Sashe 41
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Alhaji Ahlan ne ya kalle shi da fara'a yace "Alhaji, abubuwa da dama sun faru da ba zamu tsaya tattauna su da ku ba, amma yarinyar nan da ka gani tun tana wata shida a duniya aka saceta daga gare mu, bau sake sakata a idanu ba sai yanzu."
Da mamaki Alhaji Ibrahim da Hajia Kaka suka kalle shi tare da jinjina lamarin, Hajia Radiya ce ta jawo hannun Aisha ta tallabo fuskar ta suka kalli juna, dariya sukayi a tare Hajiar tace" Kin gane ni?"
A hankali Aisha ta girgiza kan ta sannan tace" Mamie, da gaske kun ahalina? Na kasa yarda da hakan?"
Da sauri Mama Nuriyya ta fuskance ta tana faÉ—in" Da gaske ne Eesha, mu iyayen ki ne, kinga ni c mahaifiyar ki, ni na haifeki Eesha, ga kuma Abbun ki..."
Ta faɗa da nuna mata Abbu Mukhtar, sannan ta nuna Alhaji babba tace" Ga kuma Papin ki, sannan ga Mamin ki..." Ta Nuna Hajia Radiya sannan ta ci gaba da nuna mata sauran tana faɗin" Ga Goggon ki, wannan ma haka, ga Baffan ki, ga kuma kawun ki, ga kuma ƙaramin ƙanin ki, Eesha dukanmu nan ahalinki, baki da sama da mu Eesha, ki yarda dan Allah, kin ji."
Duk cikin wanda aka nuna mata ta fi kafe duban ta ga Kabil, ƙaramin yaro wanda yayi kama da mama Nuriyya kyakkyawa da shi, a hankali Aisha ta matsa kusan shi ta rusuna gaban shi, hannu ta bashi suka riƙe hannun juna gam, murmushi ta mishi tace" Me ye sunan ka?"
Kamar yadda ya saba faÉ—a a makaranta ya faÉ—a mata cewa" Kabil Mukhtar Saheeb Ahlan."
Tsare shi tayi da idanu na sakanni, sai kuma tayi murmushi ta shafa kan shi tare da miƙewa tsaye, a hankali ta juya ta kalli inda Sa'ad yake kamar gunki, ba wai bai ji daɗin ganin ahalinta bane, sai dai dama ya san suna haɗuwa dole su raba su, Aisha kuma a yanzu za ta girmi matsayin shi ne ta yadda ba lallai ma ya iya jerawa da ita ba, shine fa Dalilin da ya sa *ya ƙi haɗata da su*. A hankali ta tako ta zo gaban shi tace "Ka ji me suke faɗa, ya ka ce *Abbu*? Ka yarda da su? Idan baka amince ba babu inda zan tafi."
Da ƙarfi Mama Nuriyya ta sauke wani numfashi ta tsurawa bakin Sa'ad idanu, inda Mukhtar ya ƙara matsowa shi ma amsar shi yake so ya ji, ganin duk shi ake kallo yasa Sa'ad maida hankalin shi gaba ɗaya kan Aisha, a raunane, cikin raunatacciyar murya ya buɗa baki yace "Na yarda mana Eesha."
Daga haka bai sake cewa komai ba sai kallon Hajia Kaka da yake kamar ya ce mata tace Dan Allah su barta nan za su kula da ita, muryar DG suka ji daga baya cikin kwaratsi yana faÉ—in "Aisha ai ba zai iya musawa ba cewa su iyayen ki ne, saboda ya fi ki sanin su dama."
Da mamaki aka sake maida kallo ga DG dake maganar har Aisha ma dake hararen shi tace "Kamar ya?"
Taɓe baki yayi yace "Kamar yadda kika ji na faɗa, Sa'ad ya jima da sanin ke ƴar wacece kuma yasan inda zai samu Ahalin ki, amma son zuciya da mummunan ƙudirin da yake da shi a kan ki yasa yake ɓoye ki baya so kowa ya san ke wacece."
Sama da ƙasa ta sake watsa mishi harara tace" Ƙaryar banza, Abbuna ba zai taɓa min haka ba, da ya san ahalina kafin yau, na tabbata zai haɗa ni da su ba sai sun neme ni ba."
Wani murmushi yayi yace" A ganin ki kenan, amma ai gaya nan gaban ki, ya musa abinda na faɗa ya ce ƙa..."
Cikin ɓacin rai Sa'ad ya nufe shi yana faɗin "DG ka daina wannan wasar bana so, idan ba haka ba zan raunataka a wurin nan."
Alhaji Ibrahim da Sabeer ne suka riƙe Sa'ad ɗin ida Sabeer ke bashi baki "Yi haƙuri abokina, abun bai kai na haka ba ai."
Alhaji babba ne ya gyara tsayuwa yace "Ko ma dai me ye, mu alkairi ya mana tunda ya taimake ta, dan haka zamu tafi da ita yanzu."
Da sauri Hajia Kaka ta riƙo hannun Aisha ta fashe da kuka tana faɗin "Hasbunallah wani'imal wakil, ƴar rainota, ban taɓa tunanin rabuwar mu da wuri haka, lallai na yarda da ake cewa sabo tirken wawa, Aisha bana so ki tafi ki barni, haka ma Sa'ad."
Sa'ad ɗin da Kaka ta faɗa yasa Aisha kallon shi tana ƙanƙance idanu ba ko ƙyabtawa tace" Abbu, da gaske wai ka san komai kafin yanzu?"
A rayuwar nan dai bai taɓa tunanin akwai abinda zai tsorata shi ba bare ya kayar masa da gaba, amma sai gashi tambayar Aisha ta jefa shi a wannan halin na tsananin firgici, sai kuma ya shiga rarraba idanu da fargaban amsa mata tambayar nan, baya so ya mata ƙarya, kuma yana tsoron abinda faɗan gaskiyar zai iya jawo masa a wannan halin, shirun shi ne yayi yawa har saida ta sake matsowa kusan shi tana kallon shi jiki a sanyaye tace "Abbu, ka amsa min mana, ko dai gaskiya ya faɗa?"
Iska y feso daga bakin shi, sannan ya É—aga kanshi sosai ya kalle ta ido cikin ido ya furta "E Eesha, da gaske, amma ba gaskiya bane da ya c..."
Aisha da ɓacin rai da rashin son ɗaukan raini, a tafashe ta ƙura masa idanu tana mishi wani kallo tace "Da gaske ne? To wace manufa ce gareka a kaina?"
Da sauri ya kalle ta yace "Babu Aisha, bana da wata mummunar manufa a kanki sai alkairi, karki yarda da abinda wannan..."
Cike da son ƙara hura wuta DG yace "Shin zaka ce baka sa aka mata tiyata ka loda ƙwayoyi a cikin ta bane? Ai ita Aisha da wayon ta, kuma tana cikin hayyacin ta aka mata aikin."
A razane Abbu Mukhtar ya kalli DG da mamaki yace "Me? Ƙwaya fa ka ce?"
Da sauri Mama Nuriyya ta yo kan Aisha tare da jawo ta kusan ta a rikice ta shiga ɗaga rigar Aisha har tayi nasarar ɗagata ƙasan cibiyar ta ya fito, Mama Nuriyya, Abbu Mukhtar, Yaya Bilal, da Hajia Radiya duk zazzaro idanu sukayi suna kallon cikin na Aisha wanda suka ga shatin dake nuna tabbas ɗinki aka yi duk da ɓaro-ɓaro ba'a gane ɗinki ne saboda kwarewar likitan, sai kuma suka kalli Sa'ad ya ji ya gama sarewa da komai tare da ƙudirin kawai ma ya miƙa kan shi tunda dai dama dole za su raba shi da ita.
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*19*
Cike da makirci DG yace "Uhummm! Kun gani, ba na faÉ—a muku ba."
Da sauri Hajia Kaka ta isa gaban DG, shi ai bai ɗauka tsohuwar nan zata iya taɓuka wani abu ba, Shiyasa ko a jikin shi har ta tsaya gaban shi, ɗaga hannu tayi ta dallawa fuskar shi wani kyakyawan tafi tana faɗin "Shashancin banza..."
Sai kuma ta dinga nuna shi da yatsa tana cewa "Wa ye kai? Me ye tsakanin ka da shi? Me ya maka a rayuwa da son ganin bayan shi ya zama maudi'inka?"
Da irin kallon tsana da takaici yake kallon ta har Sa'ad ya yi gaggawar riƙeta dan shi dai baya son tone-tonen nan a yanzu da ya shiryu, da a baya ne ai ba zai ji kunya ba, dan iyayen shi ma kai tsaye yake faɗa musu gaskiyar magana bare kuma waɗanda basu haife shi ba. Cike da murmushin makirci DG ya shafa kumcin shi yace "Shi ya san waye ni Hajia, ba zan damu ba dan kin mare ni, amma hakan ba zai hanani faɗan gaskiya ba, ƙwarai Sa'ad da ɗaya ogan sune suka sa aka farka cikin Aisha sannan aka loda ƙwayar da nauyin ta ya kai garam (g) ɗa..."
Take Aisha ta É—aga mishi hannu alamar yayi shiru, ai kuwa shirun yayi yana kallon ta har ta matso kusan su tana kallon Sa'ad a kausashe tace" Da gaske ka san da wannan abun dake cikina?"
Cike da tashin hankali Sa'ad ya raunana kallon shi gare ta ya furta" Eeshaaaa...."
Da sauri ta katse shi da" Ba Eesha ba, gaskiya nake so ka faÉ—a min?"
Kamar zai fashe da kuka kuma kamar zai daketa a hassale da Takaicin DG yace" E hakane, amma ni kasuw..."
Cikin tafasar zuci da ƙunar rai Aisha ta jefa mishi wayar da ya bata ɗazun a ƙirjin shi, hakan yasa shi saurin dafe ƙirji sai kuma wayar ta faɗi ƙasa, a kausashe sosai cike da tsana ta furta" *Na tsane ka Sa'ad*."
Juyawa tayi a fusace da niyyar zuwa kusa da mahaifiyar ta tace ta gaggauta ɗauketa daga nan, sai Hajia Kaka ta riƙe hannun ta tace" Aisha, kar kiyi haka, alkairi ya miki a rayuwa, kar ki saka mishi da sharri mana."
Girgiza kai Aisha tayi ta riƙo hannun Hajia Kaka tace "A'a Hajia, ba sharri zan saka mishi da shi ba, amma Hajia me yasa ya min haka? A duniyar nan taimako na da wahala sosai, kafin na haɗu da shi nayi barar abinci a wurin jama'a amma ba wanda ya bani ko loma ɗaya, daga ƙarshe wasu kallon banza suka dinga min har da min tayin kwana tare da su, a wani gidan kuma korar kare aka min har da sharrin sata, amma *shi*..."
Numfashi ta sauke tace" Bai yi wani tunanin komai a kaina ba ya taimake ni, hasalima a lokacin ko sunana bai tambaya ba, Hajia Kaka wannan dalilin ya sa ya cancanci girmamawa a wajena har nake kiran shi da sunan *Abbuna*, dan uba ne kawai zai iya wannan kasadar akan bin da ya haifa."