← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 168

Sashe 141

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*65*

Abba da ya ga kiran Jabir ya É—auka rigima ce zai masa, amma sai ya ji yace "Abba, Abba dan Allah ku dawo, wallahi Aliyu ba lafiya, yaushe zaku dawo?"

Da yanayin tashin hankali Abba yace "Subhanallah! Aliyun? Me ya same shi Jabir? Jiya munyi waya É—azu ma da safe haka, yana ina?"

Girgiza kai Jabir yayi kamar yana gaban Abba yace "Abba Aliyu wasu maganganu yake ta yi alamar dai baya hayyacin shi, dan Allah ku zo sai mu kaishi wajen malamai."

Cikin son ya nutsar da shi yace "Kaga Jabir, nutsu, sannan ka faÉ—a min me ya faru da Aliyu? HaÉ—ari ya yi?"

Ajiyar zuciya Jabir ya sauke yana istigfari na abinda bakin shi zai maimaita kafin a sanyaye sosai yace "Abba, wai Aliyu ne ke faÉ—in wani abu dai haka ni da Maala, to ai kaga bai da lafiya ko? Dan Allah ku dawo."

Yanzu ne kaÉ—ai Abba ya fahimci Jabir, dan haka ya numfasa a nutse sosai yace "Jabir, kenan nima idan na maimaita mka abinda Aliyu ya faÉ—a maka, haka zaka É—auke ni mai aljanu?"

Wata dariya ce ta kubce mishi irin ta haba ɗin nan tare da tausasa murya a ldabce yace "Abba, kayi haƙuri, na san nayi laifi saboda jiya ban kira ba naji ya kuka sauka, sannan ban kira da safe na gaishe ku ba, kuyi haƙuri dan Allah, amma kada ku hukuntani ta hanyar irin wannan wasar mai hatsari."

Ba alamar wasa Abba yace "Jabir, da gaske nake maka maganar nan Jabir, na zo nan ne na nema maka auren Ummu, kuma tun daga mahaifin ka, Anna, Alhaji (Alka) da ita kanta iyayen ya duka sun amince, yanzu kaine kawai ka rage."

Tsaye ya miƙe saboda jin yau dai kamar duk mutanen basu da lafiya, ciwon kan shi ne ya ji ya sake ruɓanya dan har jijiyar kan shi ya ji tana amsawa da ƙarfi, cikin yanayin tashin hankali da ruɗu Jabir yace" Abba..., Abba da gaske kuke maganar nan? Abba Maama fa? Wai me yake damunku ne yau ɗin nan? Abba ta ya kuma ni zan iya... A'a Abba, gaskiya ba zan iya ba, ba zan iya wannan abun ba idan ma da gaske kuke faɗa kenan."

Jin yadda Jabir ya rikice yana magana yasa Abba faÉ—in" Shiiiii! Jabir nutsu ka saurare ni? Maga..."

Da sauri Jabir ya girgiza kai yace" A'a Abba, Abba dan Allah ku daina wannan maganar, Abba sai anjima, kaga dama tun jiya bana da lafiya, zan sha magani na kwanta Abba."

A É—an kausashe Abba yace" Jabir, da kai nake magana fa, ka saurare ni mana."

Ajiyar zuciya Jabir ya sauke mai nauyi tare da tsayawa cak daga kai da kawon da yake yi, a hankali kuma ya sulale ya zauna kan kujera yana dafe goshin shi cikin wata tikitacciyar murya kamar zai fashe da kuka a sanyaye yace" Kayi haƙuri Abba, dan Allah ka ce min wasa kake min?"

Shima Abba a nutse yace" Jabir ba da wasa nake maka ba, wannan shine abinda muka tattauna, Jabir, na san kaan ba haramun bane hakan ko? Sannan kasan ba zan sa ka abinda zai cutar da kai ba, rayuwar Ummu na ga tana cikin haÉ—ari na rashin samun wanda ya dace, shiyasa nayi bugun gaba a kan ka Jabir, yanzu in tambaye ka?"

Shiru Jabir yayi sai murza goshin shi da yake yi yana jin kawai mafarki yake yi kuma burin shi shine ya farka, Abba da ya ji bai ce komai ba sai yace" Jabir, ka yarda ni uba ne a gare ka?"

Shiru Jabir ya sake yi yana tunanin da irin hakane ake so a cuce shi kenan? A kanainaye shi yadda zai kasa motsawa, Maama fa suke magana? Wai me suka sha ne yau? Maama? Maaman Kuwailat da yake da burin a bashi ya raine ta? Maama dai wacce ko idanu baya haɗawa da ita? Maama dai matar da Abban shi ya saki, wandaa ya masa komai a rayuwar nan, tunda daga ilimin da ya samu har zuwa kan duniya da ubangiji ya fuwace masa yake samu, shine ake so wai ya auri... Aure fa? Ya auri Maama dai? Subhanallah! Wannan saɓo da mutanen nan ke yi yau Allah ne kaɗai zai iya gafarta musu gaskiya.

Saida ya sauke numfashi mai nauyi sannan a ƙasan maƙoshi ya furta "E Abba, ban da wani uba a duniyar nan sama da kai."

Kamar suna gaban juna saida yai murmushi sannan yace "Kuma zan iya umartar ka kayi indai ba saɓa shari'a ba?"

Saida Jabir ya runtse idanu wasu zafafen hawaue suka taho mishi, shiru yayi saida Abba ya sake faÉ—in "Da kai nake Jabir?"

Da sauri Jabir ya amsa da "Zan yi komai da ka umarce ni Abba, amma dan Allah..."

Sai kuma yayi shiru na wasu daƙiƙu, kafin ya sassauta murya kamar mai raɗa yace "Dan girman Allah Abba *ka da ka umarce ni da kwantawa shinfiɗar da ka tashi*, ba zan iya aikata haka ba Abba ko da zaka yankani ne, gwara na bar duniyar nan kana mai alfaharin kasancewata ɗanka, ba wai na tafi kana kallona a matsayin wanda yasan wani ƙololuwar sirrin da ya taɓa zama sirrin ka ba."

Yana gama faɗin haka bai jira jin me Abba zai ce ba kawai ya kashe kiran tare da wurga wayar kan kujerar dake gefen shi ya sake dafe kan shi, ya jima haka yana tunani da jin kamar ya kasa yarda da lamarin, ba'a fi minti talatin ba kiran Abban shi ya shigo waya, a wannan lokacin ya san Abban shi na aiki ne, amma abun mamaki yana ganin kiran saida ya ji gaban shi ya faɗi haka kawai, sai ya shiga tsoron ɗaga kiran wanda hakan yasa bai ɗaga ba saida kiran ya yanke, gaba ɗaya sai suk saka mishi jin tsoro da kuma wani irin ƙyama da jin haushin komai. Dama ya jima da burin son tafiya Kano dan ya ɗauki karatu gaban malamai nan guda biyu, dan haka kawai ya miƙe ya fara shirya kayan shi, saida ya gaa tsaf ya fito ya samu kira a wayar shi sosai har da Abban shi da Abba ma duk ya sake kira.

Girgiza kan shi yayi yana ayyna _"Ban taɓa tunanin zaku iya kawo min haka a ran ku ba, to me kuka ɗauke ni? Ko mayen mata ne ni ina ni ina Maama saboda Allah? Shikean baku san me zakuyi tunani a kai ba, sai ku tunano abubuwan ku sai kuma ku ce dole sai an yarda saboda ba haramun bane?"_ Haka ya gama komai tare da rufe abindake buƙatar rufewa da kashe na kashewa sannan ya fice da makullin motar shi yana kiran lambar *Hassan*, yana ɗagawa yake sanar da shi gashi nan fa zai kamo hanyar Kano, da farin ciki Hasan yake faɗa masa sai ya zo yana jira, yana samun wannan tabbacin ya kashe wayar shi gaba ɗaya ya kama hanya da rana tsaka tamkar wanda aka kora daga gari.

*******************

A kasalance ta farka tana buɗa idanun ta da jin jikin ta ya mata wani irin nauyi, a hankali ta kai hannu kan marar ta ta shafa sannan ta sake yaye zanin rufar ta zuro ƙafafun ta tasauko, da ɗan sauri ta nufi ban ɗaki dan yin fitsarin da take tunanin yaa fara taho mata tun a gado.

Tabbas tayi fitsari, sai dai har da abun da bata yi tsammanin shi bane yanzu da safe, sai kawai ta gyata jikin ta ta ɗauki pad da sabon pant ta saka sannan ta tara wa kan ta ruwan wanka ta fito dan cire rigar baccin ta. Gaban madubi ta tsaya ta cire figar baccin, hakan yasa bras ɗin da take sakawa kwana uku yau saboda gyran nonon da Mamie ta ce wallahi sai tayi baƙa wacce ta kama ta sosai, a nutse ta ɓalle ta sannan ta cire ta aje gefe, sai ta samu kan ta da jin kunyar kallon nonuwan nata saboda ita kanta wani abu taga sun ƙara yi da ta kasa ganewa, sai take ganin su kamar ba a jikn ta ba wallahi tsbar yadda suka ƙara yin wani digir digir da su a ƙirjin nata da kuma yadda suka wani busu sai ƙyalli suke, wataƙila na man hulbar da ta shafa ne? Ko kuma dai saboda cikar nan da sukayi ne? Yatsa tasa ta ɗan latsawa ta ga da gaske dai nata ne, sai kawai ta saki murmushi tana hango... Yadda Jibril zai yi da kayan nan, jin kamar ruwan da ta tara sun cika ya sa ta nufi ban ɗaki da sauri.

Wanka tayi sosai ta fito ta shirya cikin kayan da ta fi anfani da su wato doguwar riga, bayan mai da turare ba ta shafa komai ba ta fito da wayar ta a hannu tana kallon lambar Jibril da take son ta kira amma Mama ta ce mata kar ta kuskura shima sun gaya maa daga yanzu har a ɗaura auren kar ya kira ta, ita kuma bata san Mamie ta saka mata lambar Jibril a baƙin jadawalin da ko ya kira kashe za'a ce maa wayar ta bare ma ɗana kiran nan ya shigo ta ankare, falo ta samu su Mama da Mamie da Nabila suna karin kumallo, gaisawa sukayi kafin Mamie ta kalle ta tace "Aunty wannan baccin na jaraba kuma fa da kika samu yanzu da safe?"

A kasalance Ummu ta girgiza kai tace "Ba komai aunty."

Sai kuma ta kalli Mama tace "Mama, ina son yin magana da Jibril, dan Allah ki ce anty ta barni na kira sau É—aya."
Chapter 141 · 0% Book details