Sashe 167
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kawai yayi dariya ya shiga ɗakin shi dan ya jira dawowar ta. Ta jima kafin ta dawo gidan jiki a sanyaye kuma a eikice ta shiga ɗakin nashi, ƙasa ta jefar da jakar ta tana faɗin "Shikenan, Jabir ka tona ma zaman da muke cikin ɗaki asiri, wallahi ciki ne da ni, wai likita har da min faɗa kamar uwata wai ciki wata biyar amma ban sani ba dan hauka...han."
Ƙwafa tayi tana zama kan gadon, zaune yayi yna kallon ta da irin basarwa yace "Ciki fa Maama? Ke gare ki wai? Subhanallah."
Kallon shi tayi tace "Wallahi ka sani Jabir, shiru kawai ka min dan dama kana so ka ga bayana."
Sai kuma tayi kamar zata fashe da kuka tace "Yanzu fisabililahi ya kake so nayi? Ranar da mukayi waya Abbu Bilal ya ce min zai zo fa ya aiwatar da shirin sa a kanmu, sannan su Mammie da Hajia da Eesha, kai har ma da Nabila da uncle Fahad iskanci suke min wallahi, kai har ma fa aunty, sai ka ji ta ce idan Eesha ta haihu za'ayi kasa da kaza, duk burin ta akan hiahuwar Eesha ne, tunda ni ai Yayar ka ce ba abinda kake min, ni kuma sai nace e mana."
Kamota Jabir yayi jikin shi ya matse ta tsam cikin muryar dariya yana ɗan jijjigata da daddaɓa bayan ta yace" Shikenan Maamana, ba dai cikina ne ba, ni ai ban san ya shiga ba dan bai yi shawara da ni ba, kuma kinga ai kin shaideni da riƙon alƙawari, amma ki min alfarma ɗaya, ina kewar mahaifiya, ina ji ina ma na san kamannin ta? A ƙalla da zan dinga tuna fuskar ta ko na ga mai kama da ita, hakan yasa a duniya buri ɗaya ya rage min yanzu bayan samun ki, wannan burin kuma shine *UMMU KULSUM* ta haifa min *ɗana* daga tsatson ta, na roƙe ki Maama, ki barshi ya zo duniya ba tare da tsangwamar ki ko nuna masa ƙiyayya ba, ina tabbatar miki daga shi shikenan."
ÆŠaga kanta tayi ta kalle shi da irin tuhuma tace" Da gaske?"
Jinjina mata kai yayi yace" In sha Allah."
Laɓe baki tayi cike da tausaya mishi, ai ya gama da ita kuma, yo me ye a ciki wai? Dan ta haifa masa ɗa ɗaya dai ƙwallin ƙwal? Ba komai ai dan gaban idanun ta wanzami ya kai ziyara gidan su, kai ita ma lokacin ba wayo ne da ita ba fa, dan haka zata haifo guda ɗayan mana, Alhaji ma ba gashi ta bashi ɗaya ba da yake tuna ta da ita? Shi ma zata masa hakan kawai dan ai ta fi *son sa* gaskiya akan Alhaji, e ta faɗa kam, wanda zasu yada mata magana kuma ai idan ta musu shiru ta bisu da idanu ta gama da su kawai, dan haka za ta sake shiga ɗakin yaƙin mata in sha Allah ita ma nan da wata huɗu.
*Kwana biyu* da faruwar haka Aisha ta haihu, nan fa aka shiga hidimar suna inda mutanen Agadez suka taho biki, Ummu na ta kai da kawo babu zama, gashi wasu baƙin ma a gidan ta suka sauka har da aunty Mardiyya da ta ce ita bata surukuntaka da Jabir dan dama ɗan ta ne, Mama Nuriyya ce dai bata leƙo gidan ba ita a dole kunyar zuwa gidan babbar ƴarta take ji, sai bayan suna ne suna shirye shiryen komawa sun dawo daga kasuwa da yamma kwatsam suka biyo ba tare da Ummu ta sani ba.
Hakan ya sa Jabir suka samu a farfajiya yana wanke kayan su shi da Ummu ita kuma tana ɓarar dankalin turawa suna hira abun su, gaisawa sukayi da Jabir sosai inda ya shiga ciki dan ya canza kayan jikin shi ya basu wuri, hakan yasa Mama cire takalmen ta ta nufo Ummu dake tsaye da shi tana faɗin "Na shiga uku ni Nuriyya, aunty dama bawa kika mayar da mijin naki? Dan kawai kin girme shi da wasu ƴan shekaru sai kike saka shi wanki."
Da gudu Ummu tayi bayan aunty Nuriyya da suka tafi kasuwa tare tana faÉ—in "Mama ki gaya mata wallahi ba haka bane, aunty dakata kiji in gaya miki gaskiya."
Dakatawar Mama tayi tace "Ina jin ki to munafuka."
Ba tare da ta fito daga bayan Mardiyya ba tace "Aunty, bari ya fito ki tambaye shi kiji, Billahil'azim ban taɓa saka shi da kaina ba, kinsan ai shi mai koyi da Annabi ne."
Hararan ta Maman tayi amma ba dan ta yarda da abinda ta faɗa ba, haka suka shiga ciki suka zauna Jabir kuma ya fita. Wannan zuwan ne da sukayi Ummu ke jin labarin wai Alhaji Abbas dai ƙanin margayi Alhaji ya tura su nemo masa auren Mama uwar marayu, wani irin farin ciki ne ya lulluɓe ta har da hawaye da kuma zumiɗin son jin amsar da Maman ta bayar, sun faɗa mata ta ce za ta yi nazari tunda gaskiya har da matar shi ma ta amince kuma tare suka je, wannan kam halayen ta ne na gari ke bibiyar ta.
*BAYAN WANI LOKACI*
Tun bayan barin ta gidan yau ne na farko d ta shigo shi, shima ba dan dalilin rasuwar Hajia babba ba da bata zo ba, tare da Kuwailat suka zo wacce yanzu ta zama ƴar gidan tun bayan haihuwar *Abubakar Siddiƙ*, Kuwailat ke goye da shi suka shiga duka ɓangaren matan ta musu gaisuwa, Hajia Atika da har yanzu bata daina ƙiyayya da Ummu ba kuma ita kan ta bata san dalili ko mafarin ƙiyayyar ba, ƙwarai ta ƙara jin hasada duba da yadda Ummu ta koma, tana baƙin cikin ta auri mijin su, da ta fara zawarci ta ɗauka zata samu wani dattijon nan, amma sai ta samu yaron da a yanzu ita ce zata tsufa ta barshi idan bata kula da kan ta ba, gashi alamu sun nuna hankalin ta kwance yake saboda wata ƙiba da tayi mai tsari da kyau, ga hasken ta da ya ƙara bayyana har wani yelow yelow tayi, ko da yake ai tana ji ga Zeinab irin ci gaban da take samu da dukiyar da ta mallaka yanzu, dan haka kawai ta yarda Ummu ta tsere mata nesa ba kusa ba.
Saddiƙ kan shi da ta gani bayan Kuwailat ta sauke shi saida ta ƙura masa idanu, ba ta san ma cikin kyawawan iyayen nashi da wa yayi kama ba, Jabir ne? Ko kuma Ummun ce? Abinda zata iya cewa a taƙaice kawai shine ɗan kyakyawa ne gashi cikin ƙoshin lafiyar shi.
Anan Ummu suka samu Mama ita ma bata jima da zuwa ba, dama kuma tun bayan auren ta da Alhaji Abbas bai ɗaukta daga nan garin ba saboda ya ga nan ta saba nan take da ahali, dan haka shine ke zuwa duk lokaci bayan lokaci, yanzu haka Mama rayuwa take cikin ƴanci da farin ciki saboda tana ƙarƙashin inuwar aure, sannan tana tsananin farin ciki da godewa ubangiji kan ni'imomin da ya mata a rayuwa da ba zataiya misalta su ba, dan yanzu haka Mama cike ne da ita na wasu ƙananan watanni, wanda har Allah Allah take ayi bikin su Kuwailat da aka saka rana kafin cikin ta ya fito fili.
*Abubuwa* ne suka tari suka ma Ummu da Jabir yawa na wannan hidima, dan aure uku Alhaji Kabir ya haɗa zai yi, na farko shine na Aliyu da amaryar sa *Ni'imatullah* wacce ɗalibar sa ce, sai kuma auren Khamis da amaryar sa shima wacce ƴa ce ga ɗan uwan Hajia Radiya, lokacin bikin Fahad da suka kai amarya suka haɗu har soyayyar su ta ƙullu wato *Zinnira*, sai kuma auren Kuwailat da angon ta balarabe *Mansur* wanda sai bayan komawar shi yake sanar da Aliyi shi fa yana son ƴar maaman Jabir.
Jabir ya zama uba ne ga amarya Kuwailat, dan duk wani abu da zai haɗa Ummu da Alhaji Kabir magana kan wannan hidima, shi suke sakawa a tsakani saboda Ummu ta ƙi yarda suyi magana, ba dan bata so ba ko dan tana riƙe da shi, kawai dai bat son doguwar mu'amula na haɗa su, gaisawa sukan yi idan sun haɗu, amma bayan haka ba komai, to ita ma, kasancewar ta na uwar amarya wannan hidimar ce ta sako ta gaba, sai kuma Jabir dake ƙoƙarin ramawa kura aniyar ta, wato irin hidima da faɗi tashin da Aliyu yayi lokacin nashi auren, ga kuma Mansur da ya masa tattaki ya zo har ƙasar nan saboda ɗaura auren shi kawai, haka kuma ga Khamis da shi ma ba baya ba wajen bada tashi gudummuwar, dan haka da kwanakin sukaa ƙarota ya zama kamar mahaukaci, ba dan Maaman shi dake saita shi a hanya ba, musamman cikin sa da bata wasa da shi, dan tasan da ya fara jin yunwa zai ruɗu ne ya fara masifa da mutane har ma da angayen.
Anyi biki lafiya amare sun tare É—akin mazajen su, inda amarya Kuwailat kuma tare wajen Maman ta sai bayan sati É—aya zasu tafi, Alhamdulillah dai an gama hidimar lafiya kuma kowa hankalin sa ya kwanta.
*Washe Gari 07:18*
*Cikin* wata nutsatsiyar shigar jallabiya da ihramin ta ya fito yana ɗaura agogon hannun shi, Ummu na ganin shi tayi saurin miƙawa Kuwailat kofin haɗe sassaken ɓaure da ta tsiyaya mata tare da miƙewa, karɓa Kuwailat tayi ita ma ta miƙe ɗin tana rusunawa da kallon Jabir tace " *Yaya* fita zakayi?"
A nutse Jabir shima dake kallon ta yace "Fita zanyi *autar Abba*, malam ya tafi jinyar mahaifin shi a Maroc, ni zan fara gabatar da karatu yau."
Da wani sahihin murmushi mai kama da na maman ta Ummu tace "Kai, amma Yaya naji daÉ—i sosai, Allah ya bada sa'a."
Da jin daÉ—i ya amsa mata da "Ameen."
Har ta wuce sai kuma yace "Ya, kunyi waya da mijin naki?"
Da kunya Kuwailat ta amsa da "Yaya ai kiran shi ke tashina a bacci da asuba."
Da sauri ta shige cikin É—akin ta, a nutse Jabir ya maida duban shi kan SaddiÆ™ dake bacci kan kujera, sai kuma ya kalli Ummu dake bin shi da wani kallo kamar n tuhuma, da alamar tambaya da idanu ya mata alamar" Ya ya?"