƙe ta kuma wani abu mummuna zai faru, ita kan ta Ummu za ta san gata ya mata amma nan gaba. Malam Adam ma ya fahimci zancen sosai da sosai, dan haka shima bai ga laifin Alhajin ba, hasalima matakin da ya ɗauka ya masa daidai, duk da dai Ummu ta fi birge shi, dan ba duka mace ke iya kallon mijin ta ta faɗa masa bata gamsuwa ba, mafi aksari ƙawayen su ne suke sanin haka, shiyasa sai ka ga ba'a samawa matsalar mafita ba sai mace ta ƙara durmiyawa wata babbar matsalar, a haka sai a rabu a wulaƙance ana zargin juna.

Dake yana kusan kujerar Mama ne, É—an matso da kan shi yayi kusan kunnen ta ya raÉ—a mata "Kar ki damu zamuyi magana, ki rarrashe ta kawai ta tashi muje."

Tallabo fuskar Ummu tayi dake ta son duƙar da kan ta, hakan ya ɗan hassala Mama tace "Ke! Dube ni nan, kiyi haƙuri mana aka ce, ba zaki ɗauki *RUBUTACCIYAR KI* a yadda ta zo miki bane? Rufe min bakin nan."

Ta ƙarashe har da hararen Ummu, asali Alhajin take so ta harara, ita dai koma yana kan daidai ai bata ga anfanin ya kira ta ya zaunar da ita sannan ya sakar mata ƴa gaban ta, ya san yadda uwa ke ji kuwa? Ya san me take ji a halin yanzu? Ya yi tunani da kyau kafin ya yanke hukuncin nan? A hassale ta miƙe tare da cicciɓa Ummu ta kama hannun ta suka nufi ɗakin Ummun da lokacin shasheƙa kawai take kamar ranta zai fita, suna shiga ta saki hannun ta tace "Haɗa min abinda zaki iya anfani da shi na tsawon lokaci, daga baya kya zo ki ɗauki sauran."

Madadin tayi abinda Mama ta ce, sai kawai Ummu ta faɗo jikin Mama ta sake fashewa da kuka, runtse idanu Mama tayi saboda suya da zuciyar ta ke yi, a hankali ta sa hannu tana shafa bayan Ummu, tun ita ma kukan da Ummu ke yi yasa ta zubar da hawaye tana faɗin "Kiyi haƙuri kin ji, kiyi haƙuri Ummu, in sha Allah ba zaki tagayyara ba, Allah yana tare d ke, ki ɗauki rabuwar ki da shi ita tafi zama alkairi, kiyi ta addu'a Allah ya musanya miki da mafi alkairi, kin ji ko ? Yo shiru daina kukan bana so."

Cikin matsanancin kuka Ummu tace" Wanene zai fi Alhaji Kabir alkairi Mama ? Wanene zai fi min shi a rayuwata? Mama mai yasa baiyi tunani ba kafin yanke hukunci? Shekarar mu goa sha uku a ce mun rabu? Dama ni ce baya so a cikin matan shi?"
Chapter 108 · 0% Book details