Sashe 73
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin É—an taxin ya bashi amsa Nabila tayi caraf da walet É—in jami'in tana faÉ—in "Billahillazi ba zaka biya shi ba, kai dakata ka gani..."
Rigar wayar ta ta cire daga wayar, sau ga kuÉ—i a ciki wanda tayi guzuri da su, nuna ma jami'in tayi tace "Ka gani, ba wai kuÉ—in ne bani da ba, da na zo ce mishi nayi ya jira ya fito, niyya ta in amso kuÉ—in a wurin wanda ya sa ni zuwa garin nan sannan in bashi, amma É—an rainin hankali ya gaya min magana, shiyasa na ce ba zan biya ba, yayi yadda zai yi da ni dan Allah, kai ma kuma ka cire hannun ka, in ba haka ba wallahi zan kirta maka naka daidai gwargado."
Sabuwar rigima ce ta sake kaurewa a gurin, shi jami'in burin shi ya karɓi lalitar shi da ya ga ta riƙe gam, dama ƙarfin hali ne zai yi ya biya kuɗin shi dai dan su bar ƙofar gidan nan, amma a yadda wata yayi nisa ɗin nan dole yake tattala komai, ba dan ma ubannin gidan nashi masu kyauta da tausayi bane? Ai da sua ganin rayuwa, shiyasa ba ya nadamar aiki a ƙarƙashin su. Suna tsaka da wannan hayaniya har jami'i na biyu dake ƙofa ta biyu ya ga abinda ke faruwa ta ƙaramar kamara dake gurin, yayi tunanin ba lafiya ba dan haka ya fito shima, sai dai ɗaya jami'in na cikin faɗa mishi abinda ke faruwa motar Yaya Bilal ta sulalo tamkar kifi dan ko sautin ta baka cika ji ba ta dakata ƙofar gidan.
Tun daga cikin mota ya kula rigima ce a ke, amma shi saɓanin jami'an tunanin da ya yi na farko shine _Ko dai ta bugu dayawa ta rasa ina ma za'a kai ta_, _ko kuma dai bata da kuɗin taxin kua shi matuƙin ya fahimci haka shiyasa ya direta ƙofar gidan su_, dan kuwa shi dai ya ga yarinyar babu tarbiya, duk da shigar ta a wannan zamani akwai matasan da suka ɗauka ita ce wayewa, amma dai yasan duk wacce ta samu ginshiƙi mai kyau to ba zata yi haka ba, da ladabi jami'an suka gaishe shi inda ɗaya ya ɗora da "Yallaɓai, kar wannan ya dame ka, ka shiga ciki dan Allah zamu yi maganin matsalar."
Cikin taushin muryar da dattako ya dube su yace "Me yake faruwa ne?"
Kallon Nabila ta sake yi sosai da niyyar tambayar to shi ma wanene wai? Da kowa ya zo zai yi ta tambayar me ke faruwa? Su basu ga abinda ke faruwa bane? Amma kuma sai wani irin kwarjinin mutumin ya lulluɓeta, sahihiyar fuskar kamalar shi, da shigar shi sun fi ƙarfin ta masa rashin kunya, dan alamun shi basu yi kama da na wanda zai ɗauki raini daga gare ta ba, basa kama da Fahad, dan wannan duhun fata gare shi sannan yana da ƙiba, amma kuma ko da babu kama ta fuska akwai kama ta yanayi sosai tsakanin su, ƙwarai da gaske zubin shi irin na Fahad ne, yatsun ƙafa da na hannu da muryar shi, gashi yadda yayi tsaye dandanan ya dafe ƙugu da hannun dama yadda Fahad ke yi ya ƙara fito da suffar su. To ko shine Saheeb Ahlan ɗin ? Amma kuma wannan? Yadda Fahad ke faɗa mata ai ba shi kaɗai bane ya haifa, yana da yayu maza da mata fa, bai kamata a ce wannan shi kaɗai ba shine Saheeb.
Girgiza kai Yaya Bilal yayi cike da takaici sanda wani jami'in ya sanar da shi abinda ke faruwa ɗin, aljihunan shi ya laluba, sai kuma ya duba gaban rigar shi dan baya son taɓa kuɗin da ke wasu aljihunan sakamakon dawowar da yayi Fa'iza zai kai siyayya na kayan baby da matar Yayan ta ta haihu, daga can kuma zai wuce wani muhimmin uzuri shi ma, jakar biyar ba ko canji ya ciro ya miƙa ma mai taxin yace "Karɓi nan, je ka dan Allah."
Da sauri ya karɓa yace "Canjin fa?" Cikin yatsina fuska Yaya Bilal yace "Barshi kawai, tafi kai dai."
Da sauri zagaya ya ciro akwatin ta ƙarama ya aje mata gaban ta sannan ya shiga taxin shi ya tayar ya bar ƙofar gidan, cikin bala'i Nabila ke kallon taxin tana faɗin "Ka yi asara wallahi, dama irin ku kuna yin hakane dan kun san akwai masu zuciyar imani da zasu iya biyan ku har da ƙari, banza ɗan daudu mai faɗa da mata, ka yi sa'a bana dambe da ƴan daudu irin ka, da tuni wani zancen ake ba wannan ba, dan jinsina ya fi naka ƙarko."
Saida ta gama wannan zazzaga suna haÉ—a idanu da Yaya Bilal ta ga ashe ita yake kallo, cikin dattako yace mata" Shikenan ya isa, É—auki jakar ki tafi gida ki huta."
Yana faɗin haka ya juya ya koma ga motar shi, masu gadin ma da sauri kowa yayi bakin ƙofa dan buɗe mishi, madadin su ga tayi wani wurin janye da jakar ta, sai suka ga ta ja jakar tana neman shiga ta ƙaramar ƙofa, Yaya Bilal ma da ya ga haka tunanin kenan dai bala'in bai ƙare ba yayi, dan haka ya sake fitowa daga motar tare da yi ma jami'in alama kar ya buɗe babbar ƙofar kawai zai wuce ma ta ƙarama, Nabila dake ta ƙoƙarin kutsa kai ya haɗe ma fuska yace "Wai ke lafiya? Dan Allah ki bar nan wurin, ko so kike na rasa aikina ne?"
Hararan shi tayi tace "Kaga dai ina jin kunyar ka, kar kasa mu raba hali da kai yanzu."
Yaya Bila da ya ƙaraso ne yace "Ina zaki je nan ? Kinsan wani ne a gidan?"
Wani murmushi tayi tace "Allah sarki, ko dai kaine Abbun Fahad? Ina wuni Abba?"
Jin ta ambaci Fahad y sa ya haÉ—e fuska, dan zai iya ceda ya fara gano inda matsalar take, fuska a haÉ—e yace "Kin san shi ne? Me ye tsakanin ki da shi? Wacece ke?"
Tambayoyin nashi kama suka mata da na rainin hankali, amma kuma kwarjini ba ya bata damar cizga shi ko kaÉ—an, dan haka ta tausasa murya fuskar ta a gimtse tace "Sunana Nabila, ni budurwar Fahad ce, kuma wacce zai aura."
Da mamakin dama wannan ita ce Nabila ya kafeta da idanu, dan samun tabbaci ya nuna ta da yatsa yace "Ke f de Beela?"
Murmushi tayi wai da jin kunya tace "Ni ce Abba."
Wani irin murmushi yayi da shi kanshi bai san na menene ba, muskutawa yayi yana kallon ta yace "Ba ni ne Abbu ba, Yayan sa ne ni, yanzu me ya kawo ki? Na É—auka MaraÉ—i kike?"
Murmushi tayi tace "E hakane Yayan mu, wurin shi na zo ai, yana nan ne?"
Girgiza kai yayi yace "Ban sani ba, amma dai na bar shi gida yana kwana."
Ƙara jan jakar ta tayi tace "To shikenan, bari in shiga ciki."
Da azama jami'in ya sake niyyar tare ta, amma sai Yaya Bilal ya mishi alamar ya bar ta, dan idan suka ce zasu hana ta wata masifar ce kuma, gyara ta shiga idan ya so shi ya kwatanta mata a tsanake cewa Fahad ɗin nan shirin su a kan shi shine yau za su je nema mishi auren Fati, idan har kawu Abbas ya amince to fa yadda Alhaji ya ce shine a sati ɗaya za'a ɗaura musu aure, dan haka zai fi kyau ta haƙura da Fahad.
Ko motar bai waiwaya ba ya bita ciki har zuwa falon Hajia ind anan ɗakin Fahad ɗin yake, Mama Nuriyya na zaune tare da Hajia tana shafa mata maganin ciwon ƙafafu suna ƴar hirar su Yaya Bilal ya shigo Nabila na bayan shi tana ta rarako idanu tana kallon irin daular da Fahad ke ciki, amma shine ya zaɓe ta ita da ta rayu a filin *share zauna*, a ganin ta kamar basu dace ba, amma soyayya ba ta da haka ai, saï dai kuma ta tabbatar da Fahad bai da hankali tunda har ya girma a nan amma yake rayuwa da ita a wannan ƙaramin gida, duk da shima gidan ɗaya ne daga cikin mallakar mahaifin shi, amma ai ko ganin shi ba za'a yi ba idan aka ga wannan.
Mama Nuriyya da Hajia baƙuwar fuskar suka ƙurawa idanu, har suka matsa kusa da su kafin Yaya Bilal ya gaishe da Hajia Mama Nuriyya ma ta mishi sannu da zuwa, ɗorawa yayi da "Mamie ina Fahad?"
Da mamaki ta sake kallon shi, kuma sai gaban ta ya faɗi saboda tunanin ko yarinyar na da alaƙa da neman da yake ma Fahad ɗin? A tausashe tace "Fahad yana ciki, ina jin bacci yake, amma lafiya kake neman shi?"
Numfashi ya sauke tare da juyawa ya kalli Nabila sannan yace "Wannan ita ce Nabila, ita ke neman shi."
Da sauri Hajia ta tashi tsaye saboda wani irin fargaba na zulumin idan fa Alhaji ya same ta gidan nan za'a yi ɓatacciya, kallon Nabila tayi da ta sunkuyar da kai dan ta fahimci ita ce surukar ta ta, cikin taushin murya Hajia tace" Me yasa kika zo nan? Jiya jiya ne shima ya zo, shine kika biyo shi?"
Kallon ta Nabila tayi da girmamawa tace" Ba haka bane Mama, na zo ina so na gan shi, akwai wata matsala ne."
"Wace irin matsala ce da za ta sa ki biyo saurayi har gidan su?" Cewar Hajia tana kafe ta da kallon tuhuma, shiru Nabila tayi dan ba zata iya faɗa musu abinda ya kawo ta ba, dan haka Hajia ta sake haɗe fuska sosai tace "Ki gaggauta barin nan, bana so mahaifin shi ya same ki gidan nan, dan ranki zai ɓace."
Cikin ladabi da tausa murya Nabila ta dube ta tace "Kiyi haƙuri Hajia dan Allah ku bani damar ganin shi, da zaran na sanar da shi abinda ya kawo ni zan tafi, dan ban taɓa zuwa nan ba kuma ban san kowa ba."
Gaban Hajia ne ya ƙara faɗuwa, abu ɗaya ya zo mata duba da yadda ta tirje tana son ganin shi, dan hka ta kalli Nabila a gigice tace" *Ciki* ne dake yarinya?"