← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 168

Sashe 21

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"E wallahi, yana shigowa ya same ni muna waya ya ce bari ya kaini." Duk tayi maganar tana tafiya inda ita ma Hajir ke bin ta har zuwa ƙaramin falon nasu dake ɗauke da ɗakunan su da kuma na yara, jiki a sanyaye dan maganar gaskiya jin wai tare da mijin nasu za ta tafi wanda yau girkin ta ne kuma bata ma san ya dawo ba ya sosa mata rai ƙwarai, ko dai ya shigo ta ganshi ma? Sannan ya faɗa mata ga in da za su tafi, shikenan sai ya yi gaban kan shi kawai? Dan dai kawai Mardiyya na da kuɗi saboda ƴar babban gida ce, sannan tana taimaka masa ƙwarai da gaske, dan tunda ya yi ritaya ma ita ta bashi jari yake kasuwanci, sannan yanzu haka gidan ita ke aje kayan abinci, kuma bata taɓa nunawa gazawarta ko ta musu gori ba, amma dai ai ba kuma a ce a mata yadda aka ga dama ba, ko dan ta tsufa ne? Ko kuma ta kai shekarun da yake ganin ba ta da wata mamora a jiki?

Mardiyya na fita ta same shi yana jiran ta, dan haka ta shiga motar suka kama hanyar zuwa gidan ƙanwar ta ta dake aure a babban ahalin da kowace uwa burin ta a ce ƴar ta na gidan nan, saboda shaharar su wajen riƙe muƙamai da asalin mai gidan yayi da dama, ga alaƙa mai ƙarfi da suka haɗa da masarautar Agadez, kai tsaye basu zame ko ina ba sai ƙofar katafariyar fadar gidan *Saheeb Ahlan*.

*ME CE CE DAMUWAKI*?

Rashin ni'ima?
Rashin gamsar da mai gida?
Warin gaba?
Bushewar gaba?
Zubewar nono?
Cikowar nono ?

*Kina buƙatar...*

Fatarki tayi laushi?
Tayi santsi?
Ta kwanta luf?
Kina walkiya da annuri tamkar amarya?
Sabulu kike so ko haÉ—in shafawa ki wanke ko mai na shafawa?
Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida?
Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba?
Humra da zata tayar da sha'awarsa?
Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi?
Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki?
Turaren wuta irin na asali barebari?
Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi?
Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki?
Turare don yaranki?

_Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._

Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haÉ—i irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haÉ—in *kayan marmari*.

*Garaɓasa*

Ga waÉ—anda sukayi nisa kuma haÉ—in kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuÉ—in mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haÉ—i irin na kayan daya shafi na marmari da É—anye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*.

*JANNAT HOUSE.*🧕

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HARUN*

*MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A.

Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166

Call: 07038274166 & 07031057802

Location: Kano with nationwide delivery.

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*10*

*Abida* suka ci karo da ita farkon shigar su, da gudu gudu Abida ta taso ta faÉ—a jikin Mardiyya tana fashewa da kukan da ya sake É—aga hankalin Mardiyyar har tayi saurin É—agota tana kallon fuskar ta tace "Abida, lafiya kike kuka? Me ya samu Nuriyya? Ta mutu ne?"

Cikin kuka ta rufe fuska tana share hawaye ta girgiza mata kai tace "A'a, ba ta mutu ba."

Da sauri Mardiyya tace "To me ya faru kike kuka?"

Saida ta ja majina tana ta sauke ajiyar zuciya tace "Na damu sosai da halin da *Æ´ar uwa* take ciki, a madafa fa ta faÉ—i sumammiya, da babu kowa a kusa ba mu san me ye zai faru da ita ba, shiyasa na yanke shawarar zama da ita a duk inda take, dan gaskiya barin ta ita kaÉ—ai haÉ—ari ne."

Ajiyar zuciya sosai Mardiyya ta sauke tare da dafa kafaÉ—ar ta tace" Kwantar da hankalin ki kinji Abida, in sha Allah ba abinda zai faru sai alkairi, yanzu muje na ganta."

Jinjina kai tayi tare da shiga gaba Mardiyya na bin ta a baya cike da tausayawa Abidar da kuma jinjina zuciyar girma irin ta ta, za ka rantse ciki ɗaya suka fito da Nuriyya, ko ita da suke uwa ɗaya ba ta jin ta kai Abida damuwa da ita da nuna mata ƙauna, sosai take jin daɗin yadda Abida ke fara taimakawa ƙanwar ta ta idan ta tsinci kanta a wani hali kafin ita ta kawo mata ɗauki, dan haka suke girmamata da mutumta ta tamkar ƴar uwar su ta jini.

Hawa na biyu suka isa ɗakin Nuriyya, ƙofar ma a buɗe suka same ta saboda likita dake dubata sannan akwai mutane a ciki, kan tabkeken gadon ta suka same ta kwance ba ta san wanda ke kan ta ba, sai likita tsaye yana cire mata abun awon tension daga damtsen hannun ta. Gefen gadon kuma *Fa'iza* ce zaune fuskar ta ba yabo ba fallasa, hasalima kamar abun bai wani dame ta ba saboda yadda ita hankalin ta ma ba kansu yake ba, gefe kuma kuma da kan Nuriyya dake bacci Hajia *Radiya* ce riƙ da hannun Nuriyya tana ta murza tafin hannun ta.

Shigowar Mardiyya ta sa Hajia Radiya faɗin "Mardiyya kin ƙaraso? Shigo ciki, zo zauna."

A hankali ta zagaya inda take ta zauna suna fuskantar juna suka zubawa Nuriyya idanu, Abida kuma na tsaye kusan su tace ma Hajia Radiya "Ammi na sa a kawo mata, sannan na miƙa *Kabil* wajen Papi."

A tausashe ta kalle ta tace "To shikenan, sannun ki da ƙoƙari."

Cike da gadara da yatsina fuska Fa'iza da tunda ta ga Abida ta shigo ta shiga haÉ—e fuska tana wani ciccije baki tace ma Mardiyya "Ina wuni aunty Mardiyya?"

Sarai Mardiyya ta ganta, yi ne kawai ta yi kamar ba ta gani ba saboda ita fa ta tsani Fa'iza kuma bata birge ta, yarinya ba kowa ba ba ƴar kowa ba, amma sai ɗaukar kan bala'i da raina mutane wai ita tana auren babban ɗa ga Saheeb Ahlan wanda kuma yanzun yake minista na man fetur, dan haka tana shigowa da ta ga ta juyo ta ganta kuma ta ɗauke kai ta ƙyaleta sai ita tayi kamar ba ta ganta ba dan ta nuna mata ita ɗin ƴa ce ga *Abdus-salam Asgar*.

Da yanayin dake nuna kamar yanzun ta ganta tace "Kai, Fa'iza ce? Lafiya lau, muna lafiya?"

Ba Ta jira me za ta sake ce wa ba ta maida dubanta ga dattijuwar arzikin nan tace "Ammi, ya jikin nata?"

Kafin ta bata amsa likitan da ya gama haɗa kayan shi ya kalle su yace "Ran ki shi daɗe, jinin ta ya haura kamar dai yadda aka saba, shan magani ba zai rage mata komai ba muddin ba ta cire damuwa da yawan tunani a ranta ba, dan Allah a ƙara kiyayewa, idan kuma akwai abinda ke sakata farin ciki, to a yi ƙoƙarin ganin an sadata da shi kowane lokaci."

Jinjina kai Hajia Radiya tayi tace" In sha Allah likita, mun gode sosai."

"Sai anjima." Ya faɗa yana ficewa daga ɗakin, ganin haka Fa'iza da ita fa ba za ta iya zama anan ga kishyar ta ba wato Abida, miƙewa tayi ta kalli Hajia tace "Hajia ni zan koma, na baro ɓangaren ba kowa, Allah bata lafiya."

Ƙwarai Mardiyya ta ji zafin abinda Fa'iza ta aikata, wannan ne yasa a kowace rana take sake ji a ranta Fa'iza na da hannu a cikin *ɓatan yara biyu* na Nuriyya d suka ɓata ɓat har yau babu labarin su, kasa riƙe ɓacin ranta tayi har saida ta juya ta kalle ta tace mata "Ameen, in da gaske kike."

Da mamakin kalaman Mardiyya Fa'iza ta dube ta da kyau, a hankali ta muskuta ta hanyar gyara tsayuwar ta tace "Ban gane in da gaske nake ba? Me kike nufi?"

Miƙewa Mardiyya tayi tsaye sannan ta juyo ta fuskance ta, hakan ya sa Hajia Radiya tashi tsaye ita ma tana riƙo hannun Mardiyya da faɗin "A'a Mardiyya, ka da kiyi haka, kin ji?"

Cikin ladabi ta kalli Hajian tace "Ba komai fa Hajia, wannan ce kawai nake so na mayar wa da aniyar ta, ina so ta gane abinda take fata ko so ya samu Nuriyya, da izinin Allah ba zai same ta ba."

Da matsanancin mamaki Fa'iza ta ƙanƙance idanun ta tana mamakin lamarin Mardiyyar, kamar dai wacce dama take jiran ta? Kamar wacce dama ta zo mata a shirye? Daga addu'a? Shikenan sai a fassara ta, ajiyar zuciya ta sauke cike da wannan halin nata na ko in kula tace "Ban faɗa dan ranki ya ɓace ba, iya gaskiya ta kawai na faɗa ko da hakan zai ɓata wa wani rai, amma aunty Mardiyya na miki wani abu ne ban sani ba?"
Chapter 21 · 0% Book details