← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 149 OF 168

Sashe 149

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ɗago kan ta tayi ta kalle shi, sai kawai ta miƙe tsaye tana aika mishi wani kakkausan kallo muryar ta a ɗan ɗage sama tace "Idan ban yi kuka ba ya kake so nayi? Jabir ni ce zaka sa gaba haka kana wa wulaƙanci? Dan kawai na ce ka koma ɗakin ka? Shikenan ku maza da an ce wannan matar ku ce shikenan sai ku kasa girmamata ku dinga kallon ta kamar yanzu aka haife ta."

Jinjina kai tayi tare da komawa ta zauna tana jan majina da ƙara share idanun ta, kamar wacce ta tuna wani abu kuma sai ta kalle shi tace" Kuma da kake cewa ban gaishe ka ba, Jabir fisabilillah ni kake jira na gaishe ka dama? Ni ce fa, ni maman Kuwailat, a kawo ni gidan ka jiya amma ka dinga min ihu wai ban gaishe ka, saboda Allah maganar nan da kayi ta dace a ma'aunin hankali?"

Kallon ikon Allah kawai Jabir ke yi, saida ta gama maganar ta tsaf sai kawai ya taɓe baki yace" Hmmmmmm!"

Juyawa yayi ya sake shigewa ɗakin ya rufi ƙofar yana addu'ar Allah ya shirya wasu, ya kula ba wa wasu lafiya irin su Aliyu da maaman shi. Duk da tana son shiga ɗakin dan ta cire kayan ta tayi wanka, amma haka ta haƙura bayan ta daina kukan kawai ta kishiginɗa anan har bacci ya ɗauke ta ita ma.

Ƙarar ruwa a ban ɗaki ne ya tashe ta, ganin ɗakin nata buɗe ya tabbatar mata wato yaron nan ke wanka ko? Tashi tayi tana cire hijabin ta ta shige ɗakin ta rufo, saida ta ƙara gyara shinfiɗar tana ta ƙwafa da tsakin ya sakar mata ƙamshin wani bahagon turaren shi da ba ta san wane iri bane, yana da daɗi dai amma ita bai mata ba, tana gama gyara shinfiɗar ta cire kayan ta sannan tayi ɗaurin ƙirji dan yin wanka.

Ko da ta fito ta ji motsin shi a É—aya É—akin, dan haka ta shige ban dakin ita ma ta rufo, saida ta fara wanke kayan dattin ta sannan ta yi wanka ta shanya pant É—in ta a murfin tagar sannan ta canza pad ta fito.

*Ba ta* san fitar shi ba, saidai tana fitowa kan ɗan ƙaramin teburin dake tsakiyar falon dan babban an tura su yau da safe suna hanya, su Aisha na zuwa kula zasu yi gyaran ɗakin, farar takarda ta gani tana ɗauka kuɗi suka faɗo, duba takardar tayi tana kula duba kuɗin, gajeran rubutu ne daga Jabir _"Ki yi abinci iya ke, ina azumi."_

Wata irin ƴar dariya tayi tana zama tace" Ikon Allah! Nan Jabir wai kuɗin cefanai ne ya bani? Taɓɓ!"

Wayar ta dake hannun ta ta fara dannawa lambar Mama kira tana aje kuɗin da takardar, Mama na ɗauka Ummu cikin shagwaɓa tace" Aunty, shine ko a kira a ji ya amarya ta tashi?"

Dariya Mama Nuriyya tayi tace" Ke aunty baki sani ba, ni gidan la na so in je in gaishe ku, Abbun ki ya ce ai kawai ban da hankali, dole na haƙura fa, kula ya ce kar a kai muku abinci, ai ke ba yarinya bace za ki dafa."

Numfashi Ummu ta sauke tace" Aunty ki ƙyale Abbu, ni fa ya mara a fuska saboda auren ɗana, ai wallahi ina nan zai zo mu shirya."

Dariya Mama ta sake yi tace" Ai kam zai zo, dan tun jiya yake ta kallon hannun shi wai ya mare ki, har da cewa na kira ki naji kina lafiya? Ni kuma na ce na ƙi ai yana da waya."

A tausashe tace" Aunty ina zaman lafiya? Bayan kun haÉ—ani da yaron nan yna ta min rashin kunya a gida."

Tintsirewa Maman tayi da dariya tana faɗin" To Allah dai ya bada haƙuri, kinga aunty bari na je su Maman ki ne ke ta shirin tafiyar su."

Da sauri tace" To, saura kuma su tafi ba wanda ya zo min ban kwana." Har za ta aje wayar sai kula tace" Aunty a turo min abinci dan Allah, yanzu na tashi fa."

Da" To." Kawai mama ta amsa ba tare da tunanin to me ya sa ba zata dafa da kan ta ba ko dan mijin ta? Sallama sukayi inda kowa ya shjga yin abinda ke gaban shi. Sai azahar su Mama suka zo yi mata ban kwana, saboda zasu tafi ƙarfe 03:00 dan a Zinder zasu kwana kafin da asuba su wuce, saida tayi ƙwallar rabuwa da Maman haka ma Nabila saida tayi kuka kafin su bar Maman ta tafi.

*Ƙarfe 06:34*

Tana zaune kan kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya tana danna wayar ta inda take sauraren wata nutsatsiyar waƙar hausa, hankalin ta ya ɗauku kan mutanen grp ɗin su da suke ta mata barkar aure da tayi wanda ita bata faɗa ba ma sun dai ji ne, hakan ya sa har ya shigo yana sallama ba ta kula ba, saida ya yaye labule ya shigo yna sake yin salama ne tayi saurin ɗqga kanta ta kalli ƙofar.

Take ta maida duban ta kan wayar ta cikin daƙilewa ta amsa da "Wa'alaika salam."

Ba ta sake kallon inda yake ba, a nutse ya shigo bayan ya cire takalmin shi tare da duban ta a karo na biyu, ledar hannun shi ya aje kan teburin tare da yin zaune kan kujera yana faÉ—in "Alhamdulillah ala ni'imatil islam."

In kafin ya shigo ta san akwai wani abu a kusan ta haka yanzun ma da yake zaune, abinda ya saka shi kenan zuba mata idanu yana kallo, ba kwalliya tayi ba bayan kwalli dake ga idanun ta, amma ɗaurin da ta kashe kan riga da siket din da duk da bata miƙe tsaye ba ya san sun mata kyau, sai kawai ya miƙe ya shiga ɗakin nashi ya yo shirin watsa ruwa kafin a kira sallah.

Tana ganin ya shiga ta miƙe da sauri ta shige ɗaki dan dama ta so yin haka, amma bata so ta bada baya ya kalle ta saboda siket ɗin ya kamata sosai, kuma daga yanzu za ta dinga zama da hijab kusa da ita saboda irin haka, yana fitowa bai gan ta sai bai damu ba ya wuce ban ɗaki, dan danan ya fito ba jimawa amma sai ya samu ledar da falon yadda ya wuce ya bar su.

Yana shiga a gaggauce ya sanyo farar jallabiya da wasu silifas masu kyau ya feso turare ya fito, da sauri ya buÉ—e ledar ya É—auko robar dabino ya buÉ—e, guda bakwai ya É—auka ya wanko waje sannan ya dawo ya zauna, a nutse yayi buÉ—a bakin shi kafin ya fita masallaci.

*Alhamdulillah.*

[03/09 à 20:54] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*69*

Sosai ran shi ya ɓace ganin ya dawo ya ƙara tarar da ledar nan, kenan ba ta damu da abinda ya shigo da shi ba, bayan kuma shi ɗin ya kasance malami ne dake koyar da ƴan mata da matasa samari yadda ake zaman aure, yana faɗawa matan su dinga karɓan duk abindz miji ya shigo da shi, shine shi za'a nuna masa iyakar sa kenan? Kai tsaye akalar sa ya juyar zuwa ɗakin nata, yana zuwa tura ƙofar kawai ya yi, kwance take saboda hauka irin na Maama bayan yanzu aka idar da sallah, kuma shi bai ma ga alamun ta yi sallar ba. Ko da ta kalli ƙofar a ɗan firgice saboda ba ta tsammanin zai shigo wannan lokacin, sai ta sake mayar da kallon ta ga wayar ta hankali kwance, cikin dakakkiyar muryar da saida ta kalle shi yace "Zo nan?"

Daga haka ya juya ya fita, da tsananin mamaki ta kalle shi tana maimaita "Zo nan?" Sai kuma ta nuna kan ta tace "Ni É—in? Ni ce Jabir za ka ma wannan kiran?"

Zaune tayi tana cije leɓen ƙasa, sai ta jinjina kai ta gyara zaman ta, ba za ta je ɗin ba, dole akwai buƙatar ya koyi yadda zai dinga mata magana, ko dai yana mijin ta ya dace ya wani ce mata wai zo? Kuma ya juya ya fita kamar wani uban da ya haife ta, to ba zata je ba ya zo ya ɗauke ta idan ƙarfin shi ya kai.

*Wato* ba za ta zo ba kenan? Minti ashirin kenan fa da ya ce ta zo, wai Maama hawan jini ne take neman saka mishi daga jiya zuwa yau ɗin nan? To ba zai yiwu ba, gaskiya shi ba zai iya haƙurin da Abban shi ya yi ba, dan haka bari yayi maganin fetsara da sheɗanancin Maaman nan marar kunya kawai.
Chapter 149 · 0% Book details