← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 166 OF 168

Sashe 166

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*76*

Komai na tafiya daidai a rayuwar su, kasuwancin su ma mazajen su na taimaja musu tare da haɗin guiwar ma'aikatan da tun fil'azal, arziƙi kam ma sha Allah bunƙasa yake, gashi kuma sunyi sa'ar maza da basu saka idanu akan dukiyar su ba, bare ma Jabir da nashi harkokin ke ta kara sako shi gaba, sai dai a ce Alhamdulillah.

Haka a zaman auren su ma farin ciki ya fi komai yawa a ciki, dan zama ne da fahimtar juna ya samu wajen zama, hakan yasa basu cika samun saɓani ba, dan ta ɓangaren Aisha da Sa'ad ita ce ke kiran shi *Abbu*, hakan yasa tana masa komai ne da mutumtawa, yayin da tayi laifi kuma sai ta masa takwaf takwaf da fuska ta ce uba ne shi ai yayi haƙuri, sai kuma ya ɗauki halin Annabawa yayi haƙurin. Ita ma dai gyambon haka take, ba dan ma yanzu rigimar da ita kan ta tana bata mamaki da ta koya, dan yanzu kaɗan a aikin ta ne idan yana mata wani abun musamman ma ta masa ba daidai ba yana faɗa, ta ga da gaske Jabir faɗa yake mata irin dai na miji da mata ɗin nan, sai ya samu nutsuwa musamman idan ta cika mishi cikin shi sai ta riƙe haɓa tana kallon shi tace _"Fisabilillah ɗazu da kana min faɗa baka ji nauyi ba? Jabir ba dan ƙasusuwan jikin ka da suka baka haɗin kai ba har ka kamo ni a tsawo, kana ganin da yanzu ba'a can cikin ƙasa kake ba?"_

Dama da ta faɗi haka sai ta fara murmushi, dan kuwa ko kallonta ba ya yi yake faɗin _" Ki sa ƙafa ki take ni mana, kinga saina koma cikin ƙasar."_

Da ya faɗi haka sai ta kawar da kai ta taɓa baki tace _" To Allah ya shirya min kai, amma wallahi ba dan mutane ba *gafarta* da ba abinda zai hanani yanko maka form ka cike ko ka samu damar shiga jerin dakarun oga (sheɗan🤣), dan abinda kake min ba dan ina da haƙuri ba kuma na ɗauki girman na yarda wauta ba abinda ba ta sakawa, ai kaima kasan da tuni na bubbuga ka a ƙasa."_

Dariya yake yi har yana tintsirawa, kafin ya rumgumota jikin ta ya haɗa kan shi da goshin ta yace" Na sani mana Maamana, shiyasa ai naa zaɓe ki, dan ke kaɗai ce zaki iya haƙurin zama da ni, yanzu ba gashi ba, muna zaune abun mu muna ta bautar ubangiji."

Jinjina kai take yi tace" Umm! Kuma gobe ma in sha Allah zamu tashi da azumi ko?"

Kanne mata idanu ɗaya yayi yace" Haƙƙun, kuma Maama zata shayar dani ko?"

Ita ma idanun ta kanne mishi tace" Me zai hana? Dan na san ka gwanin sirri ne ai."

A tare sukayi dariya suka ci gba da hirar su, kafin Ummu ta ɗauki wayar ta tana dubawa ta ga saƙon Aisha, ganin Video da sauri ta buɗe tana miƙewa tsaye tana faɗin" Kar dai yrinyar nan ta haihu ba ta gaya min ba? Sai yanzu zata turo min hoton yaro."

Kallon ta Jabir yayi yace" Idan ta gaya miki me zaki mata?"

Kallon shi tayi tana faÉ—in" Ni nake so fa na rakata asibiti."

Taɓe baki yayi yana ɗaukan tashi wayar da tunanin ya kira Sa'ad ma wallahi ya msa kashedi kar ma a fara, kai shi fa akan Maama zai iya yiwa kowa gargaɗi amma ban da mutum huɗu, na farko *Abban shi* wanda shi ya haife shi ya kawo shi duniya, na biyu kuma *Abbu* wanda shi ya haifa masa wacce ta jima da zama *rayuwar sa*, sai na uku *Alhaji Kabir* wanda shi ne ya masa gatan da babu wanda ya kwatanta yi masa a duniya, sai na huɗu kuma *Aliyu*, Aliyu: ƙwarai Aliyu halin Abban su Alhaji gare shi, ba ya da ƙyashi, ba ya da hassada, ba ya da baƙin ciki, sannan ya zamar masa komai a rayuwa, ban taɓa tsammanin Aliyu zai fahimci maganar auren shi da Ummi ba, amma sai gashi sahun farko a cikin mutanen dake son jawo hakalin shi kan ya aikata hakan, ya jima yana so ya ga canji daga Aliyu da ya ja baya da shi shima, amma wallahi Aliyu yadda kasan copie ne na shugabanmu Aliyu na asalin wato zaki, sai hakan ya ƙi zuwa a kan shi ma bare har a gani a fuskar shi, har yau har gobe Ummu yanzu kallon budurwar da suka haɗu da ita a titi yake mata suka nemi auren ta aka bsu, yana kiranta da aunty ne kawai saboda sabo, hakan yasa bai ma Aliyu shamaki da gidan shi ba, kowane lokaci ya kan iya zuwa neman sa idan yna nan, haka kuma ko yunwa yake ji ya kan gayyace shi gidan shi, dan yanzu shima burin shi shine ya saka musu da alkairi mutanen nan da halin girman su ya zarce misali.

Vodeon na buÉ—ewa Ummu ta sauke ajiyar zuciya ta koma ta zauna tana aje wayar da cewa "Haba yarinya, nima zan rama wata rana, dan kinga malam nake aura ko? Kana saka kiÉ—a ma za'a fara maka wa'azi."

Wani kallo ya mata mai kama da hagen nesa yace "Kulsum, wani lokaci abubuwan ki kamar dai irin ba ue kaÉ—ai ba ko? Sai kina abu haka kamar dai an baki ajiyar burkutu."

ÆŠan hararen gefen shi tayi tace "Ai da kalansir nake kwana a É—aki *É—an Maama*."

Jinjina kai yayi yana É—aukar wayar ta ta yace "In ga me ye Aisha ta turo da ni ba zan iya ba ake ci min mutumci?"

Kallon shi tayi tace "Kar ka sani a baki."

Jawota yayi jikin shi yana faɗin "Zo nima na nuna miki tawa ƙwarewar?"

Da sauri ta miƙe tana faɗin "Bari in dawo, kaga wainar flawa kawai naji ina sha'awar ci yanzun nan."

Da wani irin kallon haba ɗin nan ya bita har ta shige. To fa haka rayuwar tasu take tafia gwanin ban sha'awa, ga taimakekeniya tsakanin su da su kan su har birge juna suke, dan takanas ta kano Jabir saida ya wakilceta a wani taro da aka yi a kamfanin su ita da Aisha, kuma tare da. Sa'ad ya tafi suka dawo lafiya, kamar yadda ita ma akwai ranar da ta wakilce shi a makaratar Aliyu, ba kuma wani uzuri bane ya hana shi, sai dai ya zo inda zai ɗan fayyace wani sirri ne ga matan ajin shi kuma yana ji nauyin jaka, bugu da ƙari Kuwailat ma na wannan ajin a lokacin, sai ya bata wannan awa ɗaya ɗin ta musu darasin, bata ji nauyin Kuwailat ba dan abu ne da dama tana ɗan ɗorata a hanya akan wasu abubuwan, abun mamaki su kan su ɗaliban a ranar da ya koma sai suka faɗa masa sun fi son darasin malama, dan ita mace ce sannan har fari da ido ta koya musu yadda ake yi.

*Tun kwana uku* da suka wuce take ta lisafin rabon da ta ga al'adar ta, sai abun ya fara damun ta sai kuma ta wayance ta hanyar faÉ—in "Ibu É—in da ta sha lokacin da aka mata É—inki ne ya jirkita mata kwankin al'ada, Shiyasa dama bana son shan shi wallahi saboda haka yake min."

Sai kawai ta basar da maganar ta shiga wata harka daban. To zuwan Kuwailat gidan yi mata hutun sati ɗaya ya sa ta gano dai da gaske ciki gare ta, Kuwailat gani tayi maman ta tayi ƙiba sannan ga cikin ta da ya taso sosai, sannan wuni take bacci ga rashin son aiki, dan ranar da ta zo ma saida ta mata sharan ɗaki da guga ta ce tun jiya ba ta yi ba ita, sannan ta ga idan tana zaune *Yaya Jabir* idan ya shigo wanda har yanzu ta kasa cnaa mishi suna daga Yaya sai ya zo yake kama hannayen ta sannan su shiga ɗaki amma ba ta iya tashi musamman idan ta gama cin abinci kenan.

Shine ranar suna zaune Kuwailat tace "Mamie, idan Allah ya sauke ki lafiya ina so nayi walima ni da ƙawayena kawai, dan lokacin zai iya daidai da gam a jarabawar mu."

Kallon Kuwailat tayi irin mutum yayi abun mamaki gaban kan nan, sai kawai ta kalli cikin ta sannan ta kalli Kuwailat tace "Idan na haihu fa kike nufi ko?"

Da farna Kuwailat ta amsa da "E Mamie, dan Allah kada ki hanani Mamie."

Sai kawai Ummu ta miƙe zunbur duk da batayi niyyar tashi ba a lokacin, ɗaki ta shiga ta ɗauko wayar ta da jakar ta da ta san akwai kuɗi ciki da makullin motar ta ta fito, hijabin ta na sallah ta yafa tace wa Kuwailat" Idan *Abbun ki* (Jabir) ya shigo dan girman Allah ce masa asibiti na tafi, gwara su gaya min gaskiya, da gaske Jabir ciki ya min ko me yake nufi?"

Tayi maganar tana ficewa daga falon. Lokacik shigowar shi ne dama, hakan yasa tana fita ya shigo, a ladabce Kuwailat ta masa sannu da zuwa ya amsa sannan ya tambaye ta maman ta? Amsar ta bashi da ta tafi asibiti yanzu, duk da ta ce masa fita tayi, amma da ya tambayi Kuwailat yace "Asibiti? Yin m? Ko wani ne ba lafiya?"

Sai kawai tace masa "A'a lafia lau, ina ga dai awo ne zata je yi ko gwaji."
Chapter 166 · 0% Book details