← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 168

Sashe 137

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da irin ka tuno abun nan Abbu yace" Kai! Alhai wai ban sanar da kai abinda ya faru ba ko? Ai tuni aka bar magnar auren ta da Larwan, wallahi wani abu ne ya faru da ya ɗaga mana hankali dole muka janye maganar, matar sa muka kula kamar ba za'a zauna lafiya da ita ba, yanzu haka tabo na nan a hannun Nabila wanda matar ta yanke ta da wuƙa kuma har cikin gidan nan, hakan yasa na ga indai har za ta iya aikata wannan ɗanyan aiki a gidan su Ummu, to ina ga idan an kai ta gidan ta? Ya kenan? Kashe ta zatayi da gaske kamar yadda ta ci alwashi?"

Cikin tashin hankali Alhaji ya dinga jajata lamarin, Abbu kuma kawai faÉ—a masa yake" Ba komai wallahi, ameen nagode da addu'a, ai dake ma za'a É—aura auren a ranar da aka saka in sha Allah, wani abokin Fahad ne Jibril wallahi ya nuna sha'awar auren nata, kuma duk sharuÉ—É—an da ta gindaya masa ya amince, sai dai mu musu fatan Allah ya sanya alkairi."

Da jin daÉ—in haka Alhaji yace" Ma sha Allah, Allah ya sanya alkairi, Allah ya tabbatar ya nuna mana wannan ranar."

Amsawa yayi da ameen kafin su ɗan taɓa hirar kasuwa, dama suna jimawa suna waya in dai suna yi, to yanzu ma haka sun ɗan jima suna wayar kafin suyi sallama da juna kowa ya shiga harkar gaban shi.

*******************

Fahad da bai san me ya faru ba shi dai Jibril ya ce ya bashi lambar yaron nan Jabir, ganin Jabir na harkar kayan maza ma'ana sutura da takalmi irin da agogo har da sauran kayan jiki dai na maza, sannan kuma sun haɗe a bikin shi sai ya ɗauka ai sun zama ɗaya yanzu dukan su, dan haka kawai ya tura mishi bai ce komai ba. Jibril kuma cike da alfahari da son ƙular da Jabir musamman ma da aka faɗa mishi ai ba ɗan tsohon mijin ta bane, kawai dai yaron shi ne da yake ɗauka kamar ɗa shima, yana kira Jabir ya ɗaga kasancewar lambar shi da har a gaban shagon shi ita ce ya saka ake neman shi da ita, dan haka ba ya ƙin ɗaga kira in ai a layin ne yayi sallama.

Bai amsa sallamar shi ba, sai magana da ya fara a gadarance yace "Ni ne, Jibril, zuwa yanzu na san kasan da saura kwana shida a ɗaura aurena da *Maaman ka*, na faɗa maka dama kada ka ja dani, idan na so abu ina samun shi ne ta ko wane hali, Jabir ka ke ko? Zan auri Ummu sannan nayi yadda nake so da ita, baka isa ka hana ni ba kamar yadda ba wanda ya isa ya hana ni aikata abinda nayi niyyar aikata mata bayan buƙatata ta biya a kan ta, ina maka murna da maaman ka za ta yi aure."

Yanke kiran yayi ya bar Jabir cikin tashin hankali, kifa kan shi yayi a teburin ofishin Aliyu dake ya fara yi wa É—alibai darasi akan aure, duba da duka karatun da ake musu babu wanda zai koyawa mata da maza yadda ake zaman aure, hakan yasa Jabir ba wa Aliyu shawara a ware mata daban ana musu koya musu yadda zasu zauna da mazan su, haka sula mazan ana koya musu yadda zasu zauna da matan, to Jabir ne ke gabatar da karatun duk ranar litinin da safe.

Tunda ya kifa kan shi bai ɗago ba saboda... Abun ya ma wuce kwatance, shi dai ya ji kawai duniyar tana masa zafi, wanda hakan ya sa shi ba tare da ya ɗago kai ba kawai ya lalubo wani abu dake kusan shi bai ma san menene ba kawai ya buga shi a teburin da ƙarfi.

Wannan ƙarar ta sa Aliyu dake ƙofar ofishin yana magana da wata ɗaliba kamar yadda ba ya yarda suna shigo masa ofishi in dai mai aure ce yasa shi kallon matashiyar dake rufe ruf cikin shiga ta kamala da daraja yace "Ina zuwa malama?"

Da sauri ya shigo ajin yana kai duban shi kan kujerar shi inda ya san anan Jabir ɗin ke zaune, ai ko anan yake ya haɗa kan shi da teburi, da sassarfa ya ƙarasa kusa da shi yana kiran "Jabir."

Shiru bai ɗago ba kuma bai amsa ba, saida ya ƙara matsowa daf da shi sannan ya sa hannu ya dafa kafaɗar shi ya sake kiran "Jabir, lafiya? Kan ka ne ke ciwo? Me ya faru?"

Har lokacin shiru yayi bai kula shi ba, dan haka Aliyu ya shiga waige waige har saida ya hango kwalin allin da Jabir ya tarwatsa mishi, sake duban shi yayi yace "Jabir, me yake damun ka? Idan baka da lafiya ne kayi min magana."

Wani numfashi numfashi ya ji ya sauke mai kama da na mai kuka, hakan ya É—aga hankali Aliyu ya ce "Subhanallah! Kaga tunda ba zaka min magana ba, bari na kira Abba (Abban Jabir) na sanar da shi, idan baka da lafiya ne sai ya zo muje asibiti."

Wayar shi dake kan teburin gefen hannun Jabir ya zura hannu zai ɗauka, ram Jabir ya riƙr hannun shi a hankali ya ɗaga kan ya kalli fuskar Aliyu yna sauke numfashi, idanun shi Aliyu da ya kalla saida gaban shi ya faɗi, sunyi jajir jajir da su ga kuma ruwa da suka cika su alamar kuka yake yi ko kuma yake shirin yi, cikin kulawa Aliyu ya rusuna a tausashe yace "Jabir, me ya faru? Wa ya rasu? Dan Allah faɗa min?"

Sakin hannun Aliyu yayi ya kawar da kai, numfashi ya sake saukewa sannan ya sake juyawa ya kalli Aliyun, cikin yanayin da shi kan shi zai iya kiran shi da baƙo, cikin tashin hankalin da bai yake mamakin yadda zuciyar shi ta ƙ bashi lafiya game da lamarin Maaman shi, murya a tausashe tamkar idan yana nasiha ga bayin Allah, ga kuma muryar na rawa rawa wanda hakan yasa maganar tashi kan ta da yake yi sai take bada wani irin kalar gagarumin tausayin wanda yake furtawa yake faɗa ma Aliyu "Me yasa Aliyu? Me ye na gaggawar? Me ya kawo ujila a cikin lamarin? Me ye na dole sai tayi aure da gaggawa? A matse take da ɗa namiji ne? Idan auren ya zama dole yanzu, me yasa ba zata aje hankalin ta tayi zaɓi na ƙwarai ba? Ta fito daga gidan Abban mu dattijon ƙwarai, sai kawai ta ɓige da auren yaron da wani abu na jikin ta ne yake so, wallahi Aliyu *sirrin ta yake so ya gani dan kawai ya tozarta ni*, me yasa? Me ya sa Maama ke ta yin wasu abubuwa kamar bata da hankali? Idan na mata magana sai ta ce ni ba tsaranta bane, amma kuma *wauta* take min kowa na gani..."

Hawaye ne suka gangaro mishi a kumatu har suka sauka kan lallausan gemun shin, shiru yayi na sakanni tare da kawar da kan shi kaɗan, sai kuma ya miƙe da sauri yana sake kallon Aliyu ya ɗan kausasa fuskar shi yace" Wallahi ba zata aure shi ba, ko zan mutu, haka ita ma ko zata mutu, sai dai muyi *mutuwar kasko*, amma ba zata auri wannan yaron ba."

Bai ba Aliyu damar cewa komai ba ya fice daga ofishin ko wayar tashi bai É—auka ba da sauran abubuwan shi, da kallo Aliyu ya bishi, sai wani irin mugun tausayin shi ya kama shi saboda hango wani abu da ya ga shi Jabir É—in ma kamar fa bai san da ya kama shi ba bare yasan hanyar da zai bi wajen sarrafa kan shi, faÉ—awa yayi kan kujera yana tunanin lamarin, yiwuwar shi ko akasin haka? Ya Allah! Gashi dai ba haram bane, sannan tabbas akwai ilimin da ya sa haka yake faruwa, to kenan dama akwai abinda ubangiji ke nufi zai faru ne tsakanin su? Ya Allah.

*Lallai* lamarin da ya sa Jabir har ya zo babban shago yau babba ne, amma da Jabir yake faɗa mishi matsalar Maama ce, sannan dan Allah yayi ƙoƙarin fahimtar da ita yaron nan da za ta aura ba mutumin kirki bane, sai kawai ya zuba idanu yake ta karantar Jabir ɗin, idanun shi, yadda yake ta magana har shasheƙa yake, yadda yake maganaro ba tsayawa da kuma sauri sauri... Lumshe idanu Alhaji yayi sannan ya buɗe akan Jabir yana sauke numfashi, cike da gamsuwa ya ɗan zuro hannun shi ya dafa guiwar Jabir yace "Na yarda da kai Jabir, zan ɗauki mataki akan haka, ba zan sake bari ta kula kowa ba yanzu, dan naga fitina take neman mu da shi ko?"

Da sauri Jabir tamkar yaron da ke neman uwar sa ido rufe ya gyaÉ—a kai yace "E Abba."

Shima jinjina kai yayi yace "Shikenan, zan mata magana, in sha Allah *Maaman ka za ta sake dawowa gare mu*."

Wani murmushi yayi ya jinjina kai yace "Yawwa Abba, ka dawo da ita kawai, kaga ba zata sake kula kowane jaki ba."

Murmushi Alhaji yayi yana haɗe wasu irin yawu, ga abu nan ƙarara yana gani, tausayin Jabir sosai ya cika masa ruhi da zuciya, haka ya sallame shi ya tafi yana mamaki da tunani kan abun kamar dai yadda Aliyu ke can yana nashi tunanin.

*Alhamdulillah.*
[31/08 à 15:33] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_
Chapter 137 · 0% Book details