Sashe 15
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali dreban ya ja ya tsaya, kafin su bata umarnin fita ma ta buɗe motar ta fita da ɗan gudu gudu ta nemi shiga wata kusurwa dake tsakanin wasu gidaje, da sauri ƙaton nan ya fito daga daga motar ya nufi kusurwar shima, amma yana ganin Aisha tana shirin saɓule siket ɗin ta sai yayi saurin juya mata baya bayan ya bita da kallon oho! Ashe kina nan ? Ganin ya juya baya yasa Aisha fara takawa a hankali tana ɗan ja baya tana yi kuma kamar za ta duƙa har saida ta shige kwanar dake jikin gidan, kafin kace kwabo ta faɗa wani matsakaicin gida wanda mai gidan ya buɗe ƙofar yana shirin fita wajen aiki...
Yadda ta faÉ—o gidan yasa shi dakatawa daga shirin jefa jakar shi cikin mota yana kallon ta, sai kuma ya kalli amaryar tashi da ko wata uku basu cika ba da aure yace "Kin san ta ne?"
Wani kallo ta fara jifan shi da shi matashiyar, sai kuma tace "Kamar ya na santa? Idan ma na san ta za ta shigo mana hakane da gudu?"
Aisha da bata yi tsammanin ganin mutane a farfajiyar ba tsare su take da shanyayyun idanunta kamar wacce aka aiko ta ta karancesu, jin mai gidan na faɗin "Shiyasa nake gaya miki ki kiyaye jawo min maƙwabtan nan, b dama suka gana sake musu fuska sai su..."
Kafin ya gama faɗa Aisha tayi saurin gyara siket ɗinta da ta tattare tana ɗan takawa kusa da su tana cewa "Assalama alaikum, kuyi haƙuri dan Allah? Na shigo muku kai tsaye haka ba, wallahi wasu mutane ne suka satoni tun daga garinmu, kuma ni ban san su ba kuma ban san nan a ina muke ba, yanzu ma wayo na musu shine na gudo, dan Allah ku taimaka min? Idan suka duba basu Ganni ba nasan zasu tafiyar su sai na tafi."
Kallon juna matar da mijin sukayi, sai kuma dukansu suka bita da kallon rainin hankali da rashin gamsuwa da abinda ta faɗa, sai kawai mijin yace" Baiwar Allah, dan Allah ki fitar min a gida kin ji, nan ba wajen taimako bane, sannan ni na sha haɗuwa da ire-irenku, dan haka ki fita ko na fitar dake ta ƙarfi."
*Dake* ƙofar gidan nasu ce kawai a buɗe a wannan lokacin, hakan yasa dreban nan da ƙaton da suka biyo ta da gudu gudu suna duddubawa dn ta ɓace musu yasa su leƙo kawunansu cikin gidan, da sauri kuma suka janye kawunan nasu ba tare da sun ga Aisha dake gefen hagunsu ba ta raɓe tunda ta ji kamar sautin gudu an nufo gidan, dreban ne ya ɗan ɗagowa mai gidan hannu dake bin su da wani irin kallo har ya rufe mota ya tunkaro su da niyyar sai ya mari ɗaya à cikinsu, dan yadda suka faɗo masa gida haka tare da kalle masa mata dake sanye da kayan bacci a jikin ta abun ya ƙona masa rai, kafin ya isa gare su kuma dreban da ya ɗgo masa hannu alamar gaisuwa ne yace "Barka yallaɓai, dan Allah wata yarinya muke nema, bata shigo nan ba?"
Matar da ta ji mijin bai amsa ba, sannan yana tunkarar su da yanayin nan nashi na rigima da ta sani dan yaje garesu ayi duk wacce za'a yi yasa ba tare da tayi tunanin komawa É—aki ta saya shigar ta ba tace" Yarinya? Æacewa tayi?"
Da azama dreban yace" A'a madam, nemanta ne muke, har gidan oganmu ta shiga ta ɗaukewa matarsa sarƙarta mai tsada da kuma kuɗi, daga yin talla fa, dan Allah kun ganta ne? Na tabbata bata yi nisa b..."
Tunda ya fara magana matar ke kallon Aisha da ta rarako manyan idanunta tana girgiza mata kai da mata alama dan Allah tayi shiru da bakin ta, shi ma mijin daga ƙarshe kallon ta yayi sai kuma ya kalle su yayi saurin katse shi da cewa" To dan kuna neman yarinya shine zaku faɗo min gida haka dan Allah? Yanzu idan kune aka wa haka zaku ji daɗi?"
Tunanin kar mijin ya fallasa yarinyar yasa matar saurin cewa" Allah sarki, bamu ganta ba gaskiya, bata shigo nan ba."
Da sauri mijin ya juyo ya kalle ta jin ta zabga ƙarya daga nan tsaye, shi fa so yayi ya faɗa dan a kamata, wato da ta shigo musu nan dan su ma ta yaye su ne ko? Amma bai ce mata komai ba sai kallon _" Ya haka kuma?"_ Da ya bita dashi sannan ya kalle su yace" Bamu ganta ba."
Ɗaya ƙaton nan tsaf ya karanci yanayinsu, amma tunda safiya ce sai ya jinjina kai kawai ya ma dreban alama da su tafi, amma tabbas zai dakonci fitar mijin ya dawo gidan dan yarinyar n'a cikin gidan nan.
Suna tafiya ya faÉ—awa dreban yadda zasu yi, Aisha ma na ganin tafiyar su ta fito daga É—an lungun daya shamakesu da ganinta ta haÉ—e hannaye ta ce ma matar "Nagode sosai Aunty, nagode miki Æ™..."
Ɗaga mata hannu tayi tace "Kinga, ni bana taimake ki bane dan ina goyon bayan halinki, tausayi kawai naji kina bani dana kalli idanunki, amma ki sake hali ƙanwata, wannan ɗabi'ar bata dace da namiji ba ma bare mace."
Kallon mijinta tayi tace masa "Sai anjima Bebe, sai ka dawo, idan ta fita ka kulle min ƙofata ta baya."
Murmushi ya mata ya jinjina kai sannan ya kalli Aisha yace "Bismillah ko?"
Marairaicewa tayi tace "Dan All..." Sai kuma taga tuni matar ta shige ɗaki, hakan yasa ta juya jiki a saɓule da kuma ɗar ɗar ta fita a gidan tana leƙe, ganin bata hangesu ba sai tayi hannun ta na hagu duba daga hannun hagu ta fito ta shigo gidan nan, tana leƙa kwanar ta tabbatar babu su anan ma da gudu ta sake yankar na kare, inda mijin nan yayi yadda matar ta faɗa masa ta hanyar rufo ƙofar da makulli daga baya sannan ya fita yana ta nanata abinda ya faru yanzun.
********************
Murmushi ne ya suɓuce mata na murnar abinda Alhajin ya faɗa mata ya yanke shawara a kan Jabir, ba ƙaramin farin ciki tyi da hakan ba, dan haka ma ita ce gaba cike da ƙarfin guiwa dan su sanar da Jabir ɗin abinda suka yanke.
Zaune suka same shi yana kallon ciwon shi na ƙafa da ya kame sosai saboda maganin da Maman su Ummu ta bashi, ba dan yadda y fito daga gidan ba shiri ba ma ai da ya taho da maganin shi ya ci gaba da shafawa, fitowar su ta sa shi gyara zamanshi a ƙasan carfet yana sadda kanshi ganin Alhaji Kabir ya riƙe hannun Ummu Kulsum dake ta hanzarin ta kawo ga Jabir su zauna su faɗa masa abinda suka yanke, fatan ta shine ya amince, burin ta ya amince da shawarar tasu, dan gaskiya ita fa ta tsani mahaifin nan nashi bare kuma matar sa.
Alhaji Kabir kuma da ya ga Jabir ya sadda kanshi ƙasa baya kallon su, sai ya samu damar riƙo ƙugunta ya dawo da ita baya kaɗan saboda tashin hankalin dake ziyartar shi sakamakon tafiyar da take da sauri jigidarta kuma sai sauti take bayarwa dake nuna ana tafiya ita kuma tana kaɗawa. Cikin salo da dubara ya ɗan rufe mazaunanta da babbar rigar shi sannan ya shafi inda ke ɗauke da jigidar yana tsare fuskar ta da kallo cikin sigar raɗa yace "Ita wannan abar haka take ne da tonon silili?"
Ummu Kulsum dake ta zaro idanu tunda ya riƙo hannun ta take juyawa dan ta ga ko Jabir na kallon su, sai taga dai kanshi na ƙasa kuma har wannan lokacin, cikin dubara da son ƙwatar kanta dan kunya ta mishi raɗa ita ma da cewa" Ba haka bane, sake ni mana kar ya gan mu fa."
Ɗan kallon Jabir yayi sai kuma ya kalle ta yace" Yaro ne mai nutsuwa da hankali, dubi, kanshi a ƙasa? Yanzu amsa min tambayata."
Cikin sigar shagwaɓa da turo baki tace" Ba haka bane, nima ban san me yasa take haka ba, haka dai take kawai."
Ɗauke hannun shi yayi daga ƙugun nata tare da sakin ta yace" Tana ɗaukar hankalin na kusa da ke, ina fata ba duka namiji zai ji kaɗawar sautin ta ba, dan ƙarar ta na ɗaukar hankalina sosai."
Murmushi tayi tana ƙara nutsa kanta cikin babbar rigar shi da kunya tace" Da gaske? To ai Maman mu ce ta saka min, kuma tun ina yarinya ma nake da ita, kawai tana sassauya mana ne."
Wani basaraken murmushi ya sakar mata yana jin kamar ana dawo masa da ƙuruciyar sa ne ya laƙaci hancinta yace" E mana, a ƴan kwanakin nan da muka yi tare da ke, da sautinta nake iya gane nisan tazarata da ke."
Faɗaɗa murmushi ta tayi tare da rufe fuskar ta, shi ma dariya ya yi ya shiga gaban ta ya samu kujera ya zauna yana kallon Jabir da kanshi ke ƙasa har yanzu yace" Malam Jabir kana zaune?"
Ummu ma takowa tayi ta samu kujera ta zauna sa'ilin da Jabir ke faÉ—in" E Abba, sannu da fitowa?"
Yana gyara zamanshi yace" Yawwa Jabir, sannu, ka ci abincin kuwa?"
Da nutsuwa yace" Na ci Abba, Alhamdulillah."
" Ma sha Allah." Ya faÉ—a yana sake maida dukkan hankalinshi ga Jabir É—in sannan ya kira sunan shi da" Jabir."
A tausashe shi ma ya amsa da "Na'am."
Cike da dattako ya fara faɗin "Jabir, ina da yaro mai sunan Aliyu, burinshi ɗaya da naka wato zama mai ilimi, sai dai kai kana son faɗakarwa idan ka koya saɓanin shi da kawai yana so ya koya ne dan ya san yadda zai bautawa ubangijinsa, yanzu haka yana Saudia a babbar jami'ar dake ƙasar yana karatun shi, shekarar sa ɗaya da tafiya, kuma yana so idan ya kammala da nan akwai malamai da alarammomi da ya faɗa min yana son zuwa Sudan dan koyon karatu a wurin su har ma da kalar ƙira'o'i, da wannan ne na yi shawara da Ummu Kulsum kuma ta bani goyon baya."