← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 168

Sashe 111

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da jin sunan aunty Ummu ta sake gasgatawa, haka suka gaisa sosai har Kuwailat ta fito, shiru sukayi saida ta raɓa ta fita daga ɗakin sannan Ummu tace" Duk da dai ina son sanin da wa nake tare? Amma ki ɗan gafarce ni, ba zan iya komai ba idan ban watsa ruwa jikina ba, amma ba zan jima ba."

Da murmushi Aisha tace" Ba damuwa aunty, ki É—auki lokacin ki."

Murmushi Ummu tayi tare da nufa madafar tana ji koma menene ya kawo matar nan gidan su to yana da alaƙa da sambatun da aunty Nur ta fara yi jiya cewa wai ita ƴar ta ce.

*Alhamdulillah.*
[18/08 à 12:27] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*52*

Ta jima zaune ita kaɗai har Kuwailat ta dawo ɗakin da abun kari ta aje mata ta ce in ji Mama, tayi ftain cikin karammata da sukayi, amma abin da ke tafe da ita da taradaddin tabbacin karɓuwar da zata samu ya sa ruwa kaɗai ta kurɓa dan ko a gidan ta bata samu ta sha ba kafin ta fito.

Ƙarar buɗo ƙofar baɗaki yasa ta ɗga kai ta kalli ƙofar, ganin Ummu ɗaure da towel wanda ya sauko mata har kan guiwa, da kuma wani ƙarami a kan ta har zuwa kafaɗun ta saita saukar da kan ta, Ummu da fara'a tace "Na barki ke kaɗai ko? Yi haƙuri."

Murmushi Aisha tai tace "Ba komai aunty."

Hakan yasa Ummu zaunawa bakn gadon ta ba Aisha baya ta fara goge ruwan jikin ta kafin ta fara shafa mai, saida ta kammata tsaf ta shafa kulaccar ta sannan ta miƙe dan saka kaya, a drower ta nemo riga da siket din da ta yi niyyar sakawa, saida ta fara saka siket ya zauna maya daidai tare da janyo jigidar ta wacce ta shige ƙasan siket ɗin hakan kuma baya mata daɗi, sannan ne ta fara kiciniyar saka riga bayan ta sassauko da towel ɗin dake kan ƙrjin ta, hakan yasa tun rigar bata gama sauko mata ba towel ɗin ya zame ya faɗi ƙasa.

Aisha da tunda ta ga Ummu ta fara saka kaya ta ɗauki wayar ta tana dannawa ba dan wani abu muhimmi take ba, sai dan kar wani abu ya ɗauki hankalin ta, zamewar towel din yasa ta ɗan saurin ɗago kan ta ta kalli ɓangaren, fahimtar abinda ke faruwa ya sa tayi saurin kawar da duban ta.

To amma wani abu da ya ɗan ɗauki hankalin ta yasa ta saurin maida kallon nata ga ƙugun Ummu, hakan ya sa gaban ta wata irin dokawa, bata san ta saki wayar ta ba ƙasa ta miƙe tare da yaye mayafin data naɗiɗiye kan ta da shi, gaba ɗaya ta aje gyalen kan gadon tare da ɗaya rigar zanen dake ɗaure jikin ta, ƙibar ta tasa saida ta ja cikin ta sannan tayi nasarar jawo jigidar dake ƙugun ta, kafin ta haɗu da iyayen ta bata saka jigida, har saida suka haɗu tayi aure ma tana da cikkn ta na fari Maman ta ta zo garin, nan take ta mata faɗa kamar ba mace ba, ba sarƙar ƙafa dan ado, duk da ma zamani ya sa yanzu ko kana son sarƙar ƙafa dole kake haƙura da ita, amma kuma hannayen ta ba awarwaro, yatsun ta ba zobe ko na wasan yara, haka dai Mama tayi ta faɗa, shine bayan haihuwar ta su aunty Mardiyya za su zo ta taho mata da jigida dozin, sai kuma wata wacce Maman ta ce ta fi bata mahimmanci saboda su ma iyayen su ne suka bata ita da aunty Mardiyya, ita aunty Mardiyya nata suna nan a ƙugun ta, ita ce dai bata da ko ɗaya duk ta ba wa ƴaƴan ta.

Ba komai ya sa Aisha jin wani abu game da haka ba sai dan Maman ta faɗa mata duwatsun ba gama gari bane, mafi yawan wanda aka yi jeren a ƙarƙashin ruwa ake samun mu, sai kuma murjani da aka ƙara ƙawata jihidar da shi, da sauri Aisha da ta jawo jigidar ta tana kallo ta kalli ƙugun Ummu da take shirin sakin rigar ta, da gudu gudu Aisha ta ƙarasa bayan Ummu da bata san me take ba.

Tana zuwa bayan Ummu kamar daga sama ta sa hannu a ƙugun ta tare da jawo jigidar ta Ummu dake irin zaren nan ne na roba dake jawuya. A tsorace Ummu ta juyo tana ƙarasa sakin rigar ta ta zuba ma Aisha wani irin kallo mai tattare da mamaki da al'ajab da jin cexa _"To, ke kuma haka kike?"_

Dan abu É—aya da ya zo mata a rai shine matan nan ne dake neman Æ´an uwan su mata, hakan yasa ta ja baya tana ci gaba da yi mata wannan bhagon kallon, Aisha ko jigidar ta dake hannun ta ta nunawa Ummu fuskar ta fal murmushi tace" Aunty Ummu, kin gani ko? Irin tawa ce, a ina kika samu wannan jigidar? Kin gani ko?"

Sai lokacin Ummu ta kalli jigidar, ita kan ta saida ta ji jikin ta ya amsa, tak tak iri ɗaya ne, amma sai ta basar ba ta ce komai ba, hakan yasa Aisha ɗan hasala ta sake matsawa kusan Ummu ta saki jigidar ta, riƙo hannayen Ummu tayi cikin kaushin murya tace "Wai me yake damun ki ne aunty *Kuwailat*? Ke fa ƴar uwata ce, wannan jigidar Mamie ce ta saka miki ita da hannayen ta, idan ke ba jinin su bace, ta ya kika samu wannan? Me yasa kika kasa fahimta ne wai? Me yasa ba zaki fahimci hawayen mahaifiya bane? Ke ma fa uwa ce, kina ganin duk inda ƴar ki zata shiga zaki kasa gane ta ne?"

A nutse Ummu ta janye hannayen ta daga na Aisha cikin nutsuwa tace" Kinga baiwar Allah, ni ban ma san wacece ke ba? Jiya wasu haka suka zo min da maganar nan, ki gane mana kema, rayuwa bayan wannan shsekarun kawai wasu su nuna min kansu wai sune iyayena, to me ya hana su nema na? Sai kawai da *RUBUTACCIYA* ta haɗa Nabila da Fahad, sai ya zama silar haɗuwata da nawa iyayen? Kina ganin an min adalci kenan? Da ba'a zo nema wa Fahad auren ƙanwata ba, da kenan ba zamu taɓa haduwa da su ba? Kinga, ni ban damu da sai nasan su wa suka haife ni ba, mahaifiyata gata can waje kin baro, ina da kyakyawan ahali anan, ina gudanar da rayuwata yadda ya kamata, dan haka ban buƙatar matsala, ina so naji da wacce ke gabana yanzun haka, dan hka ku rabu dani dan Allah, bana buƙatar arziƙin ku ko wata alfarma taku."

Raɓata Ummu tayi za ta wuce, rai ɓace saboda Aisha tana da ƙarancin haƙuri ta sake riƙo damtsen Ummu, a wani zafafe ta kalle ta tace" Ba dan nasan ke ce a gaba dani ba, wallahi da na tsinka miki marin da zai sa ki dawo hayyacin ki, me ya toshe kan ki? Kina tunanin akwai uwar da zata iya mantawa da abinda ta haifa ne? Ko da kuwa ta mummunar hanyar ta same shi? Kin san shekarun da suka kwashe suna neman mu? Kin san milyoyi nawa suka kashe kawai domin a yaɗa labaran ɓatana ni da ke? Ko kin san da iya wanda ya san wani wanda ya san inda kike kawai sun saka kyautar kuɗi har milyan biyar, ba ma ga wanda ya nuna musu mu ba? Mutumin da ya kamo hannun iyayena ya kawo su har gidan da nake a gabana suna bashi cakin (check) na milyan sha biyar, duk da haka a shirye suke da su tuɓanya ninkin ba ninki akan ki, saboda ni sun same ni kuma sun san yadda nake, amma ke basu san a ina kike ba? Wace rayuwa kike yi? Me kike yi? Ya kika zama?"
Chapter 111 · 0% Book details