Sashe 37
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A sukwane ya nufe ta cike da faɗa da bala'i yna faɗin "Ke dallah riƙe gaisuwar ki, idan ban kwana ba zaki ganni ne?"
Yana isa gare ta sai kuma ya rasa ainahin me zai ce mata, faɗa akan ta fito babu hijabi? Kar fa ta fara zargin shi akan wani abu, sai ta ga zaƙewar shi tayi yawa ai. Kasa kallon fuskar ta yayi yana ta sissine kai da yace" Maza shiga ciki..."
Da rashin fahimtar shi gaba ɗaya ta raɓa jiki a sanyaye tana taɓe baki, har ta ɗan yi nisa yana tsaye bayanta ƙerere sai kuma yace" Ji nan...?"
A hankali ta juyo ta sauke dubanta gare shi ta amsa da" Na'am." Saida ya haÉ—e fuska irin kar ta ga damar san nan yana kakkawar da kai yace" Ki daina fitowa haka ba sutura, maza na shigowa kowane lokaci."
Da maÉ—aukakin mamaki ta kalle shi za ta tambaye shi ya sutura? Bayan wannan ta jikin ta? Amma sai ta ga ya juya ya bar ta nan tsaye, sai kawai ta juya tana sake duban shigar ta, to ita yanzu me ye aibun rigar tan nan? Girgiza kai kawai tayi ta furta" Allah ya shirya ka Abbu, ashe shiyasa kullum addu'ar Hajia kenan akan ka."
Tunda yake tunkaro DG ya fahimci kallon ƙurilla da yake mata da kuma mamaki a fuskar shi hakazalika tambayoyi fal bakin shi, yasan ba zasu ƙarke a daɗi ba, dan haka ya ci magani sosai ya ƙaraso a tsume dan in cin uwa ma ta kama sai a yi ya tsaya gaban shi, cikin dakakkiyar murya ya dafe ƙugu ya kalle shi yace "Mun gam magana, za ka iya tafiya?"
Kallon idanun Sa'ad É—in yayi da matsanancin mamaki yace "Oga, wa...ccen yarin...yar...kamar...wacce muk..."
Gaba da gaba dan ya nuna musu ya tafasa fa baya tsoron ƙuna yasa kai tsaye ya katse shi da cewa "Ita ce DG."
Da mamaki DG ya sake kallon hanyar da Aisha ta bi yace "Amma me take nan? Dama kuma tana hannun ka shine ka ƙyalemu muke ta haukan karaɗe gari a kan ta? Me yasa *Sa'ad*?"
Saida ya sauke numfashi yana kallon fuskar DG É—in sannan yace "Tana da mahimmanci a rayuwata, bana so na rasata kuma ba zan iya rabuwa da ita ba, dan haka kawai ku bar maganar neman ta."
Da yanayin fara hasalla ganin milyoyin kuɗaɗe ya karɓa akan yarinyar nan DG yace "Ba zamu iya haƙura ba, kai ne zaka haƙura ka bamu ita, ni ba cutar da ita zanyi ba, kawai ka bani ita Sa'ad, saboda na karɓi kuɗi masu yawa akan ta, kuma nayi alƙawarin zan samo ta."
Wani malalacin murmushi Sa'ad yayi ya ɗan ja baya yana ƙare mishi kallo yace" Wato in baka ita ko? Tunda kaine Ibu? In ɗaukota in baka ka tafi da ita ni ga sakarai wawa marar anfani ko? To bari ka ji..."
Matsowa ya sake yi daf da shi ya ɗora yatsarshi a ƙirjin DG yana daddagashi da ƙarfi yana faɗin" Zai fi kyau ku rabu da ita, idan ba haka ba kuma zamu samu babbar matsala da ku, kun san ni haka nima na san ku."
Cikin haɗe fuska DG yace" Ai kuwa zaka yi nadama, dan a shirye muke mu karɓi yarinyar nan ta kowace irin siga."
Murmushin gefen laɓɓa Sa'ad yayi yace" Ka san wani abu? Siyar da ƙwaya kawai nake kafin yanzu, ko sigari bata taɓa ban sha'awa ba wallahi, dan nasan kaɗan a aikin ƙwaya ne yasa ka aikata fiye da abinda kake faɗa za'a aikata yanzun."
Cike da jin haushin wannan abu da Sa'ad ya faɗa dan ƙarara nufi yake ƙwaya ce ta sa yayi wannan ambatun tsabar bai ɗauki abinda ya faɗa da mahimmanci ba, jinjina kai yayi yana ja baya yace" Shikenan, zan tabbatar maka da aikin ƴan ƙwaya, kuma zaka yi nadama akan haka, mu zuba ni da kai."
Murmushi ya mishi cike da wofantar zancen yace" Sauka lafiya."
Da irin jinjina kan nan na zaka gane kuren ka ya juya ya fita cike da alwashi kala-kala akan Sa'ad ɗin, kuma yay alƙawari yau ko gobe yarinyar nan za ta shigo hannun shi, dan haka akwai buƙatar yayi aiki cikin gaggawa da zai raba yarinyar da gidan su Sa'ad ɗin dan ya damƙa ta hannun Hajia Fa'iza, ruwan ta ne ta dafa ta ta cinye ko ta gasa, shi bai dame shi ba tunda ya samu kuɗin shi.
*Ga mai son shiga grp ɗin RUBUTACCIYA ya tuntuɓi wannan lambar 82-21-91-74*
*Idan aka zuba comment zaku iya samun wata page in sha Allah.*
*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
*RUBUTACCIYA*
👩â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨ðŸ‘©â€â¤ï¸â€ðŸ‘¨
_NA_
*SAMIRA HAROUNA*
_SADAUKARWA GA_
*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_
_Bismillahir- rahamanir-rahim._
*17*
Kiran DG ne ya tashe shi da safiyar nan, cikin jin haushi ya É—aga kiran bai ce komai ba yana saurare, a tausashe DG yace "Oga, ina nan cikin gida, na zo muyi magana ne."
Akwai magana sosai a bakin shi, amma takaici yasa kawai ya yanke kiran ya taso ya fito a harzuƙe dan ya ji me ye na zuwa musu gida a wannan lokacin? Shi dai ya ɗauka ba komai tsakanin shi da su daya rage, kasuwanci ne kuma ya daina shi yanzu wasu sabgogin yake yi da suke bashi halaliyar shi, kuma yanzu hankalin shi ya fi kwantawa da haka, zai ma iya rantsuwa ya fi wata uku bai ga ƙwaya da idanun shi ba idan ba wacce aka ciro a cikin Aisha ba, tana nan ana ajiye a cikin motar shi a ƙasan kujera yana so ya samu inda zai binne ta, daga nan ba shi ba sake taɓa ƙwaya har abada.
Yana zuwa ya same shi tsaye yana wasa da bishiyar mangwaron da tayi shar shar tana daf da fara fidda ƴaƴa, DG na hango shi ya yi wani shu'umin murmushi, dan yadda ya haɗe fuska ya san ran shi ɓace ya fito nan, hakan yasa ma ya fito daga shi sai singlet baƙa da wando tree quater, yana ƙarasowa ya tsaya yana dafe ƙugu yace "Ina ji?"
Gyara tsayawa DG yayi yace "Barka da safiya Oga, dama akan maganar ɓatan yarinyar nan ne, yall..."
A tsanake cikin tausasawa da kasala Sa'ad yace "Kaga, ba abinda ya dame ni da yarinyar nan, ku je ku nemeta idan kun ganta ku riƙe na bar muku, ni yanzu wannan sabgar bata gabana, amma ka san wani abu guda..."
Ya faɗa cike da gargaɗi da nuno shi da yatsa yace "Ku cire idonku a kan yarinyar nan, ta fi ƙarfin ku kuma tana da masu tsaya mata idan wani abu ya same ta, dan haka ina baku shawara ku rabu da ita...."
Kafin ya dasa aya inda yake fuskanta ya hangi Aish ta fito daga ɓangaren su Maman shi riƙe da bokiti, yadda alamu suka nuna mishi ba komai a bokitin bai ɗaga hankalin shi ba kamar ganinta da hula a kanta wacce duk rabin gashin ta a fili yake, sanye kuma da doguwar rigar kanti dake fito da surar jiki duk da bata matse ta ba, La'ilaha illallah ! Me yake damun Aisha ne? Dubi fa rigar nan rawa take a jikin ta, ga shi ta fito mata da ɗan ƙirjin nan nata da wannan shafaffen cikin...
Ganin idan ta ci gaba da tafiya za ta kai ga kusurwar da idanun DG na iya sauke dubansu ga ƙugun ta, dan haka yayi azamar daka mata tsawa da ƙarfi yace "Ke!"
A zabure Aisha ta tsaya tare da waigawa inda sautin ya fito, ganin shi tsaye tare da wani kuma a yanayin da bata taɓa ganin shi ba sai ta ji kunya ta rufe ta, sadda kanta tayi a tausashe tace "Ina kwana?"
A sukwane ya tunkare cike da bala'i yana faɗin "Ke dallah riƙe ina kwanan ki, da ban kwana ba zaki ganni ne yanzu?"
Da mamakin faɗan kuma na miye? Me tayi yanzu kuma daga haduwar su har ya ƙaraso kusan ta ya ɗan kakkareta yana kallon fuskar ta dan baya son kallon komai bayan nan ɗin yace "Ya zaki dinga fitowa babu sutura a jikin ki? Bayan kin san ba ke kaɗai bace a gidan."
Ƙarin mamaki akan wanda ya bata, ƙanƙance shanyayyun idanun ta tayi ta shiga kallon kan ta, sutura? To bayan wannan? Tsirara ta fito ne? Da mamaki ta kalle shi tace "Amma...."
Saida yayi maganar ne ya kuma gane kamar fa yayi tsauri dayawa, me yasa ya aikata haka? Idan fa tayi tunanin wani abu a kan shi? Cike da basarwa irin ba shi É—in nan bane ya kawar da kai a tausashe yace "Ki kula, ki daina fitowa haka, Kinga maza na shigowa da ba muharramanki ba."
Ita dai bata daina kallon shi da mamakin nan ba har ta jinjina masa kai tace "To, zan kiyaye."
Da ido ya mata alamar ta wuce to, ɗan taɓe baki tayi ta juya a sanyaye ta wuce ciki tana addu'ar "Allah ya shirya ka Abbu." Dan sai yanzu ta fahimci Dalilin da ya sa kullum addu'ar Hajia kenan a kan shi.
Tunda ya juyo y ga fuskar DG cike da mamaki yana bin Aisha da kallon ƙwaƙwafi ya san sauran zancen, kuma ya san ba zasu kwashe lafiya ba, dan haka ma ya cika fuskar shi tam da haɗewa ta yadda idan ma cin uwa ta kama ai zai iya akan ƴar shi ko? Yana zuwa gabanshi ya dafe ƙugu yana kallon shi yace "Ina ji?"
Ba tare da ya daina kallon hanyar da ta bi ba yace "Oga, yarinyar can..."
Katseshi yayi da cewa "Ita ce, sai me?"
Da mamaki DG ya kalli Sa'ad É—in yace "Sai me? Oga sai me kake tambaya?"
Sai kuma ya É—aga murya yana faÉ—in "Oga yarinyar nan fa ita ce muke ta haukan nema a garin nan kamar za mu tashi duniya, tana hannun ka dama ka mana shiru? Me yasa? Me yasa zaka mana haka? Tu yaushe take tare da kai? Me kuma kake mata?"