Sashe 29
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dariya tayi ta koma ta zauna tana ƙwala kiran sunan Aisha, amsawa tayi daga madafa ta fito da sauri... Kallo ɗaya tak yayi niyyar yi ma yarinyar nan, to amma ai sanin kowa ne shaiɗan na farmakar bayi na ƙwarai ta kowace irin kusurwa, in ba haka ba, ta ya yarinyar nan sheɗan zai ribace shi har ya dinga kallon shigar ta wacce ta yi ne kawai dan daga ita sai Kaka gidan, kuma atamfa ce jikin ta ɗinkin riga da siket, kawai kyau da kum dacewa da surar t a sukayi, sai ya zamana babu kallabi ko hijabi à kan ta, hakanne ya sa kitsonta da yau kwana uku da suka yi shi tare da Leila manya manya ya zubo a bayan ta har wasu wutsiyar gashin suka diro kan ƙirjin ta.
Tunda ta gan shi ta kyaɓe fuska kasancewar ta gwanar shagwaɓa har ta ƙaraso, tana zuwa ta tsaya tsakiyar kujerar da yake da inda Hajia take tana kallon shi kamar za ta yi kuka tace "Abbu, ina ka je? Kwana huɗu fa kenan Hajia tana ta neman ka."
Kallon ta Hajia tayi tana ɓoye dariyar ta, ko ita fa bata tambaye shi ba kuma bata tambayar shi idan yayi irin wannan shirun, hakan yasa take dariya da kuma kallon shi tana so ta ga zai amsa ma Aishar ko shariyar za ta samu ita ma. Sa'ad kuma lamarin ne ya so girman tunanin shi, to shi yanzu wannan ƴar za ta tsare tana tambaya inda yaje? Har tana masa wani kuka-kuka da kuma shagwaɓa kamar wata iyalin shi? Hajia kuma ta wani kasa dakatar da ita har ta na mishi dariya? A kausashe ya kalle ta cikin daƙilalliyar murya yace "Ke! Ni ba Abbun ki bane ba kuma na kowa ba, kika ake kirana Abbu sai na zubar miki da haƙora."
Jin haka yasa Aisha bi ta gabanshi ta zauna ƙasa kusa da ƙafafun Kaka tana mishi wani irin kallo ta riƙe hannun Hajiar tace "Hajia ai ba zaki bari ya fasa min baki ba ko?"
"Ba zan bari ba kam." Ta faÉ—a tana dariya, sai kum tace "Je ki kawo mishi abinci, yunwa yake ji."
Yunƙurawa tayi za ta miƙe tana kallo shi tace "To amma Hajia ya faɗa mana ina yaje kwana huɗu, kuma bai faɗawa kowa zai yi tafiya ba, fisabilillah haka ya dace?"
Duk ƙoƙarin Hajia saida ta tintsire da dariya tana kallon Sa'ad da ya bita da wani kallo yace "Ba zan faɗa ba ke, ɗanki ne ni ɗin?"
Sai kuma ya kalli Hajia dake dariya ya nuna mata Aisha data nufi madafa yace "Ki gaya mata ta daina min irin haka, a kaf gidan nan babu mai min irin gangancin nan, ciki kuwa har da Ibu."
Juyowa Aisha tayi ta kalle shi cikin marairaicewa tace "Gaskiya bai dace ba, *Abbu* ake cewa fa ba *Ibu* ba, ka ji *Abbuna*."
Idan ranshi ya ɓace kallon shi na gudana da sauri sauri ne, ma'ana ya kan dinga yawan ƙyafta idanu, to ganin haka yasa Kaka tabbatar da ya yi ful fa a wannan ɓangaren, dan haka ta juya ta kalli da lallai take son maida Sa'ad ɗin abokin wasan ta tace "Ƴar rainona, maza je ki kawo mishi abinci, baki san ko Iro tela ba ya mishi irin haka ba? Maza je zubo mishi abincin."
Turo baki Aisha tayi ta juya da sauri tana faÉ—in "To Mamie, ni dai ai gaskiya na faÉ—a mishi, kuma Kinga ko ni ina girmama shi ina kiran shi da Abbu, kenan shi ma ya dinga kiran Papina da Abbu."
Zunbur ya miƙe tsaye ya nufi madafar da mugun sauri, hakan yasa Hajia Kaka juyawa ta bishi da kallo tana kiran" Sa'ad, Sa'ad, Kaga Sa'adu..."
Cak! Kuma sai ya dakata ya juyo ya kalli kakar kamar yana shirin kai mata duka, cikin taushin muryar nan tashi kamar ta mace yace" Hajia, ban ce bana son sunan nan ba? Ni ba sunana Sa'adu ba."
Murmushi tayi tace" Shikenan naji, yanzu ina ka nufa?"
Nuna mata madafa yayi yace" Waccen Æ´ar taki zan takawa birki daga neman hawa min kai da take shirin yi, naga fa alama ke kika É—aure mata gindi a gidan nan, to wallahi za ta bar gidan nan idan ta sake hassalani."
Zaro idanu Kaka tayi ta riƙe haɓa tace" Ni kuma? Ban da laifi kai ma ai shaida ne ko, amma zan manta magana ta daina, kai kuma ka bar maganar za ta bar gidan nan, dan wallahi na saba da ita yanzu bana so mu rabu."
Kamar wani mai bata umarni ya nuna mata wajen zamanta yace" To je ki zauna ina zuwa."
Yana faɗa yayi hanyar madafar, tsaye tayi ba ta gusa ba dan ita tasan waye Sa'ad, yadda bata da tabbacin ya daina kula wasu mata, haka ba yadda za'a yi ta bar shi yana samun kusanci da ƴar mutane, dan haka take tsaye bakin ƙofar tana jira ta ga ya jima ta kutsa kai.
*Yana* shiga Aisha na zuba miyar a farantin tare da cokali a hannun ta da zata kai mishi, kalmar "Ke!" Da ya faɗa a kausashe yasa ta zabura har ta liƙe idanu, amma da ta ɗauki muryar sai ta juyo a hankali tana kallon shi tace "Na'am Abb..."
A hassale à kuma zafafe ya sake faɗin "Ke ba Abbu ba, ni ba Abbunki bane, ban da aure, ko baki fahimta bane? Sau nawa zan gaya miki ne?"
Ganin dai yanzu daga ita sai shi ne yasa ta jinjina kan ta turo bakin ta tace "Kayi haƙuri, ai ba sai ka haifeni ba zan kira ka da Abbu, girmamawa ce saboda taimakon da ka min."
Saida ya É—an kawar da kan shi yace "To bana son girmamawan, idan zaki iya kirana da Yaya ki kira, idan ba zaki iya ba kuma kirani da Sa'ad."
Ɗan buɗa ƙaramin bakin ta tayi da mamaki tace "Lahhh! Kiran sunan ka a wajena ai zunubi ne babba."
A ƙufule yana kallon ta yace "To kirani da kai, idan ba haka ba kuma ranki zai ɓace."
Zuba mishi idanu kawai tayi bata tanka mishi ba, dan haka ya ƙarasa kusa da ita ganin ta zuba miya a abincin kuma yunwa yake ji da ba zai iya hushi da abincin ba yasa shi ɗaukar farantin tare da maka mata harara sannan ya nufi hanyar barin madarar... Ƙarar wayar shi ta sa ya shiga lalubanta a aljihu, yana cirowa ganin sunan Hambali ne ya sa ya ɗan yi tsaye, shi ya ma manta da shi saboda wasu sabgogi da ya ƙara durmiya kanshi à ciki duk da dai wannan halatattu ne, wannan kiran kuma ya sa shi iya tunawa da akwai fa ajiya a acikin yarinyar nan, dan zaman da sukayi da ita tausayi take bashi sai kuma Allah ya ɗauke tunanin shi daga kanta.
A hankali ta danna ok sannan ya ɗora a kunne ba tare da ya ƙara tako ɗaya ba yace "Ina ji?"
Ba tare da Hambali ya damu da yadda ya amsa mishi ɗin ba dan hakan ɗabi'ar sa ce yace "Sa'ad, wai me na maka ne daka daina ɗaukar kirana? Ko dan yarinyar ta ɓata ne kafin ta shiga hannun ka?"
A wani gadarance Sa'ad ya waina idanun shi yace "Ba wannan maganar, ya aka yi yanzu?"
Cikin yanayin tashin hankali Hambali yace "Sa'ad akwai gagarumar matsala, dan gane da rashin ganin yarinyar nan, Sa'ad kai ne MaraÉ—i, dan girman Allah ka taimaka min a ga yarinyar nan."
Kyaɓe fuska yayi tare da taɓe baki yace "Wace irin matsala kuma?"
Da rashin gaskiya Hambali yace "Ba sai ka ji ba Sa'ad, kai dai ka taimaka min mu ganta, na maka alƙawarin biyan ka kuɗin da kayi asara har da ninkin su ma, ni dai kawai na ga yarinyar."
Ajiyar zuciya Sa'ad ya sauke ya buÉ—a baki yace "Ka ga, ni yanzun w..." Muryar Dr. Ema ya ji yace "Oga, ba ni shi a wayar zan masa bayanin haÉ—arin da take ciki."
Da sauri Hambali yace "Yawwa, Sa'ad ga Ema zakuyi magana." Ba tare da ya musa ba ya saurara har saida ya ji Muryar Ema yace "Oga Sa'ad, yarinyar tana cikin haÉ—ari."
Da wani irin yanayin sauri Sa'ad ya juyo ya kalli Aisha da tun farko shi take kallo, amma da ta ga wayar shi yake sai ta ci gaba da goge madafar, Ã tausashe ya furta "Wane irin haÉ—ari?"
Cikin tashin hankali Ema yace "Oga, a ƙa'ida bai kamata abinda ke cikin ta ya wuce sati biyu ba, yanzu kuma Kaga wata ɗaya fa kenan, yallaɓai idan baka damu da yarinyar ba, dan Allah kayi ƙoƙarin samota kafin a ɗora wani sati a kai, dan daga yanzu zuwa kowane irin lokaci ledar robar da aka zuba cocaïne ɗin da ƙwayar da ake sarrafa benelin da kuma tramol za su iya fashewa, hakan kuma zai iya ja wa yarinyar mummunar matsala, lalacewar kayan cikin ta, taɓa ƙwaƙwalwarta har ma da shafar jijiyoyin dake lura da gudanar tafiyar jinin ta, Oga, a taƙaice dai ba mutuwar farat ɗaya za ta yi ba, daga hanci, bakin ta da kunne kowane zai iya aman jini, bayan haka ba za'a iya gane kan matsalar ba kai tsaye, kafin a gano kuma... An makara."
Kallon da yake ma Aisha tana ta gugar tiles fuskar ta ɗauke da murmushi, tunani yake idan abinda ya zayyana ya faru fa? Zai rasa *ƙwaya ɗaya tak* dake duban shi tana faɗa mishi gaskiya, zai rasa mai kallon shi tana mishi shagwaɓa son ranta kamar wata matar shi. A rashin sanin yana kallon ta ta ɗago kan ta, sai kuwa tayi sa'ar sauke idanun ta cikin nashi idon yana mata wani marayan kallo mai ma'anoni, a take ta saki murmushi ta furta "Abbu..."
Wata razana yayi da bai san dalili ba har saida ya saki farantin ya fashe abincin ya zube, ƙarar farntin kuma ta haddasa mishi wata faɗuwar gaba da sarawa da kan shi yayi, a hankali ya buɗe idanun shi daga rufewar da ya musu, sai kuma ya juya mata baya da ƙyar ya iya furta "Tana cikin wannan haɗarin, shine ba ku gaya min ba?"