← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 106 OF 168

Sashe 106

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama Nuriyya da Abbu ne suka bita da kallon da har Yaya Luƙman saida ya tsare su da idanu da yanayin jin haushi, dan dama duk abin da ke faruwa ai suna lura da komai, an ɗauki minti biyu kafin Ummu ta fito Nabila a bayan ta, zunbulelen hijab ne jikin ta da ya mata kyau, kanta na ƙasa idanun ta a kan ƙafafun ta har ta ƙarasa ta zauna ƙasa kusa da ƙafafun Ummu, a taƙaice kawai ta iya furta "Ina wunin ku?"

Dukan su da fara'a suka amsa mata da "Lafiya lau Nabila, ya gida?"

Ba Ta amsa ba sai sadda kai da ta ƙara yi, hakan yasa malam Adam faɗin "Nabila, waɗannan sune shaƙiƙan saurayin ki Fahad, sun zo ne su baki haƙuri akan abinda ya faru, sannan kuma su sake jadadda neman auren ki."

Shiru ɗakin ya ɗauka saboda lokacin kowa Nabila yake kallo, amma fa ban da Mama Nuriyya da idanun ta ke kan Ummu tana kallon duk wani motsin ta, a lokacin ita tama manta me ya kawo su gidan, ƴar ta kawai take hangowa gaban ta. An ɗauki lokaci kafin Nabila cikin sanyayyar murya tace "Ba komai, ni dama ban riƙe su ba, saboda alkairi suka min, dan sanadin abinda ya faru ne na gane gaskiya, dan haka ma ni godiya zan musu."

Da jin daɗin haka suka mata godiya tare da saka mata albarka, sannan daga bisani malam Adam ya ɗora da "Sai kuma buƙatar su ta gaba, suna so su samu amincewar ki dn à ɗaura muku aure ke da Fahad, ya kika gani? Kin amince da haka?"

A hankali ta É—aga kai ta kalle shi, sai tayi murmushi a nutse ta sake sunkuyar da kan ta tace "Abba, ni dama na jima da faÉ—awa Fahad aure ni da shi bai kamace mu ba, bare kuma yanzu da aka nuna min ban dace da shi ba, Abba, istibra'i nake jira nayi, akwai dayawa masu son aurena, zan duba É—aya daga ciki wanda zai yi daidai da ajina na aura."

Tana gama faɗin haka ta miƙe tsaye ta juya da sassarfa ta koma ɗakin ta, da kallo duk suka bita har da Mama da Ummu, saida suka ga ɓacewar ta Ummu ta kalli Yaa Bilal da ta ga ya fi mata rangwamen kallo tace" Abba, kar ku damu da abinda Nabila tayi, in sha Allah zanyi magana da ita, nasan ranta ne ya ɓace na abinda ya faru, amma wannan ba damuwa bace in sha Allah."

Murmushi Yaya Bilal yayi yace" Ba komai *ƴata*, tana da gaskiya ai, zamu ƙara kwana ɗaya dan jiran jin abinda zaku tattauna."

Murmushi Ummu tayi ta sunkuyar da kai, duk haramar miƙewa sukayi, hakan yasa Mama Nuriyya kallon Abbu Mukhtar ta riƙe hannun shi tana kallon Ummu tace" K ce zamu yi maganar nan, ƴata ce fa."

A nutse ya tallabota ta tashi tsaye cikin rarrashi yana faÉ—in "Kinga nutsu, na sani Æ´ar ki ce, kinga yanzu aiken da Hajia ta mana bamu samu amincewar ya..."

Girgiza mishi kai tayi irin ba fa zata ƙara yarda da shi ba, sannan ta juya ta kalli inda Ummu take, da ƙarfi ta so fincike hannun ta da ya riƙe amma ya ƙi sakin ta, hakan yasa tayi azamar kamo hijabin Ummu ta riƙe gam har saida Ummu ta kalle ta a ɗan tsorace, cikin fitar hayyaci take kallon Ummu tana cewa "Aunty Ummu, ai kin san bamu taɓa ganin juna ba ko sai yau? Ban taɓa jin abinda nake ji a kan ki game da wani ba, ina ji a jikina muna da alaƙa, dan Allah ki saurare ni aunty Ummu, n..."

Rufe mata baki Abbu Mukhtar yayi, sannan ya shiga ƙoƙarin raba hannun ta da hijabin Ummu, cikin nutsuwa Ummu ta kalli Abbu Mukhtar ɗin tace" *Abbu*, ni ban san akan me take magana ba, dama aunty Nur bata da lafiya ne?"

Yaya Bilal ne yayi saurin faɗin" A'a, lafiyar ta ƙalau, ƴata, damuwa da ɗimuwar rashin ƴar ta ne ya mayar da ita haka, ta rasa jaririyar ƴar ta da ko kamannin ta bata gama shaidawa ba saboda son zuciya na wasu mutane da dalilin su marar tushe na son ɗaukar fansa akan yarinyar da ko iskan duniya ba ta gama karɓa a jikin ta ba, basu warke dga wannan raɗaɗin ba suka sake samu wata ƴar, amma ita ma sai tsohuwar matata ta ɗauke ta tayi nesa da ita saboda ita tafi so a ce ita ta fara haifawa ahalinmu jika ba wata ba, bayan wannan shekarun yau mun ga kamannin mahaifiyar mu a fuskar ki, wataƙila kin kula da kallon da dukan mu muke yi miki, ba na komai bane face ganin fuskar Hajia a fuskar ki har ma da murmushin ku iri ɗaya da kuma taushi da sanyin maganar ku, ba ita da take jin ta haife ki ba, ko ni da za'a bani kwangilar nemowa mahaifiyata ƴan biyun ta ko kuma nemo ƴar ƙanina da ta ɓata, to shakka babu ke ɗin nan ke zan kamo musu a matsayin wacce suke nema."

Murmushi Ummu ta sake yi ta kalli Mama Nuriyya sannan ta nuna mata inda Mama ke tsaye tace" Aunty Nur, ni kinga mahaifiyata nan, ita ce ta haife ni, nan kuma shine gidan mu kuma ahalina, shekarata talatin a duniya yanzu, sha bakwai daga ciki Mamana ce ta kula dani tun daga cikin tsummana har ta aurar da ni, daga sha takwas kuma zuwa talatin ni nake kula da kaina, dan haka a wannan rayuwar tawa yanzu dai bana buƙatar sanin su waye suka haife ni, bare ma nasan dalilin da yasa basu neme ni ba duk wannan shekarun, da izinin Allah shekarun da uka rage min ubangiji zai tsaya min ya kuma kula da lamurana."

Abbu Mukhtar da ya fi kowa fahimtar kalaman ta ya fahimci wani abu, _a yanzu ba ta buƙatar sanin su waye suka haife ta_? Me take nufi to? Hakan na nufin dai ba wannan ɗin ta haife ta? Magana fa tayi da hausa, duk da ba asali bahaushe bane amma yana gane hausa ƙwarai. Ummu da ta ci gaba da magana ne yasa shi maida hankali gare ta, Mama Nuriyya ta kalla tana cewa "Aunty Nur, ban san shekarun ki sun ruɓanya nawa ba, duk da hotunan ki da na gani ba su nuna haka ba, amma dai dana dinga kiran ki da sunan *Maama*, dan Allah mu ci gaba da zumuncin mu kamar yadda muke yi, ni kuma saina ɗauke ki uwa."

Jan majina tayi saboda hawayen da suka taho mata kan kumatu, kallon su tayi dukan su sannan tace" Allah maida ku gida lafiya."

Daga haka ta juya da sassarfa ta shige ɗakin Nabila ta rufo ƙofar, da wani irin sauri Mamie Nuriyya ta so fincikar hannun ta da niyyar ta bi bayan Ummu tana faɗin" Ka ji ko, wallahi ƴata ce, ke..."

Ta faÉ—a tana kallon Mama da tashin hankalin ta ya fi na kowa tace" Ki faÉ—a min wannan Æ´ata ce, ki gaya mata gaskiya ba ke kika haife ta ba, wall... "

Abinda ba taɓa faruwa ba duk shekarun nan ne ya faru, dan kuwa Yaya Bilal ya ga zata ɓallo musu ruwa daga zuwa neman aure, dan haka ya kama hannun ta da ƙarfi sannan ya shiga jan ta zuwa waje yana faɗin" Kuyi haƙuri dan Allah da abin da ya faru, in sha Allah zamu dawo gobe dan jin matsayar Nabila."

Da sauri Fa'iza da Abbu suka bi bayan su. Mama da ta gama hango komawar Ummu wajen iyayen ta na gaskiya, dan kuwa ba zata ci gaba da ɓoye musu ba, duk son ta da Ummu da ƙaunar da take masa saboda tsantsar ladabin ta da biyayyar ta da haƙuri dole ta rabu da ita, dole ta haƙura da Ummu dan yanzu kam ta ga zahirin ɗimuwar da mahaifiyar ta take ciki na rashin ƴa, abu ɗaya kawai da ba zata iya kare kanta gare su ba shine idan suka ga mijin Ummu, ta san Alhaji Kabir yayi jika da Ummu, kuma sun yi ƙoƙarin su akan hana ta aure shi amma ta ƙi fahimtar su, tana tsoron kar iyayen ta na asali su ɗauka ta aurar da ita gare shi ne dan ba ita ta haife ta ba, amma ba komai, ta rabu da Ummu ma bare laifin da zasu tuhume ta akan shi, za ta iya jure komai duk wahala kuwa.

*Alhamdulillah.*
15/08/2023, 20:15 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*50*
Chapter 106 · 0% Book details