Sashe 18
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zarah kam girgiza kai tayi cikin rashin jin daÉ—in abinda ke faruwa tace" Subhanallah, Haba Hajia, ya zaki yi jam'i bayan kin san a gidan nan akwai manya, kuma ni na faÉ—a miki wallahi ba ni na tado maganar Sa'ad ba, Alhaji ne ya tambaye ni ko ya daina abinda yake ni kuma na faÉ—a masa gaskiya."
Cikin zaƙalƙakewa Hajia Uwani tace" E mana kya ce haka, in da ɗanki ne ai ba zaki faɗa masa gaskiyar ba, sai dake na wa ɗan ne daya tsone muku idanu ko? To ni dai na faɗa muku wallahi, a sakar ma yaro mara ya yi fitsari mana, haka kawai za'a nemi tisa min yaro a gaba, ba ma tun ranar da labari ya yaɗu a gari cewa yana ginin da a shekara goma da ta wuce ba matashi kamar da ya yi irin wannan ginin, kuma anan kusa ma ba za'a samu ba, shikenan sai a dinga bi shi da jafa'i kala kala."
Hajia da tun tuni take ta ba Uwani baki ta ƙi sauraren ta ne ta kalli Zarah a tausashe tace" Ke Zarah, wuce ciki kinji? Kar na sake jin bakin ki a nan, wuce maza ga abin da zai fisheki."
Jin haka Hajia Sabira da ita ma haƙurin take ta bayarwa ita ta fara saurin shigewa falon sannan Hajia Zarah ta biyo bayan ta, Hajia ma juyawa tayi za ta bar wurin Uwani ta taɓe baki tace" Su dake ƴaƴan so ne ai an faɗa musu haka, wallahi i da ɗana ne dai kabewar kan kabari ne baƙin cikin mai taushe, ehe..."
Juyowa Hajia tayi ta mata wani irin kallo, tsohuwa ce tabbas tunda an kwarari shekara sittin da ƴan kai, amma kuma kulawa da rayuwar jin daɗi ya sa kai tsaye ba zaka ce ta kai wannan shekarun ba, bugu da ƙari tana kama jikinta sannan bata san wasa, fuskar nan a haɗe take kallon Uwanin data fara shan jinin jikinta, dan za ta iya cewa Hajia ta zame mata ƙarfen ƙafa, ba tun yau suke gwagwarmaya da matar nan ba, ta kuma buga da ita dole ta bar ta a inda take, dan haka suke zaman lafiya kawai idan ba haukanta ya motsa ba ta sako tsohuwar a ciki, to tasss take mata dan bata ɗauka ko kaɗan.
Cike da dattako da kuma gargaɗi har tana runtse idanu tace "Uwani, kin san dai ni ba tsaran ki bace ko? Sannan duk wanda ya yi zagi a kasuwa ya san da wanda yake, to ki iya bakin ki, sannan ki sani duk abinda ya samu shamuwa, to watan bakwai ne ya ja mata, da ba'a yi daren ba kuma gari ba zai waye ba, ba ke ko ɗan ki ba, *Iro tela* (Alhaji Ibrahim) ma bai isheni bare kuma ku, dan shi da kike taƙamar da shi ni na tsuguna na haifi abuna, ki kiyaye ni."
Juyawa tayi za ta wuce, sai kuma ta tuna da wani abun ta tsaya tare da juyowa, da yatsa cike a gargaÉ—i tace mata" Ki turo min idan ya dawo daga guje-gujen nashi, idan kuma ya bar gidan nan bai zo inda nake ba, laifin a kan ki."
Sake juyawa tayi a nutse tana takawa, ganin haka ne ya sa Iro tela in ji Hajia tahowa suka haɗe, duk da sun gaisa dan kusan wurin ta ma ya wuni, amma daɗin yadda ta kashe masa wutar nan wanda yake da tabbacin da shi ne sai Uwani ta ɗaga masa hankali kaɗai hankalinta zai kwanta ya sa shi sake rusunawa ya gaishe ta, amsawa tayi da fara'a tare da wucewa nata ɓangaren. Suna haɗa ido da Uwani ta turo masa baki tare da juyawa a hassale ta shiga ciki ita ma tana raya _"Ba zan turo shi ɗin ba, ki yi abinda za ki yi."_
Amma take wata zuciyar ta gaya mata _" Um um ! Kar ki bari ta ja miki abun kunya a cikin kishiyoyi, ko kin manta da Hajia *Yakura*? Matar da ta ga kina neman ɗagawa ɗanta hankali lokacin da zai auro Sabira, take, sau ɗaya tak ta ce ma Alhaji ce ta tafi gidansu sai ka nemeta, haka kuma aka yi ba ki kwana a gidan ba, dan haka yi haƙuri ki tura shi kawai, ai ba faɗuwa kika yi ba."_
Alhaji Ibrahim kuma ko a jikin shi, rigima, masifa, bala'i inda na Uwani ne ba wanda bata biya masa shafin shi ba kuma ya hardace shi tsaf a kai, dan haka idan ta so su suhulta a zauna lafiya, idan ta ƙi kuma ya ba banza ajiyar ta kamar yadda ya saba har sai ranar da ta ga dama ta nemi sulhu da kanta.
Yana cikin gudu wayar shi ta dinga ƙara, ta abun sauraron ya danna OK tare da faɗin "Ina ji?"
Da fargaban abinda zai iya yi masa ƙaton nan daga ɓangaren shi yace "Oga barka?"
Ba tare da ya dakata da gudun shi ba cikin haki na gudun da yake yi yace "Ido na zuba maka ai na ga za ka kirani ko kuma a'a, DG tun jiya fa kuka taso da yarinyar nan, kuma duk iskancin ku na tabbata 08:00 na safe sai kun iso garin nan, amma shine dake ni ga É—an isa kuka wani yi banza dani ko? To ina jin ka?"
Cikin duburburcewa da rashin gaskiya yana inda-inda yace" Ka yi haƙuri Oga, wallahi an ɗan samu matsala ne."
Daga inda yake akan titi ya tsaya cak yana ci gaba da huci ya dafe ƙugu yace" Wace rin matsala?"
A saiɓance ya furta" Yarinyar ce ta ɓata Oga, ta ɓace mana."
Shiru yayi yana kallon titi da ababen hawa, sai kawai ya ƙara tausasa muryar shi yace" Kun kyauta, amma ka sani ba zan yi asarar kwabo ba, milyoyin kuɗina ne a cikin yarinyar nan, ba'a turo min ita ba sai da na tura kuɗina, dan haka ka da ka sake kirana har sai ka nemo yarinyar, idan ba haka ba wallahi za ka biyani kuɗina ne."
Jin yana shirin katse wayar yasa DG saurin faÉ—in" Oga dan ka saurare ni?"
Tafiya ya fara yi akan titin yace" Ina jin ka?"
Cikin magiya yace" Ka yi haƙuri Oga, wallahi cikin neman ta muke har yanzu, yarinyar ta ribace mu ne har ta gudu, kuma gidan da muke zargin ta shiga a erea muka wuni muna dakon ta amma ba ta fito ba, yanzu bayan dawowar mai gidan mun karya doka mun shiga gidan muka bincike amma ba mu same ta, Shiyasa na kira dan ka san halin da ake ciki, amma na tabbata zamu samo maka ita yallaɓai."
Cike da halin ko in kula Sa'ad ya taɓe baki yace" Matsalar ka ce, na gaya maka ka da ka sake kirana muddin baka same ta ba."
Da sigar rarrashi DG ya sake faɗin" Oga, dan Allah to ka mana wani taimako? Da za ka yi magana da Yallaɓai ya turo mana ko hoton ta hakan zai taimaka mana, sannan fa ka san tana cikin hatsari saboda ba komai za ta ci ba saboda kayan nan dake cikin ta, har a samu matsala ledar ta fashe mu zo muyi haihuwar guzuma."
Tabbas gaskiya DG ya faɗa, dan haka bai watsar da maganar sa ba illa kawai cewa da yayi" Na ji." Sannan ya kashe wayar tare da ci gaba da gudun shi. Duk yadda ya so ya isa gida kafin sallah magariba abun bai yiwu ba, hakan yasa dole ya tsaya a matsalacin hanya yayi sallah, duk da yayi gumi sosai amma kuma zufar na fitar da ƙamshin Turaren Gucci da ya yi anfani da shi, ana idar da sallah ya fito dan ƙarasawa gida.
Tafe yake yana turawa Hambali saƙon ɓatan yarinyar da kuma son ya turo mishi hoton ta, yana gama tura masa saƙon ganin ya shigo layin gidan nasu ya sake mayar da wayar aljihu ya fara gudu sai dai a hankali ƙwarai, fitowar *Aisha* da gudun bala'i sakamakon wasu samari su uku da tun tana sallah a bakin wani gida sukayi tsaye suna mata magana, da ta idar ta tashi dan bar musu wurin kuma sai suka dinga kiranta suna mata magana, hakan yasa ta dinga sauri ba ta kula su ba, dan ta lura suma sheɗanu ne kamar dai wannan na ɗazu, hakane yasa suka shiga bint suma da sassarfa suna daka mata tsawa da cewa "Ke! Ke! Ba ki ji ne? Da ke ake magana."
Dalilin da yasa kenan ta tsorata matuƙa ta zabga da gudu tare da karyo kwanar da take tunanin ko ta samu maceci, cikin ikon Allah Sa'ad dake ɗan gudun shi a nutse ta kawo masa karon da ya saka shi yin baya da ƙarfi saboda abun bazata ya zo masa, hasalima bai taɓa tsammanin zuwan mutum ba a wannan lokacin, sai gashi an fito masa da ƙarfi an kuma yi awon gaba da shi, rashin sanin waye da kuma wace manufar aka bangazoshi haka yasa Sa'ad yin azamar riƙo damtsen jinsin da bai gama tantance namiji ne ko mace ba, shi dai kawai ya jawo wanda ya kawo masa karo ne dan su yi mutuwar kasko. Mummunar faɗuwa yayi da ta sa duka sassan jikin shi amsawa har saida ya runtse idanunshi sannan ya furta "Aouuuu!"
Aisha ma duk da akan jikin shi ta faɗa amma sai da ta ƙwala ƙara dan ba tayi zaton abun ba ita ma, wannan ƙarar ta ankarar da shi da mace ya yi karo kenan, a hankali ya sa hannayen shi ya ture ta gefe ɗaya sannan ya yunƙura ya tashi yana kaɓe jikin shi tare da yi mata wani kallo sanda take tashi tsaye ita ma tana waiwayawa bayanta tana faɗin "...
*ME CE CE DAMUWAKI*?
Rashin ni'ima?
Rashin gamsar da mai gida?
Warin gaba?
Bushewar gaba?
Zubewar nono?
Cikowar nono ?
*Kina buƙatar...*