Sashe 95
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ya sake gyara zama ya tausasa murya yace" Sai dai Hajia, ina ganin me zai hana ku zauna da Fahad, ku masa magana akan yarinyar da yake so, idan sun yarda zasu canza halin su sai a aura musu junan su, ko ya kika gani?"
Da sauri Fahad ya shigo yana furta" Assalama alaikum."
Hajia na ɗaga kai ta kalle shi ta sake sunkuyar da kan ta, sai Alhaji Abbas ne ya amsa, zaunawa yayi kusa da shi suna sake jajanta ma junan su da ƙarin haƙuri, saida Fahad ya kalli Hajia da ya fahimci kamar hushi take da shi tunda abun nan ya faru yace" Kawu, na ji duk abinda kuke faɗa, kawu wallahi zan auri Fatima, ina son ta yanzu, kar ka tafi da ita dan Allah kawu."
Da mamaki suka kalle shi har da Hajia ma, sai Alhaji da ya gyara zama yace" Fahad, ka san me kake faÉ—a kuwa? Fati dai da ka ce ba zaka aure ta ba, idan aka maka dole za ka gudu ka yi nesa da mu."
Girgiza kai Fahad yayi a ladabce yace" Kawu na faɗi haka a baya, amma yanzu bana so na sake ɓatawa kowa rai, wallahi zan zauna da Fatima, burin Abbu ne na ƙarshe, ku taimaka min na cika masa shi dan Allah."
Da irin kallon tuhuma Alhaji Abbas ya bishi yace" Ka tabbata?"
Da tabbaci ya jinjina kai yace" Na tabbata kawu."
Sai kuma ya sake tsare shi da idanu yace" To... Nabila fa?"
Da sauri yace" Na haƙura da ita Kawu, tun da ba kwa son ta wataƙila ba alkairi bace gare ni, ni tun ranar ma da muka zo gidan nan tare ban sake sanin ina take? Me take? Ta koma ? Ban san komai akan ta ba yanzu, kuma wallahi bana so na sani, tunda ba kwa son ta nima na haƙura da ita."
Cike da dattijantaka Alhaji Abbas yace" Fahad, kana nufin ba ka son Nabila yanzu?"
Fahad da har ga Allah ba zai iya cewa ba ya son ta ba, dan in ya faɗi haka ƙarya ya yi, da ita ya fara so, kuma ita ya fara sani ƴa mace, a hankali ya jinjina msa kai yace" Na haƙura da ita kawu."
Wani murmushi yayi mai cike da kamala da dattako sannan yace" Shikenan, tashi ka je, zan yi magana da mahaifiyarka yanzu."
A marairaice ya kalli kawun yace" Kawu Fatin fa? Za ka bar ta nan har a ɗaura mana aure, kawu na tuba wallahi, na daina duk abinda nake yi yanzu, na yi alƙawari tsakanina da mahaliccina ba zan sake aikata saɓo ba."
Kallon shi dai Alhajin yayi yana murmushi, hakan yasa Fahad ya ji a ran shi kenan bai yarda ba, dan haka ya sake riƙe ƙafar shi da rarrashi yace" Kawu Hajia ma fa hushi take dani, dan girman Allah ka ce ta yafe min, wallahi ko kula ni ba ta yi, ta tausaya min mana, ba ta ga yadda muka rabu da Abbu ba? Fita fa kawai nayi sai dawo..."
Sai kuwa hawaye a fuskar Fahad sharrrr! Har suna sauka a jikin shi, cikin kuka ya ci gaba da cewa" Dawo kawai nayi na tarar da gawar Abbuna, kullum cikin musayar yawu nake da shi, amma wallahi a raina ji nake akwai ranar da zan durƙusa na nemi afuwar sa ya yafe min sai na daina ɓata masa rai, ashe ni ina nawa tsarin ne Ubangiji ma yana na shi, sai gashi ban samu damar sake ganin shi yana numfashi ba, ko kallon ƙarshe ban ma fuskar sa ba, har yau na kasa manta safiyar da muka haɗu cin abinci na gaya masa magana da bakin nan nawa, ashe a lokacin duk..."
Haɗa kan shi yayi da guiwar Alhaji Abbas yana kuka sosai har da shasheƙa, shafa kan shi Alhaji Abbas ya dinga yi wanda ya aske ma tarin sumar nan da yake caje ta ya shafe ta da mai, cikin rarrashi Alhaji Abbas yake faɗin" Ka yi haƙuri ka daina kukan haka Fahad, mu ba wai ba ma son Nabila bane, ka gane wani abu Fahad, a lokacin da ka ce ita kake so ka aura, idan muka amince ku a haka zakuyi auren, wanda nasan niyyar da kuka gina auren a kai ba mai kyau bace, wataƙila abokanan ku ne sun yi aure? Kuma kuke so kuyi, ko kuma an fara takura muku ko saka muku ido? Dan haka kuyi tunanin ku halatta haram ɗin, ko kuma dai wata manufar can ta daban da babu Allah a cikin ta, amma Fahad ka ga da ace kun gane gaskiya ne sadidan, sannan kai da ita kuka tuba ga Allah kukayi alƙawarin ba zaku sake aikata alfasha ba, sannan ka umarci yarinyar nan da ta yi istibra'i, to da ni nan da kaina na ɗaura muku aure, ko ba komai Bilal ya gaya min cewa ka faɗa musu kai ne ka fara sanin ta ƴa mace, kuma kai kaɗai kakae mu'amala da ita, wataƙila kana da yaƙinin ko bayan auren ku zata ci gaba da kare martaba auren ka, ga kuma ciki da ya faɗa min ka mata har aka zubar, to mu kuwa me zai sa mu goya maka baya ka mata butulci? Na san duk inda take yanzu tana jin haushi da tsanar duka ahalin mu, kuma abinda aka yi ma yarinyar nan ba'a kyauta ba, dan ni ina duban matsalar ta wata fuska ce daban, shin idan a ahalin mu ne haka ta faru da wata, zamu goyi bayan a wulaƙanta ta? Ko zamu tsaya ne mu ƙwatar mata ƴancin ta?"
Sai kuma ya kalli Hajia da kan ta ke ƙasa sai dai sosai hankalin ke kan abinda yake faɗa, ɗorawa yayi da" Hajia Radiya, magana ta gaskiya ba kya kyautawa yarinyar nan ba, Fati ta gaya min abinda ya faru, kuma Alhaji Mukhtar ma ya sanar da ni komai, me ya sa? Kun manta kuna da yara mata ne? Kuma suma hayayyafa suke yi? Sannan yara irin wannan yarinyar suma haihuwar su ake ta mahaifa da kuma sa ran su zama na gari, da a ruwan sanyi kuka rabu da ita tare da yi mata nasihar da za ta ratsa ta, amma ta irin sigar da kuka tarbe ta ba, wataƙila dalilin haka ta sake shiga uwa duniya? Ko ta gane gaskiya Allah ne masani."
Kuka Fahad ke yi sosai da sosai, ɗakin shiru y ɗauka na tsayin mintuna uku, kafin daga bisani Fahad ya tsagaita da kukan yace "Kawu, wallahi ban kawo Nabila gidan nan ba saida muka yi alƙawarin mun tuba ba zamu sake ba, daga wannan ranar na ce ta fara istibra'i dan aure zamuyi, amma basu fahimce mu ba, ba ma wanda ya zauna ya tambaye mu ko ya ji menene damuwar mu, ni kuma har ga Allah ina son ta ne da aure tun farkon haɗuwar mu, sheɗaan ne kawai da son zuciya ya rinjaye mu da son rayuwar holewa, amma da na ga abun yayi yawa na ce mata aure nake so kuma ta amince, duk da ta so nuna min kamar bamu dace ba saboda rayuwar da muka yi, amma na ce mata mu bar wa Allah komai, zai dubi kyakyawar niyyar mu ya tallafa mana."
Sai kuma yasa hannu yana share hawaye tare da faÉ—in" Ni tsorona kar ta je gidan nan tayi ta shan duk abinda ya tarbi gaban ta, ga Nabila da idan tayi zuciya ba ta cin abinci, ina tsoron yunwa ta kamata..."
Yadda ya ƙarashe maganar yana rushewa da kuka ya sa Alhaji Abbas dafa bayan shi yace" Fahad, daina kukan hakanan kar kan ka ya fara ciwo, yanzu tashi ka je ɗakin ka ka kwanta ka huta, in sha Allah komai zai yi daidai."
Jinjina kai yayi da ƙyar ya tashi tsaye zai tafi sai kuma ya dakata ya kalli Alhaji yace" Kawu, ka bata haƙuri ya yafe min, bana so na sake rasa wani daga cikin su alhalin suna hushi da ni, Dan Allah ka sa baki."
Jinjina masa kai yayi yace" Kar ka damu Fahad, in sha Allah Hajia za ta yafe maka har abada, je ka kwanta."
Wucexa yayi a sanye haro ya shige ɗakin shi, sai lokacin sautin kukan Hajia Radiya ya fito fili, cikin nutsuwa Alhaji Abbas yace" Hajia, haƙuri zakuyi ku nemi iyayen yarinyar nan sannan ku nemawa Fahad auren ta, tunda har sun ɗauri niyyar gyarawa, mune muka lalata komai."
Da sauri ta dakata daga share hawaye ta kalle shi tace" Auren ta? Nabilar?"
Da tabbaci ya bata amsa da" E, baki ga yadda yake magana akan ta bane? Ya yarda zai auri Fati ne dan kawai ya muku biyayyar da ya kasa yi muku a baya? Amma har yanzu yarinyar nan ce a ran shi, kina gani fa ya kasa cewa baya son ta, sai dai ya ce ya haƙura kawai, gashi ya damu da son sanin halin da take ciki, amma da fari ce mana yayi ba ya so ma ya san me ke faruwa da ita, Hajia Radiya, ina tsoron wata ƙaƙƙarfar alaƙar da kan iya zuwa da tsananin rabo ce ta zo da guguwar da ta ɗauke Alhaji Saheeb, wanda idan muka ce kokawa zamu ci gaba da yi bamu san rayuka nawa za ta ɗauka ba, dan Allah ki bar shi ya aure ta, ki mishi addu'a Allah ya sa haka shi ya fi zama alkairi, ina ji a jikina zaman su zai kafa tarihin da ba'a cika rubutawa ba a duniya, dan Allah?"
Shiru tayi na sakanni, nazarin ta bai wuce yanzu nan sai ya auri yarinyar nan? Alhaji ai ya ce ba ya son ta, kuma idan aka ga Fahad ya auri Nabila sai dai idan *bayan ran shi*, to ko dai da gaske ne? Hakan na nufin wataƙila akwai aure a tsakanin nasu har ma da rabo? Shi ya sa ma furucin Alhaji ya tafi da shi makwancin shi? Y Allah! A nutse ta kalli Alhaji ta jinjina kai tace "Na amince, ka yi abinda ya dace kawai."
Take murmushi ya bayyana a fuskar shi yace "Ma sha Allah, naji daɗin jin haka gaskiya, Allah ya tabbatar mana da alkairi, Alhaji kuma Allah ya jiƙanshi da rahama."