← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 168

Sashe 116

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dake rasuwar nan da aka yi tasa ana barin shiga babu ƙwaƙwaran tsaro, buɗe mishi ƙofa sukayi ya wuce shi da motar shi bayan sun gaisa, da kuma jagorancin wata mai aiki ya isa har falon Hajia inda nan Mardiyya take tare da ita. Akwai mutane sosai a falon, amma inda aka nuna mishi Mardiyya tana zaune daga ita sai Hajia da wata tsohuwa ce a ɗan corridor, dan haka ya shiga takawa a nutse har ya isa wurin, yana zuwa ya durƙusa yana gaishe su, salayyar dake kusa da Aunty Mardiyya ta warware ta shinfiɗa ta ce masa yaa zauna, duk da kuwa dukan su kallon son sanin ina suka san shi suke? Musamman aunty Mardiyya da yake mata fuskar Aghali, wato autan Anna wanda aka ce yana kma da Fatime maman Jabir, dan ita kafin auren ta da Alka Fatime ta rasu, dan haka ba ta san ta ba gaskiya.

A nutse ya zauna kan shi a ƙasa kafin ya ɗan ɗago ya kalli aunty Mardiyya da shi ba zai iya manta ta ba yace "Mammie, na san baki shaida ni ba, ni ne Jabir, ɗan margayiya Fatime."

La'ilaha ilallah ! Wani irin farin ciki da ta nuna a fuskar ta mai tafe da cikar ƙwalla a idanun ta ya saka shi tsura mata idanu, duk da dai har da kunya a tare da Anna, amma shi bai ga haka ba gaskiya, wani irin farin ciki ne ya bayyana gare ta tana faɗin "Lahhhh ! Jabir ? Kai ne haka? Jabir, yaushe ka zo?"

Murmushi yayi mai birgew cikin taushin murya yace "Yau muka zo Mammie tare da Abba, na tambaya aka ce ba ku nan, ni kuma ba zan iya jira sai kun zo ba, shiyasa na zo."

Cike da ƙaunar yaron wanda haka kawai take jin ta ta matso ta ɗora hannun ta na dama a kan shi tana shafawa tana faɗin "Allah sarki Jabir, baka manta da ni ashe? Gaskiya na ji daɗi sosai da ziyarar nan taka, ya kake Jabir? An sha karatu?"

Saida suka sake gaisawa kafin ta nunawa su Hajia dake kallon su tace "Hajia, É—an Fatime ne babbar Æ´ar mijina wacce ta rasu bayan haihuwar sa, ya jima rabon shi da nan sosa, shine sai yau suka zo."

Cike da dattijantaka Hajia ta miƙa mishi hannun ta da murmushi, da gimmawa Jabir ya miƙo mata nashi hannun, ɗan jinjinawa tayi tana faɗin" Jabir, Allah ya maka albarka, gashi kuma kai ka baro Maraɗi yaran nawa kuma duka suna can wani muhimmin abu."

Cikin nutsuwa yace" Ameen Ya Allah, nagode sosai, Allah ya ƙara muku lafiya da nisan kwana, Allah kuma ya jiƙan Alhaji da rahama."

Ya É—an jima suna hira da aunty Mardiyya kafin ya yi haramar tafiya yana faÉ—in" Tsarabar ku tana gida, naga rashin dacewar zuwa muku da ita nan, sai idan kun koma in sha Allah."

Da mamaki aunty Mardiyya tace" Kenan ba zan same ku ba? Ina so mu sake zama Jabir muyi hira sosai."

Ya ji daÉ—in haka, dan haka ma yace" Ni kaina ina son haka aunty, dan akwai abinda nake so dangina su yi min, to kinsan Anna yadda take, bata sakar min jiki yadda zamu tattauna ba."

Cike da bawa maganar sa mahimmanci tace" Na sani Jabir, ka ci gaba da haƙuri kai dai, ni kaina ina so ne muyi hirar bayan rabuwa, musamman akan ɓatan ka da aka dinga jita-jita, ina so naji gaskiyar lamarin, amma dai ba zaku koma ba har sai na zo ko?"

Jinjina kai yyi yana murmushi yace" Zan yi ƙoƙarin ko da kwana ɗaya ne mu ƙara har ku dawo."

Da farin ciki ta amsa da" Yawwa, nagode sosai Jabir, in sha Allah sai na zo."

Su Hajia ya kalla ya musu sai anjima, cike da tsokana Hajia da son mutumta baƙon na Mardiyya tace" To Jabir, sai kwana biyu, duk da dai naji kafi son kakar ka Mardiyya akan ni Maman ka, dan ita kaɗai ka kawowa tsaraba."

Dariya ce ta kubce mishi saboda murna ya rusuna yace" Tsaraba ba zata haÉ—ani da Mamana ba, in sha Allah zan sake dawowa na kawo muku taku tsarabar da ta fi ta kowa."

Dariya Hajia tayi tace" To Allah ya yarda, a ƙalla dai ko baka dawo dan kawo min tsaraba ba, ka dawo dan na sake ganin kamilalliya kuma kyakyawar fuskar ka."

Murmushi yayi sosai cikin taushin murya yace" Nagode, kamar yadda zan iya dawowa ko dan na sake ganin ainahin dattijanka."

Duk dariya sukayi kamar waÉ—anda suka jima da sanin juna, saida aunty Mardiyya ta raka shi har inda ya aje mota suna ci gaba da sai anjima kafin ta juyo shi kuma ya bar harabar gidan.

*WASHE GARI*

Tunda ya kira Alhaji bai ɗaga ba ya koma kiran Aliyu, duk da ya san ko lokacin da yake nan suna barin wayoyin su gida ne idan zasu tafi masallaci, amma kuma duba da lokacin da suke dawowa yayi sai ya sake kira, kira uku ya ma Aliyu ba'a ɗaga ba, dake yana da riƙo da aƙidar idan ka kira mutum sau uku bai amsa ba to kar ka sake kira, kamar dai yadda aka ce ka koma idan kayi sallama gidan mutum sau uku ba'a amsa maka ba. Yana da yaƙinin idan Aliyu ya gama uzurin da ya hana shi ɗagawa zai kira shi, duk da yafi tunanin kawai ba ya kusa ne, dan ko me yake yi idan ya kira ko bai ɗaga ba to zai tura masa da gajeran saƙon *zan kira ka*, dan haka suka ci gaba da zaga dangi shi da Abban shi ana ta nuna musu Jabir dai, wanda kowa yayi watsi da shi saboda dalili marar ƙarfi.

*Bayan* ya shigo ɗakin ya tarar da kiran Jabir uku, maida mishi kira yayi nan take yana zama bakin gado, ba jimawa Jabir ya ɗaga, daga ɓangaren Aliyu ya fara faɗin "Alaramma barka, ka kira ina waje."

A sanyaye Jabir kamar wanda ke rowar muryar sa yace "Umm! Me kake yi?"

Cike da takaici Aliyu yace "Kana min magana kamar kana yi da budurwar ka, to ba abinda nake, me yasa ka kira ni kai?"

Nauyayyar ajiyar zuciya Jabir ya sauke, sai ya ji kamar Aliyu faÉ—a yake masa ko wani abu mai kma da hka, dan haka kawai yace "Ba komai, sai anjima."

Aliyu ma da ya fahimci me Jabir É—in ke nufi da abinda yake shirin aikatawa, wato ya yi hushi kenan? Waina idanu yayi da sauri yace "Dakata."

Ɗan saurarawa Jabir yayi, sannan ne Aliyu ya shiga jero numfashi, abinda ya ji ne yake ta masa yawo a tunani, gashi kuma ba yadda zai yi, shiyasa duk ranshi ke jagule yake jin haushin kowa da komai, amma dake basa samun saɓanin dake wuce awanni ma da Jabir ɗin yasa yace "Ina jin ka, ya Abba?"

Take Jabir ya fahimci akwai damuwa, dan dama da ka ji ɓacin ran Aliyu musamman baka san hawa ko sauka ba, to tabbas wani abu ya ɓata masa rai ko yana cikin tunanin wani abu dake caza masa kai, saɓanin shi da ya ƙware wajen shanye damuwar sa, zaka iya msa laifi sau ɗaya ya maka uziri, sau biyu ma haka, to idan kayi na uku ne zai iya maka magana shima a nutse, amma idan ka maimata bayan haka? To fa nan zakuyi ba daɗi. Cike da kulawa Jabir yace da shi "Me yake damun ka?"

Shiru Aliyu yayi yana lumshe idanu, sai kuma ya saki murmushi saboda jin daɗin yadda Jabir ya fahimta duk da bai ga fuskar shi ko yanayin shi ba sannan yace "Maganar tana da mahimmanci, kuma akwai buƙatar mu zauna sosai ni da kai, dan haka bai kamata muyi ta a waya ba, zan jira har ka dawo."

Jabir mutul ne mai sauƙin kai da fahimtar mutane da kuma rashin son shiga rayuwar wasu, duk da ya tabbatar wa kan shi akwai matsalar, amma kuma tunda ga shi yadda ya ce, sai kawai ya masa uzuri yace" Shikenan, Allah ya datar damu."

A ake Aliyu ya amsa da" Ameen, ya Abba ? Ya kuma su Anna da kowa da kowa?"

A nutse shima yace" Kowa lafiya lau, ya Abbana yake? Na kira ba'a É—aga ba, da fatan suna lafiya?"

Saida Aliyu ya feso iska daga baki kafin yace" Lafiya lau Abba, yanzu ma na baro shi falon Hajia babba."

Cikin jin daÉ—i Jabir yace" Na ji daÉ—i, zan sake kiran su zuwa anjima."

Cike da tsokana Aliyu ya gyara zama yace" To ya? Anna bata maka mata a can ba? Ko dai ka rantse sai Æ´ar garinmu za ka aura?"

A daƙile Jabir yace" Idan na nema ka hana ni, sai anjima malam."

Dariya Aliyu yayi yace" Da alama ma ka samu buzuwa acan ko? Dan naga daga yin maganar kana neman kashe min waya."

Cike a gargaÉ—i Jabir yace" Aliyu."

Inda Aliyu ya amsa da tsokana" Na'am, Jabir."

Kafin kuma Jabir yace wani abu sai yace" To kaga, idan kai baka so ni ka sama min wata kyakyawar buzuwa, ka dai gane kyawun da nake nufi ai?"

Shiru Jabir yayi, kyakyawa da Aliyu yace yana nufin, yar babban gida, mai tarbiyya ƴar dattawa, wannan shine burin su akan mace, idan ubangiji ya basu kyakyawar zasu karɓa suyi godiya, amma dai addini suka fara sakawa a gaba. Sallama sukayi daga haka inda Aliyu ya tashi ya shiga wanka dan ya shirya ya fita sabgar shi da ta Jabir da ya bar mishi sallahun dubawa kafin ya zo,komai Alhamdulillah komai na tafiya daidai sai san barka.

********************

A ɗan lokacin da ya gabata na rayuwar ta bata jin akwai wani wuni da ta gabatar da ya kai mata wannan da take gudanar da shi da iyayen ta yi mata daɗi, Abbun ta, Mamien ta, sun saka ta tsakiya suna ta shafar jikin ta, Yaya Bilal kuma da aunty Fa'iza na gefen su zaune suna ta hira cikin nishaɗi, sai Aisha da har kan ƙafafun Ummu ta zauna ta rumgume wai ita ba zata yarda a barta baya ba, daga ƙarshe kuma da Sa'ad ya zo tare da yaran su duka da suka sauko daga islamiyya sai ta samu wata kujerar ta zauna.
Chapter 116 · 0% Book details