← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 132 OF 168

Sashe 132

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Fitowar ta kenan daga wanka tana ɗan cije fuska saboda gajiya da tayi sosai akan kujerar dukkhan, ƙafafun ta ta kalla da har suka mata mijirya sosai, a hankali ta ƙara gaban gado ta zauna tana ɗaukar kofin da dama ta tanadi abun ta, cokali ta sa ta buɗe babban gwangwanin madarar dake gaban ta ta zuba a kofin mai yawan, sannan ta buɗa wata ƙaramar kwalba dake ɗauke da dakakken kanunfari gari luƙui ta zuba kaɗan, haka ta zuba garin dabino shima a ciki da garin aya, ruwan dake cikin flask masu ɗumi ta ɗauka ta zuba ta gauraye, rintse idanu tayi ta kifa kai ta shanye duka sannan ta aje kofin tana sauke numfashi. Miƙewa tayi a hankali ta ƙarasa bakin ƙofa ta buɗe ta ƙwala kiran sunan Adama? Sai da ta kira sau biyu sannan ta amsa, daga nan ta tambaye ta "Ina kaskon wutar da nace ki kawo min?"

Da sauri Adama ta taho tana faÉ—in "Gashi nan Hajia, dama jira nake ki fito."

Dawowa tayi ɗakin tana takawa da ƙyar, wallahi jaraba ce tasa take wannan abubuwan, amma fa tun ranar farko data fara ta fara shiga bala'i, wannan ciwon marar nata ya dawo mata sabuwa fil, kuma wannan ma yafi waccen ƙamari saboda wannan haka take wuni kwana uku kenan, marar ta sai tayi nauyi tana yawan murɗa mata, ga kuma ruwa d take yawan fitar ta masu kauri da yauƙi da ɗumi da yake sakata canza pant duk sanda zatayi sallah.

Da ladabi Adama da ta aje kaskon tace "Gashi Hajia."

A hankali ta kalle ta cikin kasalalliyar murya tace "Nagode Adama."

Juyawa tayi zata fita Ummu tace "Adama me kuka dafa? Yunwa nake ji."

Gyara tsayuwa Adama tayi tace "Hajia ai Mamie ce ma a madafa, mu kama mata kawai muke yi, amma yanzu na sauke dambun shinkafa da tayi da cabage, s..."

Dakatar da ita tayi da "Akwai salade?"

Da fara'a tace "E Hajia, shi nake wankewa ma yanzu haka."

Jinjina kai tayi tace "To kinga ni nafi son salade É—in, idan kin gama ki kawo min shi kaÉ—ai kawai."

Jinjina kai Adama tayi ta juya tana faɗin "Shikenan Hajia." Saida ta rufo ƙofaro bayan fitar Adama sannan ta sake saka kaskon tsakanin kujerar tsugunno, kanunfari ta ɗauka guda huɗu dake irin na Saudia ne mai yaji ne sosai ta saka a wutar sannan ta zauna kan kujerar tare da rufe jikin ta da kakkaurar dara.

Idanun ta a rufe suke tana jin yadda yake shiga jikin ta tana jin zafi, ƙara rintse idanu tayi sosai tana ayyana _"Matsalar kanunfari kenan."_

Gashi daga ya fara shiga jikin ta sai ɓaɓɓago mata da ruwa yake har tana jin suna gangara a jikin ta, sai dai bata tashi daga hakan ba tana zaune saida ta ji hayaƙin ya fara rage shiga jikin ta sannan wutar ta fara ƙauri sai ta miƙe, saida ta sake komawa ban ɗaki ta kama ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito.

Tana zaune kan sallaya tana azkhar Mamie ta shigo da flate a hannun ta, zaune tayi bakin gado tana faÉ—in "Aunty kin idar ? Ga salade É—in."

Jim Ummu tayi kafin ta shafe addu'o'in neman tsarin da ta sba yi bayan kowace sallah sannan tace "Aunty, na idar."

Miƙo mata tayi tana faɗin "To gashi."

Karɓa tayi ta aje gaban ta sannan ta cire hijabi, a nutse ta ɗauki cokalin mai yatsu ta fara tsakuro salade ɗin da ya ji tumatir da ƙwai da kuma mayonnaise har da cucumber da dankalin turawa, tana fara ci ta kalli Mamie din dake kallon ta tana karantar yanayin ta tace "Aunty, gaskiya fa daga yau na daina yin komai."

Tsura mata idanu tayi kamar mai tuhumar ta tace "Me kika daina É—in?"

Sadda kan ta tayi ƙasa tana tsakurar salade ɗin tace "Shan komai aunty, na daina gaskiya."

Numfashi Mamie ta sauke tace "Me yasa?"

ÆŠan É—aga kanta tayi ta kalli Mamie É—in da kunya ta sake sadda kanta tace "Bana jin daÉ—i ne aunty."

Shiru Mamie din tayi na wani lokaci kafin tace "Shikenan, zaki iya dainawa, amma idan aka shiga satin sai ki ƙara ko na kwana uku ne."

Cike da kunya ta sunkuyar da kan ta, hakan yasa Mamie tashi zata fita, sai kuma ta dangwari kan Ummu cike da raha tace "Aunty ba dai jaraba ba, ni dai wallahi ba haka nake ba, sak abokina kika biyo."

Irin taɓararren kukan nan Ummu ta fashe da shi tana sosa inda Mamie ɗin ta ranƙwashe ta amma ba tace komai ba, sai Mamie da ta kai ƙofa tace "Ki gaggauta fa kafin rana ta hantse, kin san zamu tafi siyayyar kayan baccin nan da kuma kwanuka."

Da sauri Ummu ta kalle ta tace "Aunty, Abbu ya bayar kenan?"

Ɗaga mata gira tayi tace "Me zai hana ya bayar? Ai baya saɓa umarnina." Dariya Ummu tayi saboda yadda Mamie tayi maganar, saida ta fice sannan ta gyara zaman ta da kyau ta maida hankali ta ci salade ɗin nan.

*Alhamdulillah.*

[28/08 à 11:25] MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

*Tallah, tallah, tallah*

*SECRET DE LA FEMME DU MANGA*

_Gidan Kamshi, Sirrin Manyan Mata, nesa tazo kusa,Amarya ,Uwar gida,Ango da mai gida Har ma da yan mata da samari shin kuna sane da cewa HAJIYA FUSAM ta shirya tsaf domin gwangwaje ku da turarakunta masu dankaran kamshi? Tare Kayan gyaram jiki na musamman ,wanda daga nesa kamshin ki kadai ya wadatar ya isar da sakon zuwanki waje,gidan ki kuwa sai ya zam abun kwatance wajen kamshi, kar na cika ku da surutu bara in fara zayyano su_

Farar Humura
Bakar Humura
Humura special,
humura de bain
Humura epicé
Lait de nuit
Parfums désodorisant
Parfums rideau et dras
Lait de nuit
Alkam
Kulakcam
*WaÉ—annan kadan ne daga bangaren turaran ruwa*
Gagab, sandal flex, Durot, durus, sandal fleur, tafarce, farce, sandal bangui, sandal, hypotonic sandal, al'ut, coktail creation VIP, Gajiji, Mankaji, turaran wutar labule da cafet, Aba malan, boulettes

*Munada bangaren gyaran jiki kamar haka:*
mai mai saka santsin jiki, mai mai kanshi, Kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi santsi da laushi, kayan gyaran jiki mai saka fata ta yi fari, Sabulu mai saka fata ta yi haske, sabulu mai saka fata ta yi santsi, sabulu mai goge yanayin fata, mai wanda baya saka fari mai gyara fata

Sayen na gari mai da kudi gida,sai an gwada akan san na kwarai💃💃
Hajiya Fusam na zaune a kasar Niger domin yin magana da ita kai tsaye tuntuɓi wannan lambar *+227-97-82-44-94*
*SECRET DE LA FEMME* _(GIDAN ƘAMSHI-SIRRIN MANYAN MATA)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*62*

Siyayyar kayan bacci da kwanuka suke ba ji ba gani, sun fi awa uku suna zaga cikin babban shagon zamanin, kafin Mamie ta nemi zagayawa wajen siyar da kayan ƙwalam, da fari Ummu cewa tayi sam ba zata siyi kayan zaƙi ba, amma sai tace "Aunty ba ni zan sha ba, Kabil ne ke so shine zan siya na tura masa."

Wani kallo Ummu ta mata tace "Aunty Kabil ɗin dake ƙasar da ake sarrafa chocolat kala kala, shine zai sa a siya masa anan bayan an turo daga can?"

Murmushi Mamie tayi tace "To ai ya ce can tsada ke akwai."

Irin kallon nan Ummu ta mata na baka dai yarda da abun nan ba, hakan yasa tace "Da gaske, idan baki yarda ba sati mai zuwa muje New-York É—in."

Murmushi kawai Ummu tayi tare da yin gaba tace "Aunty kinsan Abbu faɗa yake miki idan kina shan kayan zaƙin nan, zan faɗa masa na ce ya sa ido sosai dan kin siyi sababbi."

Kallon Ummun tayi tace "Kin ga ni kar ki haɗani da shi, daga nan muna siya zan miƙa gidan mota."

Sosai Ummu ta kalle ta, sai kawai ta girgiza kai tace "Ban san mota ta fara zuwa inda Kabil yake ba ai, da tuni na sha mai a tawa motar naje."

Shiru Mamie tayi dan ta kula magana ce ta faɗa mata, ƙarasawa sukayi cikin s'a Ummu ta samu kayan ƙwalam na jerin masu ciwon suga wanda basu da zaƙi, ai ko su ta matsa dole aka siya, hakan ya sa Mamue ke ta turo baki tana bata so ita ta fasa siya amma saida Ummu ta siya, sun isa wajen biyan kuɗin kenan Jibril ya shigo neman wani turare da yake aiki da shi, da fara'a ya ƙaraso yana gaishe da Mamie, kafin ya kalli Ummu da wai salo yace "Ranki shi daɗe, da gaske dai kin hanamu ganin ki."

Murmushi tayi cik da jin kunyar rashin amsa mishi saƙonnin da har yau yana turo mata tace "Ina wuni?"

Da fara'a ya amsa da "Lafiya lau wallahi, ya kike? Ya kwana biyu?"

A taƙaice ta amsa da "Alhamdulillah."

Sai kuma ya bita da kallon ki tausaya min yace "Ranki shi daÉ—e, idan babu so me ya kawo gaba kuma?"

Ɗan zaro idanu tayi tace "Gaba kuma? Da wa? Anya ni na taɓa yin gaba ma."

Murmushi yayi yace "To ba gashi ba, da na ɗaga kirana ma, amma yanzu aka daina, saƙonnin ma da nake turowa ko kulani ba'a yi fa, a ƙalla dai ranki shi daɗe ko sallama a dinga amsa min."

Gaskiya kam ! Kuma ta ji ba daɗi da ko sallamar bata amsa mishi, duk da dai ai laifin shi ne dan ta faɗa mishi ma ai suna soyayya da Yayan ta, me ya hana ya shafa mata lafiya shi? Wai shi baya jin kunya ma dan Allah? Idan ta ce ta amince shi yana ganin zai iya da ita ne? Ko da yake laifin ta ne, tunda ai Alhaji Haris take ta sanar da shi yayi haƙuri alaƙar su ba mai yiwuwa bace, sannan ta gode da ƙauna da ya nuna mata da ɗawainiya, daga haka tayi bloquén shi a wayar ta har yau ba su sake magana ba, to shima da haka ta mishi ai da an zauna lafiya.

A hankali ta kalle shi tace "Shikenan a gafarce ni, kuma dake kasan ana ta shirin É—aurin aurena ne, to ni kaina bana da lokacin kaina bare ma waya."
Chapter 132 · 0% Book details