← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 168

Sashe 104

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yadda muryar shi ta daki kunnuwan ta yasa ta faɗuwa dandaɓar ƙasa tana ja baya, haɗe kukan ta tayi tana girgiza masa kai tace" Wallahi ba abinda ya faru tsakanin mu? Ta ya ma zaka min wannan zaton? Ba ab..."

Cikin daka mata tsawa idanun shi har ja suke yi yace" Ya zaki ce ba abinda ya faru? Bayan ke kika faÉ—i wai tsakanin ki da Jabir, ina so nasan me ya faru?"

Da hannu ta masa alamar yayi haƙuri tare da faɗin" To naji, zan faɗa maka, amma dan Allah kar ka dake ni, zan faɗa wallahi."

Tsaye yai ƙiƙam gaban ta ya dafe ƙugu alamar yana sauraren ta, cikin shasheƙar kuka ta fara faɗin" Ranar ne fa da aka ɗauke wuta na yanke hannuna a madafa, shine Jabir ya shigo sai yayi ƙoƙarin taimaka min, hannuna kawai ya riƙe yana ɗaure min ciwon da jini ke zuba, wallahi bayan haka ba abinda ya faru, shi ko kallona ma bai yi ba."

Ƙura mata idanu yayi yana kallo, sai kuma ya girgiza kai ya raɓa ta zai wuce, hakan ya sa ta juya ta bishi da kallo tana cewa" Zan je gida, za'a zo neman auren Nabi..."

Tun bata gama faÉ—a ba ya furta" Ki je kawai, ki je duk inda kike so ban hana ki ba."

Ficewa yayi Ummu kuma ta yi saƙe tana kallon ƙofar, miƙewa tayi tana share fuskar ta ta fice a ɗakin ita ma zuwa nata ɗakin. Tana shiga ta samu kira ya tsinke, lambar aunty Nuriyya ce, dan haka saida tayi zaune sannan ta sake maida kira, jim kaɗan ko aka ɗaga suka gaisa inda kowa ke kiran kowa da aunty.

Mama Nuriyya ce ta É—ora da "Muna fa garin ku?"

Da mamaki Ummu da ita matsalolin ta ma ya sa ta manta da akwai alaƙa tsakanin Fahad da su tace "Haba dai aunty, yaushe kuka zo? Shine ba sanarwa?"

Da fara'a Mama Nuriyya tace "Ba haka bane, ƙanin mijina muka zo nemawa aure, to kin san tafiya irin wannan, shiyasa ban gaya miki ba sai da muka sauka lafiya."

Sai lokacin Ummu ta tuna da wani abu, dan haka ta gyara zama tace "Aunty, ni kam na ce na ga a lambar ki kina anfani da sunan Ahlan, ko dai kun san Fahad ne?"

Tayi tambayar ne dan ta samu tabbaci, sai kuma Mama Nuriyya tace "Fahad ai shine muka zo nemawa auren, ƙanin mijina ne uwa ɗaya uba ɗaya, kin san shi ne dama?"

Murmushi Ummu tayi tace "Hakan na nufin ni da ke aunty zamu zama sarakan juna, saboda Nabila nima ƙanwata ce."

Da farin ciki Mama Nuriyya tace "Haba dan Allah? Ƙanwar ki dai? Ka ga wani ikon Allah ko? Kenan duk bidirin nan da aka sha tsakanin Nabila da Fahad Ƙanwar ki ce dama?"

A tausashe Ummu tace "Um, ƙanwata ce, sai dai...e ƙanwata ce."

Da ta so faɗa mata ita fa bata ma san iyayen ta ba, sai kuma ta ga kawai bai dace ta faɗa mata ba, haka suka dinga tattaunawa har Ummu ta faɗa mata tana shirin tafiya ma gida dan tarban su, anan Mama Nuriyya ke cewa" Fahad ma ai ya faɗa mana ta ƙi amincewa da shi, shiyasa Hajia ta ce mu zo mu same ta da iyayen ta mu bata haƙuri kan abinda ya faru, idan ta amince kum a saka musu rana kawai."

Murmushi Ummu tayi, ba zata bata tabbacin Nabila za ta amince ba, dan ta ji zafin abinda suka mata gaskiya, hakan zai sa ba zata takura Nabila ba, idan tana son Fahad ta amince, idan kuma ta daina son shi faƙat.

Da fara'a tace" In sha Allah ma alkairi ne zai faru, amma dai aunty ba yau zaku koma ba ko?"

Amsawa Mama Nuriyya tayi da" Gaskiya a'a, dan ni na jima rabona da nan, tun haihuwar Ikram ta Eesha, yanzu kuma ƙanin Ikram ma shekarar sa uku, to ina so zan yi sati ɗaya, idan mun samu amincewar Nabila fa kenan, dan in bata amince ba wallahi uban Eesha ba zai barni ba."

Dariya Ummu tayi da farin ciki tace" To Allah ya yarda, ni kaina zan zo ku mana sati, kunga ai sai na zagaya da ku kuka gari." Haka dai suka dinga hirar su kafin daga bisani su yi sallama da sai sun haÉ—u gida.

*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:15 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*49*

Tunda ta je gidan Mam ta san akwai matsala, Ummu bata taɓa zuwa gidan nan idanun ta fari ƙal ba, amma yau bbu kwali, babu jan baki ko ya ya, ga idanun nata sun yi fari fat alamar anjima ba'a shafa kwallin ba, amma dake ta sake tana walwala haka ma Kuwailat da suka zo tare, sai ta share da niyyar za ta tambaye ta daga baya, dan damuwar Ummu tashin hankalin ta ce.

*Bayan* sallah la'asar baƙin nasu suka iso, ba wanda aka gayyata saboda har lokacin Nabila faɗi take ita fa ta haƙura da auren Fahad, amma tunda ya dage sai ya turo ba damuwa su zo, amma za ta rama abinda aka mata ita ma cikin ruwan sanyi, maƙwabcin su malam Adam ne kawai sai Yaya Luƙman suka tarbe su tun daga ƙofar gida, cikin nutsuwa suka dinga yi musu iso har suka shigo ciki.

Alhamdulillah dake lokacin ba waccen gidan nasu bane, kuma duka su huɗu ne suka zo, sai kawai suka wuce har falo suka zauna kn kujeru suna ta gaisawa. Ummu na ɗakin Nabila ta idar da sallah, da sauri ta miƙe za ta fita Nabila tace "Auntyna, dan girman Allah kar ki bari Yaya Luƙman ya bayar dani haka kawai, ku ce musu ban tashi aure ba karatu nake."

Dariya Kuwailat tayi tana kallon Nabila, hakan yasa Nabila kallon ta tace "Ƴata ko kin gaji dani? Wulaƙantani fa sukayi ?"

Girgiza kai kawai Kuwailat tayi alamar a'a, hakan yasa Ummu saurin kallon ta tace" Ke kuma zaman me kike yi nan? Ki tashi ko ruwa mana ki kai wa baƙi."

Da sauri Kuwailat ta miƙe tana ɗaukar hijabin ta zata saka Nabila tace" Kuwailat da hijabj akwai amana, aunty to ki barta ta taya ni zaman ɗaki mana?"

Girgiza kai Ummu tayi tace" A'a muje ta ba baƙi ruwa."

Kuwailat ce ta fara fitowa falon, kuma daga inda ta fito mutanen dake zaune duk suna fuskantar ta ne, hakan yasa kowa idanun shi ya sauka kan ta... *Daga* wajen Mama Nuriyya da Abbu Mukhtar harbawan jijiyar dake isar da gudanar jini ne ya wakana lokaci ɗaya, inda zuciya ma ta harba da gudun ƙarfin da ya sa tunanin su ya basu kamar da alaƙa? Saboda tsabar kamar Kuwailat da suka gani a fuskar Kuwailat da ta wacce ta zama rayuwa gare su. *Kafin* su farga da kama ce kawai irin ta katari? Ko kuma dai kama ce dake samo asali daga dangantakar jini? Sai ga Ummu wacce ita girma da shekaru ya sa kamannin nata suka fi rikiɗewa zuwa ga na... *Hajiar su*.

Ba Mama Nuriyya da Abbu ba, har da Yaya Bilal da Fa'iza duk suka zaro idanun ganin wannan kamanni na Hajia a fuskar Ummu da tsufa ne kawai ya bambamta su, amma daga farar fatar, idanun, hancin, bakin dake musu murmushi sak irin na Hajiar su, zuwa ga tsayin ƙirar ta da ƴar mulmujewar, ƙwarai, wannan Hajia ce, musamman ma Bilal da Abbu Mukhtar da suka fi sanin Hajiar tun lokacin ƙuruciya, sai suke ganin da ace mahaifiyar su ta ɓata kuma a basu kwangilar samo ta, to haƙiƙa ba mai raba su da wannan, wallahi kawai Hajiar su ce.

Bayan wannan kamannin, akwai sauyawar yanayin su dake tabbatar da haɗuwar jini irin na iyaye da abun da suka haifa, hakan ne ma yasa Abbu da Mama Nuriyya kasa kawar da duban su ko da na sakan ɗaya daga fuskar ta, musamman mama Nuriyya da hawayen da suke saukowa kan fuskar ta suka sake nuna mata lallai da wani abu a ƙasa, dan hawaye ne irin masu sanyin nan ƙarau wanda ta kas dakatar da su.

Aunty Fa'iza kaɗai tayi jarumtar yin murmushi ta kalli Yaya Bilal dake son ɗauke kallon shi daga matar mutane amma ya kasa kuma bai san dalili ba tace "Yayana, ka ga wani ikon Allah? Fuskar ƙuruciyar Hajia a jikin matar nan."

Da sauri ya kalle ta da yanayin dake nuni da ya tafi wtat duniyar, amma samun wacce take ganin abinda yake gani yasa ya kalle ta cikin raÉ—a sosai yace "Ashe kin gani kema? Wannan wace irin kama ce? Kamar Æ´an biyun Mamie."
Chapter 104 · 0% Book details