← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 168

Sashe 147

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Hajia tayi ta miƙe tana faɗin "Iyayen ki dai suka cuceki, ni dama ina bayan dattijo ne, ba dan a ce na masa tsufa ba ai da ni na aure abuna saboda nagartar sa."

Da kallo Ummu ta bita tace "Oho! Kun san da haka ni kika aura min shi? Kenen ni duniyar ta zage ni?"

Juyowa Hajia ta kalle ta tace "Ke, ba fa ke kika aure shi ba, shine ya aure ki."

Saida Hajia ta fita kawu Bilal ya kalle ta a tausashe yace "Ƴata, ya haka? Dubi zaman da muka tara da iyayen mu amma kin watsa mana shi, mun tara zaman nan ne dan a saka muku albarka da baku shawarwari, amma kinga kin hasala kowa ya tafi ba tare da anyi wani abu muhimmi ba, Abbun ki kanshi da sai ta ɓace kake ganin ɓacin ran ki dubi yadda ya bar nan bayan ya kashe miki tafi a fuska?"

A hankali ta matsa kusa da shi ko sauraren Mama ba ta yi ba dake mata nasihar ta gyara halin ta, cikin rarrashi ta kama ƙafar shi tace" Abbu, Abbu ai nasan zaka fahimce ni kai, Abbu dan Allah ya dace haka da suka min? Jabir fa yaro ne Abbu kuma k..."

Irin kallon nan na hangen nesa ya mata yace" Ummu, wa ya ce miki namiji yana kaÉ—an ne?"

Duƙar da kan ta tayi tana ayyna _" Tsoho ma ya kasa iyawa da ni bare ɗan mitsitsin yaron nan?"_

A zahiri kuma sai ta kalle shi a sanyaye tana zubo da hawaye cikin muryar kuka tace" Abbu, Jabir *Æ´ata* Kuwailat ce ta *dace* da shi wallahi, saboda ka ga yanzu tana sha huÉ—u ne, amma ni? Haba Abbu dan Allah ka duba maganar nan."

Wani abu da ya gano a tare da Ummun shine, ita kamar matsalar ta ba ma wacce su suka yi ta hangowa bace, ita kamar dai shekarun Jabir ɗin ne basu mata ba ko ya ce suka mata kaɗan, in hakane zai namiji ne Jabir, kuma tunda zasu zauna bari kawai ya mata na babba da yaro, a ƙalla ya nuna mata ko kwana ɗaya mutum ya baka a duniya ya fi ka dabaroa, haka kuma ko ka ba mutum shekaru akwai abinda zai iya yi ko ya sani da kai ba lallai ka san karatun ba.

Jim yayi alamar yana tunani, sai kuma ya kalli Mama dake kallon su yace "Hajia, ku É—an bamu wuri dan Allah zan yi magana da ita."

Da murmushi Mama ta miƙe tana addu'ar Allah ya shirya ki Ummu, da kallo Ummi ta bita tana ayyana _"Yo Mama ke ki aure shi mana idan ya sake ni, ai baki da miji kema, me ya hana ki aure har yanzu?"_

Saida Mama ta fita ya kalli Aisha yace" Kuna ji, sirri zamuyi da ku, zaku riƙe sirri?"

Ɗaga kawunan su sukayi, inda Ummu tayi wani murmushi tare da gyara zaman ta irin ta ga mafita a matsalar ta, cikin raɗa yake ce musu" Kina ji ko? Yanzu zaku zauna cikin gidajen nan na wasu kwanaki, kiyi haƙuri ki zauna da shi kin ji? Alma da zaren kin ji ya ce zaku koma maraɗi, sai kiyi gaggawar sanar da ni, ni kuma nasan le zan yi da zai sa ya tafi ya bar mana ke nan, shikenan kun rabu, amma fa kada kowa ya ji."

Cikin farin ciki Ummu tace" Da gaske Abbu?"

" Ina miki wasa ne?" Ya faÉ—a yana mata kallon tuhula, girgiza kai tayi alamar a'a, hakan yasa yace" To yanzu tashi ku tafi, ki saki jikin ki kici gaba da harkokin ki kawai, ni na gaya miki kafin ku bar nan sai auren nan ya mutu."

Cikin jin daÉ—i Ummu tace" To Abbu, nagode sosai, Abbu Allah ya saka maka da alkairi, kai kawa ka fahimce ni."

Kallon Aisha tayi tace" Muje?" Miƙewa Aisha tayi tana kallon Ummu sororo da mmakin wai da gaske ita ce gaba da ita? To gashi dai ƙarara ya bayyana kawun nasu dabara ya mata, amma wai ta yarda kuma? Tsabar son a raba auren ne? Ko tsabar son girman ta ne ya hanata gane bata da wayo? Haka ta kama ta suka fita tanata share fuska a dole yanzu so take ta saki ran ta tund an bata garanti na rabuwar auren ta da yaron nan.

*Tun* bayan sallah isha'i tsirarun mutanen da suka shirya rakata sua shiga harama, Ummu dake cikin farin cikin sirrin su da kawu Bilal haka ta zauna ana rangaɗa mata kwalliya ta gani ta yaɗawa a yanar gizo, tunda ai ya ce ta saki jikin ta kar wani ya gane wani abu, wani tsadadden material ne fari ƙal aka mata riga doguwa, haka komai aka mata shigar fari sai kwalliya da ta sake fitowa da ita. Tsaf ta zauna gaban su Mama da Mamie Nuriyya suka mata nasiha kamar yadda ake ma kowace mace kafin aka fito da ita, daga ƙofar ɓangaren su Mamie zuwa ƙofa tafiya ce mai zaman kan ta, dan haka mota aka saka ta sannan aka nufi gidan da suna kallon juna ne.

Ƴan rakiya bsu jima ba suka fito daga gidan, Aisha da su Kuwailat ne suka jima dan saida Aisha ta sa yaran suka sake yin shara da goge goge suna yi suna hira kafin su baro mata gidan, a ƙafa suka taho inda Aisha ta ji daɗin tafiyar dan duk hidimar da aka yi ba'a yarda an saka ta aiki mai yawa ba saboda halin da take ciki.

*Alhamdulillah.*
[03/09 à 11:52] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*68*

Da yana ɗaukar duk abinda su Aliyu ke yi dan su ƙular da shi ne, amma yanzu sai ya gane suna yi ne dan su lalata shi fa, so suke dole ya wa maman shi sheɗana, in ba haka ba me ya haɗa shi da kaza a wannan daren? Maaman zai ba kaza ta ci dan shi ma ta bashi ƙaniya ya ci ko me? Aliyu da ya ga da gaske b zai karɓa bane da sauri ya riƙo shi yana danna msa ledar a hannu yace "Jabir dakata kaji, wannan fa haƙƙin ta ne, kuma tun daga nan ne za'a iya gane riƙon da za ka mata, ko ba komai a ran ka a ƙalla dai ka bata tunda ana ba kowa, amma idan baka bata ba kenan zaka sa ta ji a ran ta dan ba budurwa ka aure ta."

Shiru yayi yana kallon Aliyun da yake ganin kamar wayo yake so ya mishi, sai kuma ya kalli Fahad dake ta faman dariya yace" To ce ma wannan ya daina min dariya, ni wallahi ba abinda zan wa Maama."

Cikin rarashi Aliyu yace" Mun sani mana, kai da kace ba É—an iska bane kai, ko ka iskance É—in ne? "

Girgiza kai yayi yace" Um um." Tare da figar ledar yayi hanyar shiga ciki, saida safe suka dinga yi mishi har ya ɓace ma ganin su, gidan tsit ba alamar akwai mutum a ciki, gidje ne dama irin na zaman mai mata ɗaya, haka ya buɗa falon ya shiga wanda dama ba'a yi gyara ba saboda ba zama zasu yi na lokaci ba, fridge, carfet, labulaye da wasu abubuwan buƙata ne kawai a falon, sai wasu sofa masu kyau da ya ƙawata falon.

Ɗaki biyu ne a ciki sai ban ɗaki dake gefen su bayan ta tsakat gida, ɗakin da ya ga hasken fitila ya nufa, ba rufe yake gaba ɗqya ba kuma ba buɗe yake ba, dan haka ya ɗan ƙwanƙwasa ƙofar tare da zuba wata irin siririyar sallama da ta saka gaban Ummu faɗuwa, duk da gidan miji take amma ta ma ɗan manta da wanene mijin nata, kayan baccin ta da aka haɗe mata da ƙananan kayan ta na ciki kawai take ta faman warewa, da sauri ta miƙe tana kallon ƙofar, sai kuma ta gyar tsayuwa tana ci gaba da duban ƙofa da son sanin lafiya kuma? Me y zo yi mata? Ba tare da ta gusa daga inda take ba irin ɗan nan ya zo wajen Maaman shi a gatse tace "Oui, wa ye?"

Jabir dake baƙin ƙofa jin ta msa wannan tambayar sai ranshi ya sosu, sai kawai ya turo ƙofar a gadarance ya shigo, kallo ɗaya ya mata ya ɗauke kan shi, kayan da aka kawo ta da su ne bata cire ba, ƙwarai Maama tayi kyau kuma sai tayi wani irin sharr da ita kamar ƴar budurwa, musamman da babu ɗan kwali a kan ta sai ƙananan kitson nan da ya fito rass ga wani jan lalle da aka cika hannayen ta da shi gaba da baya haka ma ƙafafu.
Chapter 147 · 0% Book details