← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 168

Sashe 31

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da haka ta shigo cikin gidan ta aje bokitin da ƙyar ta buɗe ƙofar sannan ta shiga da ruwan, tana shiga ɗaki tana sauke Uzei a goye wayar ta ta sake ɗaukar kururuwa, ta ɗauka kafin ta ɗaga kiran ta lura an kira ta ma dayawa bata ɗaga ba, ganin baban Uzei ɗin ne yasa ta yin tsaye kamar tana gaban shi cike da masifa tun bata ɗaga ba tana faɗin "Dama ko baka kirani ba zan kira ka, wallahi na gaji da masifar gidan ka."

Tana faÉ—a ta É—aga kiran a kausashe kamar wata namiji tace "Hello!"

A ɗane yake à inda yake, bare tunda Jabir ya bar gidan ya kan rasa wanda zai doka idan hannun shi na Ƙaiƙayi, cikin masifa da hargagi yace "Ke wani irin iskancin ne wai ki aje waya ana ta kiran ki b zaki ɗaga ba? Kin san kira nawa na miki? Gidan uban wa kika shiga?"

Cikin kwaratsi da hargagi ita ma wanda kwanan nan ya kunno musu kai ita ma tace "Ban sani ba, haka kawai daga É—aga kiran ka zaka rufe ni da bala'i, ba sai in ina gidan bane zan É—auki kiran ka ba?"

A wani mugun zafafe yace "Ni kike faÉ—awa haka? To ina kika tafi? Ai baki gaya min zaki fita ba."

Cikin jin haushi da tafasar zuci tace "ÆŠaukar ruwa na tafi, kuma wallahi in gaya maka ni na gaji, na gaji da wannan wahalar, Haba dan Allah, da wanne zan ji to? Aikina ko kula da gidan? Ko kuma rainon wannan yarinyar mai shegen kuka?"

Cikin takaici Mu'az yace "To yanzu ya kike so na miki? Ni zan dinga zuwa ina É—auko miki ruwan?"

A zafafe tace "Cikin biyu kayi É—aya wallahi, ko a sama min almajirin da zai dinga zuwa yana É—auko min kafin na fita aiki, ko kuma ka canza min gida mu koma inda ake samun ruwa, amma ni na gaji wallahi."

Cike da rainin wayo yace "Ƙaddara ban ɗauki ko ɗaya ba, ya zaki yi kenan?"

A take tace" Sai na bar maka gidan ka."

Cikin wofantarwa yace" Ba wannan ya sa na kira ki ba, Jabir bai dawo ba?"

Cikin wani sabon takaici tace" Bai dawo ba, da ya zo da zan maka ƙorafin ɗauko ruwa ne?"

*Dammmm*! Ya ji gaban shi ya amsa, kamar ya? Me take nufi? Ɗan nashi kenan y zama mai kawo mata ruwa kawai? Kenan bai da wani anfani bayan wannan? Hakan na nufin ba ɓatan shi ne ya dame ta ba, ita kawai ko yanzu ya dawo za ta ci gaba da saka shi ɗaukar ruwa ne kamar wani jaki? Karo na farko da ya ji yana nadamar kasancewar ta *matar shi*, karo na farko da ya ji yayi nadama akan abinda ya aikata wa ɗan shi, cikin jin zafin abinda ta faɗa yace "Kenan yanzu kin fara sanin anfanin shi? Da yana gidan baki taɓa rashin ruwa ba, har wasa kike da su dan su ƙare ki ce ya ɗebo miki, kenan yanzu kin fara gane anfanin zaman Jabir a tare da ke?"

Cikin turo baki da shashantarwa tace "Ban sani ba."

Gaskiya ya gode Allah da baya kusa, dan ba abinda zai hana shi taɓa lafiyar jikin ta, cikin gargadi yace "Za ki sani ne malama, ba dai ya bar miki gidan ba? Za ki sani wallahi."

Cikin É—aga murya tace "Dakata malam, wai lafiya kake neman É—ora min laifin da ba nawa ba? Duk abinda na ma Jabir ai a gurin ka na gani, dan haka ni kada ka sake min maganar wannan yaron, kuma zan rayu da Jabir ko babu shi."

Tana gama faɗin haka ta kashe kiran, wanda hakan ba ƙaramin ƙon masa rai yayi ba haro saida idanun shi sukayi ja kuma suka kawo ruw na takaici da baƙin ciki, amma ba komai za su haɗu, sati nawa ya rage ya dawo garin? Za Ta gane kuren ta.

*******************

Tsaye ta same shi Hajia Kaka na tambayar "To ko dai abincin ne ya zube? Na ji faÉ—uwar faranti ai a ciki."

A daƙile kawai ya amsa da "E, idan na dawo na ci." Da kulawa ta dube shi tace "Za ka dawo ɗin ne?"

Jinjina kai yayi yace "Zan dawo Hajia."

Jinjina kai tayi tace "To à dawo lafiya."

Hanyar ƙofa ya nufa Aisha ta bishi tana kallon Kaka da cewa "Mamie sai mun dawo."

Da al'ajabin da ya kusa sheƙe Hajia daga zaune ta dakata daga lashe yatsunta da ta ci abinci tace "Ke kuma fa ina zaki je ? Ban gane sai kun dawo ba?"

Dakatawa Aisha ma tayi ta juyo da mamaki tace "Abbu bai faÉ—a miki ba?"

Yana kusan fita ne ya ji wannan deba sai ya tsaya yana kallon su, lokacin Hajia ta girgiza mata kai tace "Bai gaya min komai ba, ya dai ce zai fita."

A tsanake Aisha ta juya ta kalli Sa'ad da a lokacin ya kalle ta shi ma, da kamar tuhuma ko son ƙurewa tace "Ya haka kuma Abbu?"

Dantse leɓenshi na ƙasa ya yi yana ci gaba da kallon ta kawai da tunanin hanyar da zai bi yasa ta daina kiran shi Abbu, dan za ta iya kashe mishi kasuwa a wajen ƴan mata fa, juyowa ta sake yi ta kalli Hajia tace "Hajia, Abbu ne bai da lafiya ya ce na raka shi asibiti."

Da wani irin yanayi Hajia ta miƙe tsaye tana jin hankalin ta na shirin tashi, ba wai na rashin lafiyar da ta ambata ba, hasalima ba ta yarda bai da lafiya ba dan ba alamun da ya nuna yana ko ciwon kai, zuciyar ta tsintsinkewa ta fara yi, dan kuwa ita abinda ya zo mata a rai shine kar dai Sa'ad nema yake ya kai yarinyar nan inda zai mata lalata? Dalilin da yasa take ta kaffa-kaffa da ita kenan, dan bata ga alamar buɗewar idon yarinyar ba ta wannan sigar, Shiyasa bata so a ce jikan ta sila, musamman da ta yarda yarinyar ta kai macen da za ta iya ɗaukar hankalin shi, dan tafi dayawa daga cikin matan da yake shigo musu da su gidan nan.

Saida ta kai inda Aisha take ta riƙe hannun ta jim a nata sai ta kalle shi tace "Asibiti za ka je? To ka tafi kai kaɗai mana, Allah ya tsare ya baka lafiya."

Ba tare da tunanin me Hajia ke nufi da abinda ta yi ba ya É—an sassauta murya yace "A'a Hajia, ai tare za mu tafi, ki barta Muje yanzu zamu dawo."

Girgiza mishi kai tayi tace "A'a Sa'ad, ka je kawai, gaskiya bana son ta fita a daren nan."

ÆŠan matsowa ya sake yi yana kallon Hajian yace "Hajia, wallahi ba jimawa zamuyi ba, kuma zuwan nata na da mahimmanci ne."

"Me ya kawo mahimmancin zuwan nata asibiti da kai?" Hajia ta faÉ—a tana kallon shi, É—an kallon Aisha yayi sai kuma ya kalle ta yace "Hajia, idan na dawo zan miki bayanin komai, wallahi abu ne mai mahimmanci, kuma ya shafi sanin asalin ta."

Da irin kallon hangen nesa ta bishi da kuma rashin samun sukuni, ba ta ce mi shi komai ba kuma bata saki hannun Aisha ba alamar bata gamsu ba, zubawa Hajia idanu yayi yana hango wasu abubuwa, sam ba wai bata son rabuwa da ita bane ko kuma bata so ta fita dan dare yayi, ai gaba ɗaya ma yanzu ƙarfe 08:00 tayi, sai ya ji zuciyar shi na neman raya mishi wani abu na daban a kan Hajia wanda baya so ya ji haka game da ita, dan abinda ke haɗa shi da mahaifiyar shi kenan, ya san yana neman mata kuma ba wai sun zama rayuwar shi bane da zai ce sai da su zai iya rayuwa, a'a kawai yana neman macen da yake ganin ta dace da tsari da zubin ajin shi ne kawai idan buƙatar shi ta motsa, Allah bai mi shi jarabar da komai ke iya tayar da sha'awar sa ba, illa kawai idan ya ga abu ne zahiri ko kuma yana kallo ya ga mace da namiji sun samu kusanci sosai, hakan kaɗai ke tayar da sa buƙatar.

*Ƙwarai* da gaske tafiyar da Aisha tayi bayan ta juya bayan ta ya ji tsigar jikin shi ta tashi gaba ɗaya har ya ji kamar zai fara harbin iska, amma kuma wallahi har ƙasan zuciyar shi bai ji a ran shi zai iya ko da bari ta san halin shi na neman mata ba bare har ya nuna mata hakan da kan shi, bai san me ya sa ba? Amma mutanen nan sun kasa gane yadda yake *jin kunya* da kuma kawaici ga yarinyar, dan haka ba zai iya yarda ya mata lalata ba ko da wasa ma. Raunana kallon shi yayi ga Hajia idanun shi har kamar za su kawo ruwa yace "Hajia, ke ma?"

Da sauri ta sunkuyar da kan ta ƙasa saboda sai ta ji ya bata tausayi, a hankali ta saki hannun Aisha sai kuma ta kama na shi hannun suka fita daga falon, saida suka kai farfajiyar ta saki hannun shi tana kallon fuskar shi a sanyaye tace "Sa'ad ka gane wani abu, yarinyar nan marainiya ce bata da kowa sai Allah sai kuma mu, kai ka kawo ta gidan nan da sunan taimako, mahaifiyarka ba ta karɓe ta saboda sanin halin ka, dan mahaifin ka bamu samu matsala da shi ba game da ita, ya kake gani idan nayi sake har sheɗan ya shiga tsakanin ku? Ba zan ji daɗi ba kuma ya rayuwar yarinyar za ta kasance?"
Chapter 31 · 0% Book details