← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 168

Sashe 112

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sassauta murya sosai Aisha tayi hawaye na zarya a kumatun ta tace" Saida mutane suka fara kiran mahaifiyar mu da mahaukaciya, saboda ɓatan mu ya zautar da tunanin ta, mahaifin mu kuma yana fama da hawan jini, idan kika gan su shi da kawu Bilal, zaki ɗauka Abbu shine gaba da kawu saboda tsufan da yayi gaggawar cimma sa saboda damuwa da zulumi, amma kuma bayan kawu Bilal har aunty Murjanatu ta shiga tsakanin su, Ummu ko na sakan ɗaya ne ki rumgumi jikin iyayen ki, ta nan zaki fahimci gaskiyar da ake faɗa miki, dan soyayyar wacce ta ɗauki cikin ka wata tara sannan ka fara shan nonon ta, da wacce ta shayar da kai daga baya bata taɓa zama ɗaya, saboda wannan *mahaifar*, wacce sunan ta ma a larabce *tausayi* yake nufi, kuma wallahi haihuwa ba wasa bace, kin yi ta kin san me ke ji, ki roƙi Maman ki ta faɗa miki gaskiya, in har ba wata manufa ce akan ki ba na ƙin son ki san iyayen ki, to za ta sanar dake ba ita t..."

A mugun zafafe Ummu ta nunowa Aisha yatsa tana zaro idanu da faÉ—in" Kar ki kuskura, kar ki ce zaki fara faÉ—awa mahaifiyata maganar banza, idan..."

Mama da ta shigo falo dan karyawa ne ta ji wannan tashin muryoyin, hakan yasa ta aje kwanon hannun ta da sauri ta shigo ɗakin, abinda ta riska ne yasa ta gaggawar yi ma Ummu tsawa, shiru duk sukayi suna kallon ta har ta ƙaraso, tana zuwa ta kalli Aisha a nutse tace "Dan Allah, zan iya ganin iyayen ki?"

Murmushi Aisha tayi tace "Me zai hana Mama, zaku iya."

Jinjina kai tayi tace "Muje ki kaini ida suke dan Allah."

Da sauri Ummu tace "Mama, me zaki je ki musu?"

Kallon ta tayi ta nunota da yatsa tace "Kar na kula jin bakin ki a maganar nan."

Tana gama faɗa ta juya zata fita, hakan yasa Aisha kallon Ummu sannan ta wuce ta ɗauki gyalen ya da wayat ta har da jakar ta sannan ta bi bayan Mama, saida suka kai ƙofa Mama ta juyo ta kalli Ummu tace "Ki saka hijabin ki, tare zamu tafi."

Kallon Maman tayi sosai, sai kawai ta jinjina kai tace "To Mama."

Juyawa tayi ita ma ta fara neman hijabi, tana É—aukowa ta fito ta samu har sun fita tsakar gida Mama na faÉ—awa Kuwailat ta É—auko hijabi ita ma zasu fita sai a rufe gidan, hakan kuwa aka yi tsaf suka tafi tare babu kowa gidan.

Babu mai hira a motar dan kowa da abinda yake saƙawa a ran shi, haka suka isa masaukin baƙin, sai dai tun daga bakin ƙofa mai gadin wurin ya leƙo ta madubi yna faɗa ma Aisha "Barka da zuwa Hajia, yanzun nan ko su Alhaji suka fita."

Da mamaki Aisha tana kallon shi tace "Suka fita kamar ya ya? Ina suka je su kuma?"

A taƙaice ya bata amsa da "Asibiti."

Dukan su na motar saida duka kalle shi har da Kuwailat dake maƙale a kafadar Ummu, Aisha ce tayi gaggawqr faɗin "Asibiti? Me ya faru? Wa ye ba lafiya cikin su?"

A nutse yace "Wallahi dai Hajia na ga sun tallabo an saka ta mota sun fita da ita, farar matar nan mai É—an tsayi..."

Bai ƙarasa ba Aisha ta furta "Mamie, inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un !"

Sai kuma ta kalle shi a gigice tace "Wane asibiti suka kaita?"

Da kulawa yace "E to, ban sani ba gaskiya, amma dai tare da Alhaji Sa'ad suka tafi."

Jin haka da sauri ta ciro wayar ta daga jaka ta fara kiran lambar Sa'ad É—in, jim kaÉ—an ya É—aga hakan yasa ta gyara zama tace "Abbuna, ina Mamie ? Ya jikin nata? Wace asibiti kuka je?"

Cikin nutsuwa daga ɓangaren Sa'ad yace "Ki fara kwantar da hankalin ki, babu abinda ya samu Maman mu, jinin ta ya hau kawai, amma Alhamdulillah yanzu haka an mata allurar bacci tana hutawa."

Nauyayyar ajiyar zuciya ya sauke, duk da ya san zata iya faɗa masa haka dan ta kwantar da hankalin ta, amma dai ta san da sauƙi ɗin, dan haka a nutse tace" Wane asibiti ne? Gani nan zuwa."

A nutse yace" Hanyar da muka biyo dake da zamu taho, akwai alllon shaidar asibitin na nan da kin karya kwana."

Tuni ma Aisha ta kama hanya dan ta gane asibitin. Tunda aka ambaci asibiti gaban Ummu ya yanke ya faɗi sosai, hatta tsigar jikin ta duk saida ta tashi tana jin ba daɗi sosai, amma dai haka tayi shiru ba ta ko nuna abinda ke ran ta ba, tana jin Mama dake gaba tana ta jajanta abun da Aisha ita kuma tana ƙara faɗa musu ai tun jiyan nan dma kuka kawai take ta ƙi cin komai, hakan yasa Mama sake ɗaurar niyyar yau sai ta sada Umm da iyayen ta, dan gaskiya ta tausaya musu sosai da sosai.

Basu sha wahalar samun ɗakin da aka kwantar da ita ba, ƙwarai da gaske Abbu yayi mamakin ganin Aisha tare da Ummu, gaisawa sukayi kafin Mama ta kalli Abbu a raunane tana riƙo hannun Ummu tace "Alhaji, dan Allah ku gafarce ni abisa ɓoye muku wani babban al'amari da nayi shekaru tara da suka wuce, na gane kuskurena daga sa'ilin da naga irin kiɗimewa da tashin hankali da mahaifiyar..."

Sai kuma ta kalli Ummu da ita ma take kallon ta tana son ta ji me zata aikata tace" Ummu, da gaske *Ummu Kulsum Æ´ar ku ce*, Æ´ar ku ce halak malak."

Faɗin irin yanayin da dukan su suka tsinci kawunan su ma ɓata lokaci ne, farin ciki mai saka kuka, jin daɗi marar misaltuwa, da kuma mamakin ya haka ta faru? Ummu ce kawai takamaiman yanayin ta bai bayyana ba, ita dai ta kalli Mama da ke ci gba da ba wa Abbu haƙuri, sai kuma ta kalli Abbu da yake kallon ita ma Ummu.

Ta jima haka kafin wasu zafafen hawaye su sauka kan kumcin ta, kallon Mma tayi dake kuka sosai tana sakin hannun Ummu da niyyar fita ta bar asibitin, da sauri Ummu ta riƙota suka kalli juna, cikin dakusashiyar murya Ummu tace "Me yasa Mama? Kin fa san halin da nake ciki, yanzu ke kawai nake da buƙata, ina so ki rarrashe ni da kan ki ne Mama, sai kuma ki damƙani hannun waɗanda basu damu dani ba."

Girgiza mata kai Mama tayi tana kuka tace "Ummu, ta ya wai kike wannan banzan tunanin? Iyayen ki suna son ki fiye da komai, kuma sun damu dake sosai Ummu, ki gane mana, har yaushe zaki bari mahaifiyar ki ta ci gaba da kukan rashin ki? Kina neman rahama kuwa?"

Wasu sababbin hawaye ne suka gangaro mata, hakan yasa cike da tausayin kan ta ta faɗa jikin Mma tana rera wani sabon kukan, daddaɓata Mama ta dinga yi a tausashe tana faɗin" Kiyi haƙuri mana Ummu, kin san bana son kukan ki ko? Ki daina mana, ki je sau ɗaya ki rumgumi iyayen ki, ina tabbatar miki zasu rarrashe ki fiye dani."

A hankali Mama ta ɓamɓare Ummi daga jikin ta, juyawa tayi za ta fita Aisha ta riƙe hannun ta tana girgiza kai tace" Mama, kin bami abu mafi daraja, bai kamata ki tafi haka ba."

Kuwailat da ta ga Mama na kuka sosai ne tayi saurin matsawa kusan ta suka rumgumi juna, hakan ya sa Aisha fuskantar Ummu dake share hawaye tayi murmushi tace" Aunty, kinga maganata ko? Na faÉ—a miki ke Æ´ar uwata ce."

Sai kawai ta sake fashexa da kuka ta jawo Aisha jikin ta suka rumgumi juna sosai suna kukan farin ciki dukan su. Muryar Abbu ce ta daki kunnuwan su ya furta" *Kuwailat*."

Kasancewar Ummu ta ji Aisha ta kira ta da sunan ɗazu, hakan yasa ta ɗago kan ta da sauri haka ma Aisha, sai Kuwailat ƙarama da ita ma tayi saurin juyowa ta kalle shi, a hankali Abbu ya buɗe hannayen shi alamar ta zo gare shi, nauyi da kunya ya sa Ummu sunkuyar da kan ta, dan gaskiya a dai al'adar malal bahaushe bata taɓa gani ido da ido ba, sannan tana ganin ai tayi girman da ya kamata ma ace ta wuce haka.

Cike da zumuÉ—i Abbu ya sake cewa "Zo mana, zo *Æ´ata*."

Da bata yi niyyar zuwa ba saboda jin abun wani iri, amma sunan ƴata da ya faɗa yasa Ummu har da takawa a guje tana rushewa da sabon kuka kawai ta shige ƙrjin mahaifin ta luffff tana ci gaba da kuka. Wani irin sanyi ne mai kama da an cire maka wani dutsin dake cikin zuciyar ka ta ji, haka saida jikin ta ya amsa sakamakon haka, wani irin ƙamshi ne take ji a jikin mahaifin ta wanda duk da akwai na turare amma tana jin wani ƙamshi na daban wanda zata iya cewa kamar alaƙa ce ta janyo take jin hakan, hakan yasa ta gyara tsayuwa ta sake yin ruffff tana ƙara ƙamƙamo bayan mahaifin nata da shima dole tasa yake wasu irin hawaye masu tsada na tsantsar farin ciki, abu ɗaya kawai take jin yana faɗa "*Allah na gode maka, Allah na gode maka, ko yanzu ka ɗauki rayuwata na gode maka, tunda ka nuna min wannan ranar da na sake rumgume jaririyar ƴata da ta ɓata shekara talatin..."

Duk da ya kai ƙarshe, amma da sauri Ummu ta ɗago tana girgiza kai tace "A'a, a'a *Abbu*, ba zaka tafi yanzu ba, gwara a ce ni na tafi."

Sake danna kan ta yayi a ƙrjin ji yana girgiza mata kai, ba wanda bai musu hawaye ba a wurin har Sa'ad ma, sai Yaya Bilal da ya share hawaye yace "Ni ba za'a rumgume ni ba?"

ÆŠagowa Ummu tayi, hakan yasa tayi dariya saboda kallon fuskar Yaya Bilal da har da turo baki, a hankali ta taka gaban shi, irin rumgumar nan ce sukayi ta gefen jiki kawai tare da dafa kan ta yace "Allah ya miki albarka, mun jima muna kewar ki Kuwailat."

Sakin ta yayi ta ƙarasa wajen aunty Fa'iza nan ma suka rumgume junan su, kafin Aisha ta nuna mata Sa'ad tace "Wannan shine Abbu, mijin ƙanwar ki."
Chapter 112 · 0% Book details