← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 168

Sashe 113

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya maganar Aisha ta bata tana kallon Sa'ad, shi kam cike da shaƙiyanci ya rusuna a mugun ladabce yace ma Ummu "Babbar Yaya uwa, ina kwana ? Da fatan ba zaki ce ban miki ba, dan gaskiya ba mai raba ni da ƴata a wannan shekarun da nayi ina rainon ta tsakani da Allah."

Duk dariya aka yi, sai Aisha da ta harare shi ta turo baki, Yaya Bilal ne ya dubi Kuwailat da ita ma tayi dariya yace" Wannan Æ´ar ki ce ?"

Kallon Kuwailat tayi sannan ta sada kai cike da kunya tace" E."

Da hannu ya ma Kuwailat alamar ta zo, matsaxa tayi tana zuwa ta raɓa ta jikin shi yna faɗin" Ya kike? Ya sunan ki?"

Murmushi Kuwailat tayi ta sunkuyar da kai, ta ji suna kiran Maman ta Kuwailay, dan haka ta rasa to ya za ta ce? Hakan yasa Yaya Bilal cike da tsokana faÉ—in" Ke, ni fa mijin ki ne, yau aka É—aura mana aure ko? Tunda yau na san ki, dan haka faÉ—a min ?"

Cikkn ƙyalƙyala dariya Kuwailat tace" Kuwailat."

Da mamaki sukayi kallon kallo kafin Yaya Bilal yace "Kuwailat kuma? Da gaske sunan ta ne?"

Ya tambaya yana kallon Ummu, jinjina kai tayi tana murmushi tace "...

*Alhamdulillah.*

[19/08 à 11:19] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*53*

Jinjina kai tayi tana murmushi tace "E Abba, sunan ta Kuwailat, mahaifin ta ya saka mata sunan, saboda malamin da yake matuƙar sauraren wa'azin shi ya ce ba'a cika saka sunan Kuwailat ba, hasalima ni ban taɓa jin sunan ga wata ba sai akan ta."

Da mamaki Yaya Bilal ya sake rumgume Kuwailat yana ɗago haɓarta suka kalli juna yace" Ikon Allah! Da aka haifi mahaifiyar ki Kuwailat aka saka mata, sai gashi da ta ɓata an canza mata wani sunan, amma abu na Allah sai ƴar ta taci sunan."

Cikin tsokana kuma Yaya Bilal yace" To, yanzu dai ai kina sona ko? Dan fa ba zan bari wani ya kuma ƙwace min ke, kai kuma Mukhtar..." Ya faɗa yana kallon Abbu dake ta doka murmushi mai ban ƙayatarwa yau ga shi da duka ƴaƴan shi, shi kam me zai ce da ubangiji sai godiya, Yaya Bilal ɗorawa yayi da" Ka haƙura da wannan ka samo wata, ko ka ci gaba da zama da Nurriyar ka, wannan dai tawa ce."

A nutse Abbu ya zura hannu ya kamo hannun Kuwailat, tallabo fuskar ta yayi da hannayen shi biyu suna fuskantar juna, murmushi suke ma junan su cikin nutsuwa yace" Kuwailat, zaki bar ma Æ´ata wannan sunan? Ko kina son shi na bar miki?"

Da fara'a Kuwailat cike da kunya tace" Na bar wa Mamie."

Jin daÉ—i yasa shi sumbatar goshin ta sannan ya sake kallon fuskar ta yace" Kina kama da Maman ki sosai, ita kuma tana kama da Mamata, kenan dukan ku da wa kuke kama?"

Saida Kuwailat ta É—an waina idanu tace" Mammie, ko?"

Murmushi ya sake faÉ—aÉ—awa ya sake sumbatar goshin ta sannan ya kalle ta yace" Ni kuma fa?"

Daga bakin ta yake so ya ji, dan haka da Kuwailat ta furta" Grandpa."

Ya rumgume ta tsam a jikin shi kamar zai mayar da ita ciki, cikin jin daɗi yace" Na fi son wannan sunan, dan Yaya Bilal ya riga da ya ƙwace min *amaryata*."

Dariya duk sukayi, Mama n ba gefe ta tsagaita kuka ta ɗan yi murmushi tace" Daga yau ba ni ba ƙawance dake, tunda kin ƙwacewa ƴaƴana majazensu."

Nan la dariyar suka sake yi, sai Ummu da ta tausasa murya tana kallon Abbu tace" Abbu, ina *Mamie*."

Da sauri Aisha tace" Oh ! Autyn ki? Ina ga suna nan ciki." Ta nuna É—akin da tun shigowar su nan ta ga aunty Fa'iza ta fito. Murmushi Ummu tayi ta kai w Aisha duka a damtsen ta dake cike da nama tace" Bana son iskanci, kar ki tsokane ni mana bayan yanzu na san ina da ku."

Cike da farin ciki Aisha ta riƙo ƙgun Ummi ta kama ta suka nufi ɗakin tana cewa" To na daina *aminiyata*, muje na fara yi wa ƙawata albishir."

Da kallo Abbu ya bisu, sai ya ji hawaye sun sake saukowa a kumatun shi, yaran shi biyu mata da suka sha wahalar rayuwa, suka rabu tsawon shekaru ba tare da su ba, yau ga su ubangiji ya haɗa musu su dukan su, gashi har yana kallon su suna rumgume da juna suna nufa inda mahaifiyar su take, shi kam yana so ya ga farin cikin da zai bayyana a fuskar ta, yana so ya ga hawayen da zata zubar saboda ganin haka, duk da dai yasan bacci take mai nauyi, amma dole ta farka ko dan ciwon ta ya ƙare, haka ma wannan daskararren *ciwon* da ya jima *a zuciyar ta*.

A nutse da kuma sallama suka shiga, kwance take tana bacci abun ta da ƙarin ruwa a hannun ta, ƙarasawa sukayi inda Aisha tana tsaye Ummu ta zauna bakin gado, cikin nutsuwa ta kama ɗaya hannun Maman nata tana kallon fuskar ta cike da so da ƙauna da kuma tausayawa, a hankali ta kai ɗaya hannun tana shafa goshinta da gashi ya ɗan sauko mata, ƙara matsa kan ta tayi ga fuskar ta cikin raɗa tace " *Mamie*."

Shiru ba alamar za ta farka, hakan yasa Aisha zaunawa ta ɗaya ɓangaren ta ɗan daddaɓa Maman, girgiza mata kai Ummu tayi tace "A'a, ki barsu suyi baccin su, ai ba guduwa zanyi ba."

Da raha Aisha tace "To naji shikenan, amma dai ya kamata ta farka, dan tana ganin ki ciwon nan zai ƙare mu koma gida."

Murmushi kawai Ummu tayi tace "Da alama ƴar ƙiriniyar ƙanwa na samu."

Dariya Aisha tayi ta turo baki tace "Kema aunty haka za ki faÉ—a? Abbu fa haka yake cewa."

Da tabbaci Ummu tace "Ni ma da yanzu muka haÉ—u na faÉ—i haka, bare kuma Abbu da ya haife ki."

Da sauri Aisha ta girgiza kai tace "Um um, ba Abbun mu, mijina nake nufi, Sa'ad."

Da mamaki Ummu ta game fuska tace "Shine Abbun? Lallai daÉ—i miji."

Dariya Aisha ta sake ƙyalƙyalewa da ita tace "Ba haka bane aunty, na saba ne wallahi, saboda lokacin da ya taimaka min ina kallon sa ne kamar uba, hakan yasa nake kiran shi Abbu, sai kuma ya zo ya ce yana so, to dake nima ina son abuna sai kawai mukayi aure, shine kuma na kasa daina kiran shi Abbu."

Da fara'a da kuma irin gargaɗi Ummu tace" Eesha." Cike da kunya Aisha ta rufe idanu tana dariya tace" Na daina aunty, amma fa kema zaki zama kamar ni, saboda kinga ƙawata gaba take saka mutum sai sunyi hira ko baya so."

Da mamaki Ummu ta kalli maman da Aisha ta nuna ta kirata ƙawa tace" Ƙawa kuma?"

Jinjina mata kai tayi tace" Haka take kirana, ni ma kuma ta ce ai ƙawata ce, dole na saba mue ƙawance, saboda an ce uwa ta samu kusanci da ƴaƴan ta mata sosai."

Jin daɗin hakan ya sa Ummu faɗaɗa murmushin ta ta sake kallon fuskar Maman, ita wai da ta rayu a gidan share ka zauna, suka rayu da yunwa, sai an fita an nemo za su ci, wata rana ma ba'a samun na cin, ta yi karatu a makaratun gwamnati saboda babu halin yin na kuɗi, yau ita ce ta wayi gari a wata sassauƙar safiyar *juma'a* da ta shiga tarihin ta a rayuwa, ta haɗu da uba wanda ya haife ta, sannan ga ta ga uwa wacce ita ce ta haife ta, ga kawun ta wanda a baya bata da shi, dan ƴan uwan margayi baban ta basa wani ɗaukar ta da mahimmanci kasancewar ba shi ya haife ta ba, Mama kuma fulanin jeji ne da ba wani babban ahali bane sannan ba mazauna kusa da ita ba, hakan yasa dai rayuwar ta ta daga ita sai Mama sai su Nabila, sai kuma mijin ta... *tsohon mijin ta* da ƴan uwan shi suka zama ƴan uwa gareta, da suna girmama ta da bata darajar ta, sai kuma abokanan arziƙin da ita ta ma kan ta su.

Yau kuma, ita Ummu Kulsum ɗaya ce a ciki ahali *Ahlan*, ahalin da ko a mafarki bata taɓa hango wata alaƙa ta nesa tsakanin ta da su ba bare ta kusa, yau ita ma ƴa ce ga wannan gida... Murmushi ne ya suɓuce mata, jiya jiya ta rabu da mijin da take ganin shine gatan ta a duniyar nan, tayi kukan rashi Alhaji saboda yarda da tayi cewa shine makomar ta, gatan ta, rumfar da ta fake, ƙashin bayan da ya taimaka mata ta tsaya, abu alfaharin, masoyin ta sannan kuma uban ƴar ta.
Chapter 113 · 0% Book details