← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 136 OF 168

Sashe 136

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi ita ma tace" To Abbu."

Tashi yayi ya fita ita ma ta miƙe ta shiga bn ɗaki dan yin wanka. Ba ta wani jima ba ta fito, tana cikin shafa mai Adama da ita kaɗai ce mai aikin da Ummu ta yard take shigo mat ɗaki saboda ta fi samun nutsuwa da ita ta shigo ta tambaye ta a kawo mata abinci nan ne? Amsar ita ce "A'a Adama, gani nan fitowa ma, zan ci a can."

Da fara'a ta ams mata ta juya ta fita, ba jimawa kam ta gam shiryaw ta fito, a veranda t samu Mamie da Nabila sun hira inda Mamie ke yankan É—anyar miyar faku, sai Nabila dake gyaran akaihu tana faÉ—in "Wallahi Mamie da ba'a samo mana É—anyar miyar nan ba ko? Ina g fa da na fita da kaina nemn ta."

Dariya Mamie tayi ba tare da ta kalli Nabila ba tace "Dole ma ai mu samo ko dan sabon yariman mu."

Ƙarasowa Ummu tayi dake sauraren su tace "Auntyna, ba dama mutum ya ce yana son abu ko baya so sai an fassara shi."

Duk kallon ta sukayi duk da kuwa Adama ta sanar da su tn zuwa, Nabila ce ta fara faÉ—in "Shine fa aunty Ummu, har bana so na ce ina sh'a'war wani abun."

Kallon ta Mamie tayi tace "Saboda ba ky ao a ce kina da wani abun ko?"

Duk murmushi sukayi sai Ummu da ta ja kujera ta zauna, hira suka fara yi har Ummu na cewa Mamie "Aunty, ina so zan je gidan su Ammie (gidan iyayen su Mama Nur), da kuma aunty Murjanatu da ita ma tana ta ƙorafin na ƙ zuwa na mata kwana biyu."

Saboda bata son ganin ta a damuwa tace "Ba matsala ai aunty, yaushe zaki tafi? Dan ki sanar da Abbun ki da wuri."

Saida ta É—an yi tunani na sakanni kafin tace "In sha Allah ko gobe ma."

Jinjina kai tayi tace "Ya yi, Allah ya kaimu."

Da "Ameen." Suka amsa ita da Nabila kafin suka ci gba da hira, nan Ummu sukayi waya da Mama har take sanar da abinda ya faru tsakanin ta da Larwan, sosai Mama ta ji ba daɗi dan gaskiya ta sa rai da auren Ummu da Larwan ƙwarai, haka ta danne nata rashin jin daɗin tana nuna mata tayi haƙuri komai zai wuce in sha Allah.

*A* daren Yaya Bilal ya karɓi baƙuncin iyayen Jibril, dan lokacin Abbu ma muhimmin taro yake da shi da yasa bai dawo ba, amma da Yaya Bilal ya faɗa masa abinda ake ciki sai ya ce ya ji da su kawai, Ummu ƴar sa ce, idan ya basu ita ta badu fa, duk da ya ji daɗin jin haka, sai dai wani abu ɗaya da ya ji bai msa ba shine, yadda yake ji a gari ana faɗin ƴan mata ma ya aka ƙarata wajen samun masu so da aure bare wacce ta taɓa auren? To amma ga Ummu har yanzu ko wata ɗaya ba ta yi da gama idda ba sai mza ke fito mata, e ya san tana da ilimin addini, ilimin boko daidai gwargwado, sannan tana da hasken fata da kuma kyau daidai misali. Amma fa kuma Ummu tana da kuɗi, ƙwarai tana da kuɗi, mijin ta ya bata milyan biyar ihsani ga kuma mota dake can garin da ta baro, anan kuma mahaifin ta akwai kasuwancin da ita yake juya ma wanda Alhaji margayi ya bata matsayin kyauta na haifa masa jijar farko daga ɗan sa namiji, sannan Mukhtar yana da kaso mafi tsoka a cikin dayawa daga cikin harkokin da sukayi fice aka san su da su, hakan na nufin *Ummu Kulsum*, *Aisha* da kuma *Kabil* sune kawai magadan shi, Ummu kuma matsayin ta na babba zata iy jan ragamar wasu harkokin ko a yanzu.

To wannan tunanin ya sa yaji abun bai ɗan kwanta masa a rai ba, sai kawai ya ce da su faɗawa ɗan qu ya nemi amincewar Ummu tunda yanzu ita ke da ikon zaɓawa kan ta abokin rayuwar ta ba su ba, ko ba komai dai su haka ya musu dan dace ce aka basu ai da ɗan su zai gwada sa'ar sa, idan yayi sa'a sai kaga ya zama magajin wannan katafaren gida da aka gina tamkar an maya za'a mutu a bar shi.

Daga Abbu har kawu Bilal ba wanda ya faÉ—a mata abinda ya faru, da safe ta shirya tsaf ta fita fara ziyarar ta da tayi niyyar yi wunin yau, a gurin ziyarar nata ne Jibril ya addabi rayuwar ta har ma yake faÉ—a mata ai iyayen ta ne suka bashi damar neman amincewar ta. Abun ya fice mata a rai, tunanin za ta sake komawa wani bala'in ko kula rabuwa ya sa ta nemi yakice Jibril daga jikin ta, ta nuna masa ita tana gaba da shi amma ya ce wannan ba hujja bace, dan haka da irin gatsen nan tace "Idan na amince zan aure ka Jibril, sai dai idan ka yarda zamuyi aure a sati biyun da ya rage a sa ranar da aka yi tsakanina da Yaya Larwan?"

Mai nema ne wai ya samu, kamar mai son ƙure ta sai ko Jibril yace "Na amince, wallahi Ummu na amince, ni ko yanzu kika ce zan amince, me zai hana na ƙi amincewa bayan wacce nake so ce zan samu tabbacin ta zama tawa ta har abada."

Karon farko da ta ji bata sha'awar yin aure, gaskiya ba ta so a ce ta auri Jibril saboda tsaran ta ne, gaba ɗaya ma auren ya fice mata a rai wallahi, to amma ya za ta yi? Kamar fa wuƙa xe ta sa a wuyan ta kula ta bashi damar yankar ta, ba zai yiwu ta kuma sake kawo masa wani uzurin ba ko dan kar girman ta ya faɗi, za ta zuba idanu ta ga me zai faru kawai, sai dai tana ji a jikin kamar ba lallai alaƙar ta da Jibril ta yiwu ba.

Dan kar ya ga kawai tana kore shi ne ba tare da dalili ba sai ta faɗa masa to ta yarda, amma fa bata buƙatar komai sai sadaki kawai, farin ciki a gurin Jibril ba ya misaltuwa saboda zai samu abunda yake so, ba tausayi ko jin wani wai bai dace ba, burin shi dai a ɗaura aure aga me zai faru, duk da ya san ahalin ta suna iya ɗaure shi kuma ya kasa ganin ko da rana, sannan yasan idan za'a bar shi da Fahad to tsaf Fahad zai kirɓa shi a turmi, amma fa haka ɗin, yayi niyya ne sai ya ga kalar zaren dake ƙugun matar nan sai dai daga baya a nemo shi a yanka. Ummu ma da tunda ta je gidan su Ammie ba ta dawo ba, duk da gida ne da ya fi nasu hayaniya da mutane, amma dai ta ji daɗi zama saboda kowa na faran faran da kai, sannan mahaifiyar Maman ta mace ce mai faɗa da zafi akan abu, tana da tsauri da kuma tsari ne da kai daga farko za ka ga takurawa gare ta, amma daga baya sai abun ya birge ka dan zaka fahimci gata ta maka. Kamar yadda zuwan Ummu na farko gidan da ta ga duk aikin gidan nan ƴaƴan kishiyoyin ta ƴan mata ne ke yi saboda ita bata da ƴan mata, sai Ummu ke ganin ai kamar tna azabtar da su ne saboda kishi da ganin ba ita ta haife su ba, sai ranar da ta ga hatta da pant ɗin su ita ke yin tsaye idan zasu wanke tana nuna musu yadda zasuyi, da kuma suka kwana ita da Eesha ta ga yaran komai suna yin shi ne da fara'a da sabawa da shi, ga kuma suke yi a nutse da kuma hankali, sai ta fahimci lallai *ƴa mace* duk muguntar da aka mata indai wajen aiki ne to wallahi *anfanin kan ta ne*, dan ba'a isa a ƙwace wannan abun da aka koya mata ba idan zata tafi wani gidan.

*Yadda* suka saba gaisawa bayan kwana biyu ya sa yau ma Alhaji da kan shi ya kira suka gaisa har ya bashi Kuwailat suka sha hira har yana tambayar ta "Amaryar Yaya Bilal ba wani abin da take so?"

Cikin shagwaɓa da turo baki Kuwailat ta amsa da "Ni zobe nake so na azurfa, yanzu garin mu shi ƴan mata da samari suke ya yi, sai kuma biscuit ɗin nan dake saka ni kumatu."

Dariya Abbu ya dinga ƙyalƙyalawa yace "To ba matsala amaryar Yayana, dake ai maman baby za ta zo, idan za ta koma sai na bata ko?"

Cewa tayi "Ah! To ai tare zamu koma, zuwa ne kawai za ta riga ni, amma nima na zo É—aurin auren Mamana."

Hakan yasa Abbu cewa "Za ki iya wannan yawon kuwa? Dan fa da zaren an É—aura aure za ta tare, kinga ke kuma ba zki iya wahalar nan ba, kin zo daga MaraÉ—i kin je Zinder, sannan zaku É—auko hanyar garin mu, ba fa zai wuce kwana biyu ba zaku sake juyawa zuwa Zinder É—in."

Ita Kuwailat ta ɗauka wajen komawa yake nufi, dan hka tace" Zan iya mana Grandpa, ni dai ku tanada min tsarabata, kuma Mamma (Fa'iza) ma ta min alƙawarin tsarabar da nake so."

Da tabbaci ya amsa mata da" To ba damuwa, Allah ya kaimu."

Da haka Kuwailat ta miƙa ma Alhaji waya ya amsa yana dariya da faɗin" Auta kenan, an girma ba'a san an girma ba, kullum cikin rigima take."

Dariya Abbu yayi yace" Haka fa, to ai ta ji kuna kiran ta auta ne, dole ta baku wahala kamar yada kuka so."

Dariya Alhaji yayi da irin kunyar nan yace" Gaskiya ne, amma ai in sha Allah Maman ta za ta ƙaryata mata wannan tunanin."

Shima murmushi yayi yace" Allah ya aminta."

Da" Ameen." Alhaji ya amsa kafin a nutse yace" Amma Alhaji, na ji kamar kuna maganar Zinder da waye waye? Dama shi Larwan É—in a Zinder yake da zama?"
Chapter 136 · 0% Book details