Sashe 118
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata irin dariya Hajia tayi cike da jin daɗi tace" Yi haƙuri *yarima*, tafiyar ba mai jimawa bace, shiyasa ma bana shelan zan tafi."
Murmushi yayi yana kallon fuskar ta yace" To Allah ya kaiku lafiya ya kuma dawo min daku lafiya."
Tana cikin amsawa da" Ameen." Aunty Mardiyya ta shigo da abun taɓawa da ta kawo ma Jabir ɗin, kusan shi ta zauna tana faɗin" Jabir, kun ganni jiya ma shiru ko? Wallahi dawowar tasu ne aka ɗan ƙara ɗagawa, dake kasan akwai babbar ƴar gidan nan da ta ɓata tun tana jaririya?"
Da gamsuwa Jabir ya jinjina kai yana faɗin" Ƙwarai, na tuna, na ga hakan da jimawa a yanar gizo tun muna Saudia."
ÆŠorawa tayi da" Yawwa, shine fa aka gan ta jiya, to kafin ma ita yarinyar ta yarda an É—an sha wahala, dan har Nuriyya ta kwanta asibiti, to Shiyasa aka É—an samun tsaiko."
Sosai Jabir ya taya su murna da nuna musu farin cikin shi da yi musu addu'a, kafin Hajia ta ɗora da" Shine zan je dan ƙara yi musu godiya akan abinda suka mana, sannan mu basu haƙuri akan wani abu da ya faru a baya, sai kuma autana da zan nemowa auren ƴar gidan."
Nan ma addu'ar fatan dacewa ya mata da sauka lafiya kafin ta miƙe ta basu wuri shi da aunty Mardiyya, tana fita auntyn ta kalle shi a tsanake tace" Jabir, nayi mamakin yadda daga haduwar farko Hajia ta saki jiki da kai har kuka fara'a haka, kamar dama can kun san junan ku."
Murmushi yayi kan shi ƙasa yana wasa da yatsun shi, a ranshi ya furta _" Darajar Alƙur'ani kenan."_ A bayyane kuma sai yace" Gamon jini kenan."
Jinjina kai aunty Mardiyya tayi tace" Gaskiya kam, dan ban taɓa ganin haka ba."
Sai kuma ta nuna mishi kayan dake gaban shi tace" Bismillah Jabir, ci wani abu."
Jinjina kai yayi alamar to, kafin ya sake É—agowa ya kalle ta a nutse yace" Aunty, wata alfarma nake nema a gurin ku? Saboda Abba ya ce yau zamu bar garin nan, gashi har yanzu bamu zauna ba."
A tausashe tace" Hakane Jabir, kayi haƙuri, ni ma na so mu zauna da kai, amma ba damuwa faɗi ina jin ka."
A nutse ya fara fadin" Aunty, lokacin da kuka sami labarin na gudu na bar gida, tabbas guduwa nayi saboda wahalar mahaifina, a lokacin da ban gudu ba wataƙila furucin sa na sai ya ga bayana yayi tasiri a kaina, na fita daga gida a wannan lokacin da burin shiga duniya ne, amma take *RUBUTACCIYATA* ta karkata akalata zuwa ga hanyar dattijon arziƙin da yanzu ya zama uba gareni, aunty, Alhaji Kabir ya min komai a rayuwata, komai aunty ina nufin komai, abu mafi daraja da ya bani shine dalilin shi na samu ilimin addinin da na san yadda zan bautawa ubangijina, sai kuma tallafin da ya bani yanzu haka akan kasuwancina wanda shila ban san ranar daina cin moriyar shi ba, to Abbana ya je ya mishi godiya akan haka, sai dai gaskiya godiyar Abbana ta min kaɗan, Anna da mijin ku kuma ba zasu iya barin garin nan saboda wannan ba kawai, ni kuma kimar sa ta kai na iya neman arziƙi na shekara ɗari dan kawai na tura a masa godiya, a can wajen Abbana kuma Mama ma nasan ba zata iya ba, saboda tana da faɗa sosai da rashin fahimtar mutane, bayan dogon nazari da nayi sai naga aunty ke kaɗai zaki iya yi min wannan, shiyasa nake roƙon da ki samu izini, ni zan baki kuɗin da duk zaki buƙaci wani abu dan kije ki sake yi masa godiya, dan a halin da ake ciki yanzu ina tunanin sun gama magana da Abbana akan zai bani autar sa, sai dai ban san yaushe suka yanke ba."
Cike da bashi ƙwarin guiwa aunty Mardiyya tace "Gaskiya shawara ce mai kyau, duk da dai girman abubuwan nan daka lissafa ya maka ya fi ƙarfin a masa godiya, addu'a ce kawai zaka iya saka masa da ita ko nace zamu iya, dan ba kaai kaɗai ya taimka ba har da mu, amma yi masa godiyar ma daga wajen ahalin ka zai ƙara nuna masa girman alkairin da ya yi mana a rayuwa, in sha Allah Jabir zan je, sai dai kuma ni zan ma Alka magana kan zamu tafi tare da Annan taka, dan gaskiya zai so ganin jinin ka a tafiyar nan, duk dai nasan irin mutanen nan ba lallai ya ji daɗin hakan da zamuyi ba, dan nasan ko me ya maka dan Allah ya maka."
Jinjina kai Jabir yayi cike da gamsuwa yace" Shikenan aunty, tunda kin ce haka ba zan musa ba, kuma Gaskiya ne abinda kika faÉ—a, amma yanzu yaushe zaku saka ran tafiya?"
Ƴar dariya tayi tace" Jabir, ai kai zaka bamu lokacin da ya kamata mu tafi."
Murmushi yayi shima yace" A'a aunty, ku da sai kun nemi izini, sannan ku da tafiya ni da saka muku lokaci?"
Girgiza kai tayi tace" Kar ka damu Jabir, ka saka lokacin kawai."
Shima girgiza kan yayi yace" Aunty kawai ku saka rana da kan ku."
Murmushi ta sake yi sannan tace" Shikenan to, zan fara magana da Kakan naka, yadda duk mukayi zaka ji ni, yanzu fara bani lambar wayar ka."
A nutse ya shiga zayyana mata lambar tashi tana kwafewa, take ta kira shi ya ga lambar ta shima ya É—auka ya saka suna, kafin nan sukayi sallama ta mishi Allah kiyaye hanya.
********************
Ya so yayi kara game da lamarin na Kuwailat, sai dai da ya ga an kwana har an tashi kuma an doshi sallah azahar ba wani labari, sai zuciyar sa take raya masa ko dai Ummu ta riƙe ta ne tunda sun rabu kuma da alama ran ta ɓace yake game da shi? Khamis ya tura ya ɗauko ya ne, nan ne fa suka samu labarin abinda ke faruwa na bayyanar iyayen Ummu na asali, sai ga Alhaji Kabir da farin ciki kamar ma zai fi Ummu murna, duk da yasan suna hushi da shi dan zahirin su ya nuna basu ji daɗin abinda yayi ba, amma baiyi nadama ba, dan yasan gata ya ma Ummu da sai nan gaba zasu gane me yake nufi, sai dai yana takaici na rashin mata kamar ta. Bai yi ƙasa a guiwa ba bayan sallah la'asar haka ya je gida wajen Mama, da Nabila ya ci karo ta dawo daga maƙotan su, gaisawa sukayi a mutumce yana mamakin canzawar Nabila, kafin ya gaya mata Mama yake son gani? Ba jimawa ta dawo ta mishi iso har cikin gidan.
Bayan sun gaisa yake sanar da ita abinda ya kawo shi, murna ya taya su da kuma yi musu fatan alkairi, dake Mama ta fahimci abinda Malam Adam ya gaya mata sosai, ta daina hushi da Alhaji Kbir da jin bai kyauta ba, hakan ma ya sa ta saki jiki har suka jima suna hira tana bashi labarin abinda duk ya faru. Daga ƙarshe da mamaki suka rabu yana nanata kalmar _"Dama Ummu ƴar Mukhtar Ahlan ce?"_
Sai kawai ya jinjina kai yace _"Wani hani ga Allah kenan."_, A cewar Mama yanzu haka za ta je masaukin ne dan ta duba jikin Maman Ummu duk da dai ta ga da sauƙi, amma za ta je ta duba ta ta dawo, nan ya buƙaci ko zasu iya tafiya tare dan ya ga iyayen Ummu su gaisa? Ba damuwa, shine abinda ta faɗa mishi kafin ta ƙarasa kimtsawa suka kma hanyar tafiya.
*******************
Dake tafiya ce ta masu hannu da shuni, a awa da bata kai biyu ba suka iso a jirgi, tare suka zo da Alhaji Abbas sai É—aya daga cikin masu kula da sashen ta, ita din ma ta zo da ita ne saboda idanun dake É—an sako ta gaba musamman idan dare yayi. Ganin juna da aka yi shi ya sa aka sake shiga wata sabuwar murnar aka manta da an yi a waya, haka suka jima suna ta farin cikin ganin junan su har bayan la'asar.
Tuni da sun bar gidan, sai dai dake tafiya ce da ta fi mutum biyu, sai gashi an É—auki lokaci, dan Ummu ma ta ce zata bisu ne daga nan ta zauna wajen Maman ta, haka ma Kuwailat da ta ce zasu tafi tare sai ta sa ko Nabila ta rakaya gidan Baban ta, ga kuma Mama Nuriyya da taji har da Ummu sai take ganin kamar zasu rabu kenan, hakan yasa ta ce zta bisu sai su dawo tare, to fa kafin a shirya ne har Mama ta shigo gidan ta kuma faÉ—a musu ai tare da tsohon mijin Ummu suke ya zo ya gaishe su sannan ya musu barka da ganin juna.
*Tunda* Alhaji ya shigo suna gaisawa mutanen da basu san shi ba suke ta kallon junan su, jira suke suga wani matashi ko dattijon da bai kai wannan shekaru ba, amma sai suka ga shiru ba alamar wani zai biyo bayan shi, sai dai duk da haka basu sare da zasu ga wani a matsayin mijin Ummu ba sai da Kuwailat na fitowa da sauri ta nufe shi ta zauna daf da shi tana riƙo hannun shi tana faɗin "Abba, sannu da zuwa? Ina wuni?"
Murmushi ya mata ya shafa kanta ya amsa da "Autana, lafiya lau, kina nan kin manta da Abban ki?"
Dariya tayi ta É—ora kanta a damtsen shi tace "A'a Abba, ban manta ka ba, ai yanzu gida zmu tafi."
Murmushi kawai ya mata ya kalli Abbu Mukhtar da aka shaida mishi shine surukin nasa yana murmushi yace "Kuna ta shan ƙiriniyar auta ba, ina ce dai kuna zane ta? Dan sai ta saka muku ciwon kai."