← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 168

Sashe 63

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da maɗaukakin makaki ya kalle ta yace" Na daina son ki kuma? Ummu, kin kuwa san yadda nake jin ki? Ummu har yanzu ban yi zama da macen da nake matuƙar a rayuwata ba sama da ke, UMMU ina son ki, ina ƙaunar ki fiye da tunanin ki, amma me yasa kikayi wannan tunanin?"

Saida ta sa hannu tana share hawayen ta tace" Saboda yanzu baka jimawa idan kana mu'amala dani, me yasa? Bana gamsar da kai ne? Wallahi ina kula da kaina kuma ina anfani da abinda zai sa ka gamsu, ban san... "

Fashewa ta sake yi da kukan da ya saka shi jawo ta jikin shi ya rumgume cike da tausayi, ƙwarai ta birge shi da ta iya faɗa mishi haka dan duk cikin samun maslaha ne, to amma ya zaiyi? Bai taɓa tunanin za ta zo da buƙatar da zai kasa magance mata ba, daddaɓa bayan ta ya dinga yi tare da faɗin "Yi shiru to, kukan ya isa haka, saurare ni muyi magana."

A hankali ta tsagaita kukan tana kallon shi, cikin nutsuwa yana murza tafin hannun ta yace "Ummu Kulsum, ba sonki na daina yi ba, hasalima soyayyar ki kullum ƙaruwa take a zuciyata, sai dai abinda nake so ko gane shine, ni yanzu ba kamar da bane sanda muka yi aure, Ummu ai idan kika yi nazari lokacin da muka yi aure ina da sauran ƙuruciyar da nake iya gamsar dake, kuma duk da ƙarancin shekarun ki haka nake iya tafiya dake saboda ke kanki a lokacin baki gama zama cikakkiyar mace ba, shekaru kusan goma sha uku fa suka ƙaru akan waɗanda ke kaina, to ta ya zan iya yi miki abinda nake miki baya? Wallahi tallahi Ummu bana jin wani abu mai sunan sha'awa a yanzu da nake faɗa miki, amma ƙaunar ki da kuma salon da kike zuwa min da su, su suke jan ra'ayina har nake jin ina so na kusance ki, amma maganar gaskiya ke kaɗai kike samun haka a duk cikin matana."

Numfashi ya sauke mai nauyi kafin ya kalle ta sosai inda Ummu ma dake kallon shi duk ta zaro idanu gabanta na faduwa saboda abinda ya faɗa, to kenan ya zata yi? Haka za ta ƙarar da rayuwar ta? Ya Allah! Ɗorawa yayi da" Kiyi haƙuri kinji, in sha Allah wata rana sai labari, ni ba ma wannan ne ya fi damuna ba, yadda tunda kika haifi Kuwailat baki sake samun wani cikin ba? Bayan kuma lafiyar ki ƙalau."

Kalmar ta yi haƙuri ita tafi nanatawa, ta yi haƙuri kawai? Haka kenan za ta ci gaba da zama? Tsaf ta haɗe hawayen ta tare da janye hannayen ta ta sauka daga kan gadon, rufewar da idanun ta sukayi yasa ko zanin da ta rufe jikin ta bata ɗauka ba, haka ta shiga takawa zuwa ban ɗaki ba komai a jikin ta face tarin jigida da bata iya rayuwa babu it a jikin ta har ta shige ban ɗakin, saida ta ɓace ma ganin shi ya sauke numfashi, ya zai yi yanzu? Yana son Ummu, ba zai iya rabuwa da ita ba gaskiya, in sha Allah zasu samu mafita akan wannan matsalar, ina ma yana da ƙwarin da miƙewar nan da tayi babu kaya zai iya ranƙwafar da ita a gaban shi sannan ya auna mata kaya ya shiga bata wuta? Tashi yayi ya fita daga ɗakin dan ya samu Kuwailat su tattauna dan sun jima basu yi hira ba.

Wuni tayi cikin yanayi marar daɗi, tun tana jin kasala har mararta ta fara mata ciwo kaɗan kaɗan, ta kasance komai sai ta ji yana bata haushi, ranta na ɓacewa, hatta abinci ba ta ci tare da shi da Kuwailat ba, tana kwance ɗakin ta cikin wannan mawuyacin halin ta ji muryar Nabila daga falo suna gaisawa da ita, lumshe idanu tayi tana tunanin ko me ya kawo ta kuma? Ita dai tasan wannan zuwan na dare akwai abinda Nabila take so... Wayewar Nabila da kuma buɗewar idanun ta yasa Ummu tunanin ko dai za ta iya neman taimakon Nabila?

Tana cikin tunanin nan ta ji kawai ta buɗo ɗakin ta shigo ba tare da neman izini ba, buɗa idanu tayi à hankali ta ɗan ɗaga kan ta ta kalli Nabila dake faɗin "Aunty Ummu, ba dai bacci kike tun yanzu ba? Dan Allah tashi aunty ki saurare ni."

A tsanake Ummu ta tashi zaune cike da kasala tana yatsina fuska saboda jikin ta da taji duk yana ciwo ga ɓacin rai da take ji, kallo ɗaya ta ma Nabila ta gane shigar dake jikin ta, doguwar rigar kanti ce sai wani yalolon kallabi dake kafaɗar ta kanta ɗauke da hular gashin dokin da take sakawa idan tana son rufe askin dake kan ta. Zaune Nabila tayi tana kallon idanun Ummu da mamaki saboda ganin sun yi jajir alamar ta ci kuka, duk da akwai uzurin da ya kawo ta, amma ƙaunar da take ma Ummu yasa ta dafa kafaɗar ta tace "Aunty, lafiya ? Me aka miki kike kuka ? Baki da lafiya ne?"

Kallon ta Ummu tayi da yanayin ɓacin rai tace "Me ya kawoki gidana a wannan daren Nabila?"

Ba tare da damuwa ba Nabila tace "Aunty wajen ki fa na zo, na zo ki ban aro ne?"

Wata harara da bata taɓa kwatanta yi mata ba ta zabga mata tare da faɗin "Amma ai na sha gaya miki ki daina zuwa min gida da shigar nan ta banza, ko so kike a raina min wayo ne?"

Da sigar rarrashi Nabila tace "Yi haƙuri aunty Ummu ba zan sake ba, amma wallahi kafin na zo saida na suturta sosai."
Wata hararen ta sake yi mata kawai ta É—auke kai tace "Me kike so?"

Da kulawa Nabila tace "Kafin wannan aunty Ummu, me yake damun ki? Na ga Abban Kuwailat a falo shi da ita, ke kuma kina nan ke kaÉ—ai kina kuka? Me ya faru aunty?"

Girgiza mata kai tayi tare da gyara zaman ta tace "Ba komai."

Miƙewa Nabila tayi cike da masifa da hali irin na ƴan tasha tace "Billahillazi idan baki gaya min ba to zan ɗauka Alhaji Kabeer ne kuma zan same shi na mishi akuyanci, idan ba shi ba kuma to sai idan wannan matar tashi ce Atika take ko wa da take ɓata miki rai ita ma, dan haka wallahi sai na tashi hankalin kowa yanzu."

Da sauri Ummu ta riƙo hannun ta ta zaunar da ita kan gadon tana faɗin" Ke bana son iskanci, Nabila zan ci uwar ki wallahi, dama raina a ɓace yake za ki ƙara min wani."

Dariya Nabila tayi tace" Allah huci zuciyar ki aunty, faÉ—a min me aka miki kike kuka?"

Kallon ta tayi sosai cikin nutsuwa da taraddadin abinda take son faÉ—a mata sannan tace" Nabila, nasan ke kin san magunguna, dan Allah wane magani kika sani da idan namiji ya sha zai..."

Kunya da nauyi yasa ta kasa ƙarasawa, amma dake Nabila shaƙiyiya ce tuni ta harbo jirgin nata tace" Na gane aunty, kar ki damu wallahi zan kawo miki wani magani da Fahad ɗina yake sha, ina gaya miki aunty idan ya sha shi kwana muke ni da shi ba gajiya ba tsayawa hutun zango."

Da irin kunyar nan Ummu ta dinga sosa girar ta da ɗan yatsa ba tace komai, Nabila kuma tausasa murya tayi da sigar rarrashi tace" Auntyna, dan Allah zuwa nayi ki ara min sarƙar nan ta ki ta ƙafa ta zinariya, bikin ƙawata za'a yi jibi na kece raini, ina so nayi anfani da ita na cire wannan."

Wani kallo Ummu ta mata tace" Wa? Ni zan ɗauki sarƙata mai tsada na baki? Wacce mijina ya siyo min dan so da ƙauna?"

Ƙara marairaicewa tayi tace" Dan Allah fa nace aunty, wallahi babu abinda zai sameta lafiya lau zan dawo miki da ita."

Ba da son ran Ummu ba haka ta ɗauki sarƙar taa bata saboda tana ta mata magiya, haka ta tafi da alƙawarin gobe zata kawo mata maganin nan ita mata jaraba ta gani, taji daɗin haka dan tana ganin kamar za'a samu ci gaba wannan karan.

*******************

A nutse ya zuro jar ƙafar tashi daga cikin lafiyayyen jirgin ƙasan yana mai sake riƙe jakar goyon shi fuskar shi fal fara'a na nasarar da yayi a gasar musabiƙa da aka gabatar a Iran na Alƙur'ani mai girma musamman akan tajwidi, abun farin ciki ne a ce ka bige Larabawa da mutane suka fi ganin ai kamar su ne masu abun, dan haka shi ma yake wannan farin cikin na nasarori da yake ta yi akan cikar burin shi. Aliyu na bayan shi wanda tare suka tafi dan har saida suka sake koyon wani abu a tafiyar tasu, cikin farin ciki da ƙaunar juna Aliyu ya daf kafaɗar ta Jabeer tare da bubbugawa suna murmushi, lumshe idanu Jabir yayi sannan ya sauke su fes akan Aliyu cikin wata nutsatsiyar murya wacce dama tun fil'azal yana da ita, amma yanzu da ya ke kan kwankwaɗar madarar ilimin addinin islama sai nutsuwar sa ta ƙaru, kamalar sa ta ninku, haiba da dattakon shi suka ruɓanya, cikin sautin da kai tsaye ba zaka kira shi na zallar bahaushe ba yace "Alhamdulillah, mun iso Madina lafiya, saura gida."

Da fara'a Aliyu da ya fi shi tsayi saboda baya da ƙiba siriri ne sai tarin ƙasunba yace "In sha Allah, zamu fara sanar da Abba muna shirin komawa gare su."

Murmushi Jabir ya sake yi lokacin da suka tari taxi da zata kaisu masaukin su yace "Hakane, amma fa ni zumuÉ—i yasa tuni na sa *Imran* ya kama min hanyar gidan da gauro kamata zai iya sauka kafin mu ga yadda Allah zai yi damu."

Da mamaki Aliyu ya kalle shi, amma sai Jabir ya shiga taxin kafin shi ma Aliyu ya shiga yana rufewa tare da faÉ—in" Gidan haya kuma Jabir? Za ka kama a garin maraÉ—i in da Abba yake?"
Chapter 63 · 0% Book details