Sashe 38
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A kausashe Sa'ad da ranshi ya fara ɓaci na hawar masa kai da DG ke neman yi yace "DG waye kai da zaka titsiyeni kana min wannan tambayoyin? E ɗin tana tare da ni, da yadda zaka yi ne? Tun ranar da ta kubce daga hannun ku muka haɗu da ita, sai me...?"
Sai kuma ya matso daf da shi sosai ido cikin ido yace "Tana hannuna, kuma a halin da ake ciki yanzu ji nake ta zama wani *ɓangare na rayuwata*, dan haka ku manta da ita kawai kamar ma baku taɓa sanin ta ba, alaƙa ce ta kasuwanci dama kuma babu bashi tsakanina da Hambali, dan haka kai ma kaje kayi harkar ka kawai."
Wani sakaran murmushi DG yayi yana girgiza kai yace" Ƙarya ne wallahi, ni ba ina neman ta bane dan Hambali, saboda kaina nake neman ta, milyoyin kuɗi na karɓa akan alƙawarin zan isar da ita inda ake da buƙata, dan haka kawai *Sa'ad* ka bani yarinyar nan."
Shi ma malalacin murmushin yayi ba tare da damuwa da sunan shi da ya kira ba bayan baya faɗa ɗin a tausashe yace" Ban damu da nawa ka karɓa a kan ta ba, amma ka sani alhali gareta a nan ɗin, DG *ina son yarinyata*, kuma zan iya yin komai a kanta, ba zan bari ta shiga hannu ku ba inda ina numfashi, dan haka kamar yadda na faɗa maka kawai ka manta."
Girgiza kai DG yayi yace" Nima n ba gaya maka ba zai yiwu ba, wallahi sai ta dawo hannuna ta kowace irin siga, kuma zan iya yin komai dan ganin haka ta faru."
Wata sakaryar dariya Sa'ad yayi yana faɗin" Ka ganni nan DG, siyar da ƙwaya kawai nake amma bana shan ko sigari, dan nayi imani idan ina bushe-bushen nan wata rana zan iya aikata aiki irin wanda yanzun kake aikatawa."
Cike da jin haushin abinda Sa'ad ɗin ya faɗa nufin shi kenan yana shan ƙwaya, jinjina kai yayi yace" Shikenan, zan kuwa nuna maka aikin ƙwaya ziryan, abinda nake so na sani shine, shin tasan wanene kai?"
A haussale, a mugun harzuƙe Sa'ad ya sa tafin hannu shi na dama ya tura DG saida yayi baya ƙwarai kamar zai faɗi à zafafe yace" Wa ye kai da zaka min wannan tambayoyin? Ko Ibu zai tsare ni da wannan tambayar ne bare kuma kai banza wawa."
Da yatsa manuniya ya nuno shi cike da gargaÉ—i yace" Ka cire idanun ka akan *Æ´ata*, ko na maka abinda baka tsammani."
Yana faɗa ya juya a harzuƙe yayi ɓangaren shi, da kallo DG ya bishi cike da tsana da takaici, saida ya ɓace ma ganin shi sannan ya jinjina kai cike da cin alwashin yau ko gobe zai yi iya yin shi yarinyar can ta dawo hannun shi, dan ba zai barta hannun Sa'ad ba, kuma ta kowace hanya zai bi don ganin ya dawo da ita gare shi sannan ya sadata da wacce ta dace kuma ta masa baban biyan da yanzun yake shaƙatawar shi da wannan kuɗaɗen.
*A ranar* aka riƙe *Sauban* asibiti saboda ciwon sanyin ƙashi dake damun shi, ruwan da ake yi a kai a kai kuma shi ke janyo mishi dandanan bai da lafiya, Alhaji har mamaki yake yadda Sa'ad ke ta kai da kawo da larurar ƙanin nashi duk da ba uwa ɗaya suke ba, wanda a baya ba haka yake yi ba, yanzu ma haka bayan ya karɓo sakamakon da aka tabbatar sai an ƙarawa Sauban ɗin jini ya miƙawa maman Sauban ɗin wato Sabira takardun tare da cewa "Bari naje na siyo jinin, sun ce yanzu suke buƙata."
Karɓa tayi jiki a sanyaye tana kallon shi da mamakin sababbin halayen shi tace "To, angode Sa'ad."
Juyawa yayi ya fita ba tare da ya ce mata komai ba, Hajia Uwani dake zaune tana kula da duk shige da ficen Sa'ad ɗin tana mamakin wai me ye haka? Shin bai san duka matan baban shi ba ƙaunar sa suke ba? Bai san suna mishi hassada da rufin asirin da Allah ya masa ba? Shine zai yi ta wani rawar ƙafa akan ɗn Sabira dan bai da lafiya? Da sauri ta tashi ta bi bayan shi tana ƙwala mishi kiran Baban ta Baban ta! Saida ya sauka daga matakalar ɗakin ya tsaya yana juyawa ya kalle ta, tana ƙarasowa cikin gyara gyalenta tace "Babana, wai lafiya na ga sai wani hidima kake yi da yaron nan? Kuɗin banza ka samu ne?"
Da mamakin tambayar ta, da wani dogon kallo mai kama da hangen nesa yace "Mama, dama ana samun kuÉ—in banza ne?"
Cikin raɗa tace "Kai bana son iskanci, to in ba kuɗin banza ba, uwar yaron nan kasan ba ƙaunarka take ba da ni kaina, ba su da abun magana idan ba gulmar ka ba da tsegumin kana aikata abinda bai da kyau, su fa burin su kullum bai wuce suga ci bayan ka ba hankalin su sai ya kwanta, shine zaka zo kana ta wahalar da kan ka, bayan ga uban ka nan shi da ya auro jaraba can ya ƙarata da ita."
Ya kasa gane wannan hali na Maman shi? Ita wai me yake damunta? Shine fa babba a gidan su? Fisabilillah hanyar da take É—ora shi a kai ta dace kenan? Kenan bata fata ko bayan ran mahaifin su shi ya zama uba a gare su? Girgiza kai yayi a hankali yace" Mama, kenan na cire hannuna tunda dai ba ke kika haifi Sauban ba kamari yadda kika haife ni?"
Da yanayin rashin gaskiya tace" E to, ni nufina ka daina hakanan mana, ina laifin ka? Ai kayi ƙoƙari ko?"
Gyara tsayuwa yayi yace" Zan je na siyo jinin na kawo, zan koma gida na É—auko Aisha, Hajia ta ce ta bar ta tayi girki t taho da shi."
Wawan tsaki taja tare da kawar da kai tace" Hmmm! Aisha, Aisha, Aisha dai, wai kai me ye tsakanin ka da wannan yarinyar? Yaushe za ka maida ta inda ka É—auko ta?"
A hankali ya raɓa zai wuce, a zafafe ta riƙe rigar shi tana faɗin" Ƙashin babakere.... 🤣" Wata ashariya ta malmala mi shi ta ɗora da" Ina magana da kai za ka wuce ka barni kamar wata ƴar iska? Bari jin ina kiran ka Babana, wallahi tallahi zan mugun saɓa maka a kan yarinyar nan da ta nace maka, ni baƙin ciki na ma da ban san zaman da take a gidan nan ba, shikenan dan ka raina mutane kai ba za'a gaya maka ka ji ba?"
Ƙurawa fuskar ta idanu yayi yana kallo dake ɗauke da yanayin faɗa sosai, a hankali zuciyar shi ta fara raya mishi ko dai Dalilin da yasa kenan Ibu ke saurin kai hannu a jikin ta? To kana miji mata na nemanka da masifa, ka miƙe dan ka bar mata wurin kuma ta riƙeta ta na ci gaba da yi, shin ko baka da saurin hannu ba ka koye shi ba? Da sauri ya kawar da wannan tunanin ta hanyar sanyaya murya yace "Ga Ibu nan tafe, kar ya miki faɗa cikin jama'a."
Da sauri ta juya inda taga yana kallo, ai kuwa Ibun ne tafe daga masallacin dake cikin asibitin, a hankali ta sake shi tare da kausasa kallon ta gare shi tace "Kar ka É—auka mun gama maganar nan kenan, wallahi yarinyar nan sai ta bar gidan, dan canzawar ka ma nada nasaba da ita, har wanki fa Mujahid ya ce min ya ga kana mata."
Sai kuma tayi ƙwafa ta shige ciki tun kafin Alhajin ya ƙaraso, shi ma kuma a sukwane ya nufi hanyar shi tare da kallon Alhajin a taƙaice yace" Sannu da zuwa."
Madadin amsa mishi sai ya bishi da kallo yace" Sai yaushe za ka dawo?"
Juyowa yayi a hankali ya furta" Yanzun nan." Kawai ya sake juyawa ya wuce zuwa inda za shi. Bai ɗauka zai dawo yanzun ba kamar yadda ya faɗa, amma sai gashi ya shigo da jini da kuma likitar da zata saka mishi ƙarin jinin, hakan ya sake bashi mamaki har ya dinga saka mishi albarka a zuciyar shi, amma a zahiri da sun haɗa ido sai kowa ya ɗauke idanun shi ana ƙara shan kunu kamar wasu abokan gaba.
Bayan sallah magrib ya kawo Aisha asibitin, kamar yadda ta san babu mai ƙaunar ta a gidan, hakan yasa da ta zo ma tana zaune kan tabarma rakuɓe tana kallon su kawai, duk zaman da tayi a gidan nan haka take bata shiga rayuwar su, tana iya take kwana uku ma bata leƙa ɓangaren su ba, Leila ce ka kaita kuma tana zuwa da kan ta ɓangaren na Hajia, har ƙsan ranta take jin ta kamar wata tsiya ta yadda bata son rainin wayo, dan haka take baya-baya da su ita ma. Duk son ta da son ta samu kusanci wajen maman wanda take zaune gidan dominshi haka ta haƙura dan ta gama lura tana da wuyar sha'ani, so da dama t kan ga ko ta ji saɓani tsakanin ta da ɗan nata ma , hakan yasa bata taɓa ganin suna hira ta arziƙi tsakanin su ba.
Har ƙarfe 09:00 tana zaune ba um ba um-um dan Hajia ta tafi gida tun yamma, Sa'ad kuma ba zaune yake tunda suka zo ba yana ɗan kai da kawo ne, har sai yanzu da ya kalli agogon hannun shi sannan ya kalle ta, karo na farko a zaman su da ita da ya kira sunan ta da "Mu tafi ko *Eesha*, lokacin hutawar ki ya yi."
Kallon shi tayi tana murmushi saboda jin daɗin sunan da ya kirata da shi da ba wanda ya taɓa kwatanta hakan, a hankali ta yunƙura ta miƙe tsaye, dan har yanzu a hankali take bin jikin ta saboda aikin da aka mata, shi ma miƙewa yayi hakan yasa Uwani kallon shi tace "Gida kuka nufa kai tsaye? Ko wani wurin na daban?"
Saida ya runtse idanu saboda jin zafin maganar, sai ya dake kawai saboda mutanen dake É—akin yace "Gida zamu je Mama."
Yunƙurawa tayi tana gyara gyalenta tana cewa "Bari in biku to, na ɗauka ai wani gurin za'a je daga nan, na ji kace lokacin hutawar ta ya yi..."