Sashe 133
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ta faɗa masa hakane dan yaji ya kuma haƙura ya cire ta a ran shi, ai kuwa tashin hankali da damuwa da mamaki suka gani ƙarara a fuskar shi har ya ɗan tambaya a razane" Me? Aure?"
Jinjina mishi kai tayi cike da tabbatarwa tace" E wallahi."
Lumshe idanu yayi yana ayyana _" Shikenan hatta da alwashin da ya ci a kan ta a gaban yaron nan ustaz ya tashi a banza kenan?"_
A zahiri kuma sai ya furta" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Hasbunallah wani'imal wakil!"
Fuskar shi ɗauke da damuwa ya kalle ta a sanyaye tamkar da gaske yace" Ba zan ɓoye miki ba *Nur*, wallahi ban ji daɗi ba, hasalima ban san ya zanyi ba yanzu, ban taɓa jin ba zan same ki ba wallahi."
Cike da rashin jin daɗi Ummu ta ɗan kalli Mamie da ita ma tausayin Jibril ɗin ya lulluɓe ta tace" Ayya! Kayi haƙuri kaji Jibril, ni ban san akwai wani abu tsakanin ku ba ai, kayi haƙuri kaji, Allah ya baka wacce ta fita, wanda zata auta yanzu ɗan uwan ta ne na jini."
Kallon Maman yayi bai ce komai ba, matsawa yayi kusan da ake biyan kuÉ—in ya É—auki siyayyar da sukayi yna É—orawa dan a lissafa musu kuÉ—in, ana faÉ—in kuÉ—in ya ciro kashh ya biya, Mamie saida ta zaro idanu dan fa duka siyayyar da sukayi ce ya biya, to ya zasu yi da nasu kuÉ—in? Ba fa zai samu Ummu ba, ya san da haka kuma ya musu wannan wahalar, yana biya kuÉ—in juyowa yayi kawai ya kalli fuskar Ummu yace "Nagode Nur, sai anjima."
Sai ya sake ɗaure jijiyoyin Ummu, wato irin mugayen mutanen nan sun san lagon karya zuciyar mace, Jibril na tafiya ne a hankai yana wani dafe kan shi har ƙoƙarin karo da mutane yake yi da kai wa bango karo, hakan yasa Ummu da suke ya kallon shi Mama na ɗaukar kayan tare da yaran shagon tace "Na shiga uku, aunty kar ya je ya ji wa kan shi ciwo, anya zai iya tuƙi kuwa? Wayyo Allaj, wallahi ya bani tausayi."
Shiru Ummu tayi dan gaskiya ita ma wani abu take ji game da yaron, wallahi... To a dai bar kaza cikin gashin ta, haka suka fito daga wurin jikin su duk a mace bayan an loda musu kayayyakin da suka siya sannan suka É—auki hanya.
Suna hanyar komawa gida Ummu ke waya da Mama, da mamaki Ummu tace "mama, da gaske zaku zo? Yaushe?"
Daga ɓangaren Mama ta bata amsa da "Ban saka lokaci ba Ummu, Yayan ku nake jira ya saka min ranar, amma ni ko gobe ya ce ga tikiti to zaki ganni."
Da farin ciki sosai Ummu tace "Kai! Amma Mama naji daÉ—i, wai har kun fara kewata haka?"
Da irin bsarwa Mama tace "Ke dallah! Kewar ki É—in ki me? Ni wajen Hajia zan zo, kinga sun fita daga wanka lafiya ban zo na musu barka ba, ga kuma godiya da nake so na zo nayi a madadin su Malam da su Kubra, dan duk sun ce sun É—ora min nauyin, sai kula É—aurin auren ki da nake so na riska."
Da fara'a Ummu tace" Lallai Mama, ki ce dai idan kuka zo sai wanda ya ga komawar ku? To gaskiya Mama Yaya Luƙman yayi maza ya sako mana ku ku dawo nan, dan ni wallahi ina kewar ki Mamana."
Murmushi Mama tayi tace" Amma idan na tashi zuwa zan zo miki da ƴar ki, dan kinga dai ranar Alhaji da kan shi yarinyar nan ta taso ya zo ya kawota ana ta rarrashi, shekaran jiya kuma nake gaya miki Aliyu da Jabir ne suka zo ɗaukar ta amma ta botsare ita ba zata koma gidan nan ba, saida fa Jabir ya mata magana cikin tattausan muryar nan tashi, ja'ira yadda kika san uban ta haka ta amsa mishi ba ɓata lokaci."
Dariya Ummu tayi tana kallon Mama dake tuƙi tace" Ai Mama Kuwailat har da shegantaka dan taga ba ma dukan ta, ai da zane ta kuka sa Aliyu yayi, in ba haka ba budurwa da ita zata zauna kukan Maman ta."
Mama Nuriyya da ta fahimci zancen kallon Ummu tayi tace" Dan taga ita kaÉ—ai ce a gaban ki, ki yi auren nan dai ta ga kin fara haihuwa, za ta nutsu ne ai."
Kallonta Ummu tayi tace" Auntyyyy."
Mama dake sauraren su cike da goyon baya tace" Wallahi hakane, ai dan ta ga ita kaÉ—ai take wani iskancin, ni dai zan zo miki da Æ´ar ki."
Turo baki Ummu tayi tace" To Mama karatun fa? Haka za ta gintse shi saboda son ran ta."
Mama ce tace" A'a Aliyu ne ya ce wai ba damuwa mu taho tare, ni ma nace mishi a'a ya ce ba komai."
Girgiza kai Ummu tayi tace" Mama, wallahi Aliyu na ji labari a wajen Zeinab baya ɗagawa yaran gidan nan ƙafa a kan karatu, kawai Kuwailat tausayin bana gidan da kuma kunyata ya sa yake ɗaga mata ƙafa, amma ku bari zan kira shi yanzu muyi magana, kun ga sai ku taho kawai ku barota, idan Eesha za ta taho sai su taho tare, dan ko jiya munyi magana da mijin ta (Sa'ad) ya ce shi fa sai ana jibi ɗaura auren zai bar ta ta zo."
Cike da gamsuwa Mama tace" Gaskiya dai kam ya fi." Sai anjima sukayi da cewa za ta kira Aliyu yanzun nan suyi magana.
********************
Jabir na ofishin na Aliyu yana nazarin wani littafi sabodz ƙudurin fara rubuta wani abu da yake da, amma yana ɗan bincike a kai da ci gaba da neman sani wanda har yake tunanin tafiya Kano da haɗuwa da malami biyu rak, sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da kuma Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar lemu, a gajiye Aliyu ya shigo yana zama kan kujera tare da ɗaukar ruwa ya sha, saida ya sha sosai ya sauke numfashi ya kalli Jabir da tunda ya ɗaga kai sau ɗaya ya kalle shi bai sake duban shi ba saboda mahimmancin abinda yake yi, wayar shi ya ɗauka tare da kunna data dan ya ga me ke faruwa? Lokacin ne kuma ya kalli Jabir yace "Koyarwa da wahala, ban san ko zaka iya ba?"
ÆŠan kallon shi Jabir yayi a nutse yace "Me zai hana? In dai zaka biyani da kyau."
Maganar biyan nan da Jabir ke yi ya fara saka shi tunanin wani abu, anya zai iya ɗaukar Jabir aiki a makarantar nan kuwa? Taɓe baki kawai yayi ya kalli wayar shi yana faɗin "Sai na haƙura d kai ɗin, dama dai a Ƙur'ani kafi ƙarexa sai kuma Hadith, in sha Allah ba zan rasa madadin ka ba."
Kallon shi Jabir yayi sosai yana É—an murmushi yace "Hakane, amma kasan an ce *ba rabo da gwani ba*..."
Jinjina kai Aliyu yayi yace "Gaskiya ne, kuma na sani indai canza murya wajen ƙira'o'i ake nema aka zo kan ka za'a dakata, sai kuma..."
Sai kuma ya jinjina kai da irin tabbacin nan yace "Alhamdulillah ubangiji ya baka kaifin harda wanda hakan yasa kake da sani sosai akan tasfirirrikan malamai da dama, kuma kowane ka karanta nashi tafsirin tsaf yake zaunawaa kan ka."
Murmushi Jabir ya sake yi tare da furta "Alhamdulillah, nagode Allah da ya sa na zama É—aya daga cikin rabe-raben mutane, ina da naci akan abu idan ina son hardacewa, abinda kuma ya fi saurin zauna min kai sannan na jima ban mance shi ba, shine idan na hardace shi irin bayan sallah asuba, Alhamdulillah, wannan shawarar malamina ce."
Murmushi Aliyu yayi yace" Gaskiya ne, Allah ƙara ilimi mai albarka."
A tausashe ya amsa da" Ameen Ya Allah."
Shiru suka É—an yi na sakanni, hakan ya ba Aliyu damar maida hankalin shi kan waya, shi kaÉ—ai kawai yayi dariya, ba wai dan ya cutar da Jabir ko ya ji ba daÉ—i ba, irin dai abun nan da zai sa kayi magana kai kaÉ—ai haka, cikin raha yana dariya yace" Fahad kenan Abbun Aunty, wato shi ina ga fa har sai an É—aura auren auntynmu sannan zai daina É—ora status É—in kayan nan da shelar zai aurar da Æ´ar shi."
Da sauri Jabir ya kalle shi, ba alamar wasa, ba tare da ya san abinda bakin shi ya so faÉ—a ba kenan ya furta" Kuma da *hoton Maama* ya É—ora ko?"
Kallon shi Aliyu yayi ya girgiza kai yace" A'a, kayan ne kawai."
Wawuyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ci gaba da abinda yake yi, Aliyu kuma sai ya zuba mishi idanu na daƙiƙu kafin shi ma ya ci gba da abinda yake yi, shi fa Aliyu har ya saki maganar zancan auren aunty, amma Jabir na nan da abun a rai, ƙwarai ya gani wai Maama za ta yi aure? Wallahi dai su Maama anji kunya? A ce an fito daga gidan Abba dattijon ƙwarai saboda wai buƙata, shine aka ce ta samu matashi mai arba'in da kaɗan, to in sha Allah... In sha Allah zai mata addu'a a cikin dare, ba mugunyar addu'a zai mata ba, amma dai gaskiya bata kyauta masa ba, ba zai so idan tayi aure ta sake fitowa wai zawarci ba, ba kuma zai mata addu'ar mijin ya dinga dukan ta ba har ta fito da ƙafafun ta, amma dai zai ce tayi ta mafarkin Abban su kawai... To kuma.
Jin kamar addu'ar da yake son yi mata a cikin daren bata dace ba yasa shi jan tsaki ya miƙe ba tare da ya taɓa komai daga cikin kayan da ya zube a teburin ba ya fita farfajiyar makarantar da niyyar shan iska dan yaji a cikin ofishin ma zafi da ƙuncin yanayi yayi yawa.
Fitar shi ke da wuya Ummu ta kira Aliyi, bayan sun gaisa take faɗa masa ya riƙe Kuwailat makaranta ya bari zasu taho tare da Eesha, ya ɗan nuna mata ba komai fa shi daga gare shi, amma sai ta nuna mishi yayi dan mahimmancin karatun ta da kuma kasancewar shi malami kawai ba Yaya ba, hakan ya sa ya ji ƙarfin guiwa tare da ƙudurin ba zai sake ma kuwailat ɗin sako-sako ba indai akan karatu ne ko zuwa makaranta.