Sashe 6
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dakatawa yayi ya juya ya kalli gefen da take yana sissine kai, takowa ta fara yi tana matsowa inda yake, hakan yasa duk ya sha jinin jikinshi, kusan shi ta tsaya tana ƙarewa ƙasan shi kallo da kuma kyakyawar fuskarshi da take ganin idan har ya bata haɗin kai za ta mayar da shi babban yaro, hakan kuma ba ƙaramin fito da asalinshi na buzu zai yi ba, dan ko tambaya babu da Kaga Jabir ka ga mahaifinshi ka san mahaifiyarsa ce duk ya ɗauko, hatta da gashin shi mai saurin tsayi da mummurɗewa.
Cikin wani irin salo da fara buguwa da abubuwan da take sha tace "Jab..ir, zo muje ciki..muyi magana."
A ɗarare Jabir da duk tsoron lamarin matar ya kamashi ƙara ja baya yayi sannan yace "Idan wani abu zan siyo miki ki kawo kuɗin."
A nutse ta sake matsawa daf da shi shima kuma ya ja baya tana cewa "A'a Jabir, ba abinda za ka siyo min, ni da kai ne nake so..."
Yadda take ƙoƙarin ɗora hannun ta a sashen da ko ubansa baya so ya kai nashi hannun a waje bare kuma wani daban yasa shi saurin ƙoƙarin zagayawa ta bayanta dan inda take tsaye kamar ta tare ƙofar ne yana faɗin" Kiyi haƙuri, ina sauri ne zan kai ruwa wani wuri."
Kafin ta ankare ya fice a ɗakin da sauri ya tattara jarkokinshi ya yi gaba, ƴan matan biyu dake kwance ƙafafun samarin ne suka saka mata dariya inda ɗaya ke faɗin" Maganin ki kenan jarababiya, ke in ba ɗaukar hankali ba ina abun so yake ga yaron can almajiri? Gashi yanzu a banza ya wulaƙantaki."
Tsaki tayi tare da komawa inda take ta zauna, hakan yasa É—aya daga cikin samarin ya kalle ta yace" Tunda mu mun kasa yi miki yadda kike so ai sai ki bishi ko, na rantse da Allah yau sai kin bar gidan nan."
Harara ta dalla mishi tace" Ka ga ba ruwan ka, ba kai ka kawo ni ba dai."
Cike da gadara yace" Bani na ne ba, amma shi wanda ya kawoki ai ni na kawoshi."
ÆŠaya daga cikin Æ´an matan ne tace" Kinga kedai yanzu kiyi shiru, kai ma kuma ka bar cewa za ta bar gidan nan, ka san ku kuka gayyatomu tun daga garinmu, ina ta sani nan da za ta je?"
Cike d takaici saurayin yace" Ta san da haka ita shine zata maƙalewa wani yaro, dama zuba mata idanu nayi naga tsiyarta, ina abun burgewa yake a jikin yaron can? Ina ma abinda zai iya ɗura mata bare tasan har an shigeta? Kawai gantalewa ce irin taku ta ƴaƴan tasha?"
Cikin faÉ—a da takaici ita ma budurwar tace" Na gaya muku ba ruwan ku dani, rayuwa ta ce kuma zanyi abinda nake so ne, dan kun gayyatomu ai ba auren mu kuka yi ba da zaku hanamu kula wasu, kuma Jabir ni naga abinda na gani a jikin yaron, Shiyasa nake so na reneshi dan ya zama tamkar bawana ni kaÉ—ai, idan Kaga ba zaku iya ba ku sallamemu mana muyi gaba."
Caaaa! Ƴan matan suka yo mata suna faɗin me yasa za ta ce a sallama su? Nan ɗin fa ga wuta, ga ruwa, ga abinci wanda ransu yake so shi suke siyo musu, kuma ba dafawa suke ba a gyare ake kawo musu shi, gidan kuma idan suka koma me zasu yi? Ɗaya daga cikin su kawai gidansu ke da wuta, amma dukansu babu mai tabbaci zai samu abinda zai ci da rana idan ya gama cin na safe.
********************
Ummu ta kalla tana saka hijab ɗin ta tace "Bari in leƙa in ga idan Arɗo ya dawo daga kiwon, ina so ya siyar min da akuya ɗaya sai muyi walimar bikin da ita."
A kunya Ummu Kulsum tace "Mama, ba zaki bari gobe da safe sai kije ba? Ko kuma ni ki turani tunda kinga fa sai jibi ne zaki fita daga takaba, kuma fitar nan ba dole bace."
Murmushi tayi tace "A'a Ummu, ina zamuyi wannan abun kunyar, ke da zuwa cinikin akuyar bikin ki? Bari dai ni na je ai ya zama dole."
Jinjina kai Ummu tayi tace "To Mama sai kin dawo."
Jinjina kai ita ma tayi tare da kallon Nabila dake kwance tace "Shanshani uwar yawo, idan na fita kuma ki fice kema."
Dariya Ummu tayi tana kallon Nabila data turo baki gaba tana gunguni tace "Karki damu Mama, ba za bari ta fita ba ma."
"Shikenan to." Ta faɗa tana ficewa daga tabkeken gidan, Nabila na jin haka ta tabbatar Ummu ba zata bari ta fita ba, kuma gaskiya tana so ta fita dan wannan kullen da aka mata yau dake ba makaranta ba ƙaramin taɓata yayi ba, bata leƙa gidan samarin nan ba yau, kuma dama tana musu ƴan aikace aikace irin su shara, gugar ɗaki da siyo wani abu, wani lokacin ma idan suka siyo nama ko ƙwai ita suke ba ta sarrafa musu ita ma ta ci ta ƙoshi, ga kuma kyakyawan biya da saurayin ke yi mata wanda take ganin yanzu yana sakar mata fuska sosai da kulawa da ita, to kulawa mana, tunda komai suka ci sai ya aje mata ko bata nan.
A hankali ta tashi daga kan tabarmar tana faÉ—in "Aunty Ummu gyara daga nan na É—auko kayan shinfiÉ—a."
Kallonta Ummu tayi dake duba littafinta na siratul-nabawiy tace "Tun yanzu zaki kwanta yau?"
"Umm." Ta faɗa tana shigewa ɗakin, a tsanake ta dinga fito da kayan tayi shinfiɗa Ummu na karatunta, tana idawa ne ta ɗauki buta sai ɗan kwali a kanta ta shiga banɗaki, sai dai tana shiga tsaf ta fito cikin sanɗa ta zagaya ta bayan bukkar su Lukman dake suna kusa da ƙofar shigowa ne ga kuma duhu ta wajen su dan fitila ɗaya ce mai bada haske duka girman gidan, hakan ya sa Nabila ficewa daga gidan ba tare da Sanin Ummu Kulsum ba.
Yana hanyarshi ta komowa gida cike da taraddadin masifar da zai sh gurin matar Baban shi saboda daren da yayi, kuma hakan ya samo asali ne sakamakon fita da amaryar nan tayi dan haka ita bai kai mata ruwa da rana ba sai yanzu mijin ya nemoshi ya ce ya kai musu, sai kuma ya samu su Lukman na shayar da dabbobin ƙanin mahaifinsu Arɗo ga kuma wasu suma zasu ɗibi ruwan.
*Nabila* ya gani tana fitowa daga gidan nan, da mamaki ya shiga binta da kallo tana gabanshi yana binta a baya kamar a tare suke, duk da ba wani abu da ke haÉ—ashi da mutanen gidan, Mujittafa ne kawai suke gaisawa har sukan iya tsayawa suyi hira, amma ko lokacin da yake aiki tare da margayi idan ya shiga gidan dan kai masa kayan sana'arshi, ko kuma ya aiko shi ya kawo musu kuÉ—in cefanai ko idan an raga abincin ya turo ya kawo musu, sannu kaÉ—ai ke haÉ—ashi da yaran. Dan haka yanzu ma bai ce mata uffan ba har tayi gaba shi kuma ya shiga gidan su da sanÉ—a saboda rashin sanin abinda zai tarar.
Gabaɗaya ƙofar farfajiyar ya tarar a rufe, dan haka ya ɗan ɗaga hannu ya bubbuga ƙofar a nutse, shiru ba motsi ba kuma alamar za'a kula shi, dan haka ya ci gaba da bubbugawa a nutse da tunanin tayi bacci, ko kuma tana uwar ɗaki suna waya da mahaifinshi, dan in suna wayar nan bata jin komai da kowa.
Ya ɗan jima yana bubbugawa kafin ta taso ranta a ɓace cike da masifa tace "Wanene?"
A ladabce sosai cikin ruwan sanyi yace "Aunty ni ne."
Cike da gatsali tace "To sai aka yi me? Ka dawo daga gantalin ne yanzu ka zo in buɗe maka ƙofa? To bari kaji yaro, wallahi daga yau na zo gidan nan baka nan rufe ƙofata zan dinga yi, dan ni ba ƴar iska bace da zan dinga jiran sanda ka dawo sannan na rufe ƙofata, unguwar nan da mutum ma tsaf za'a yankashi har yayi mushe ba wanda ya sani, shine zan kai ƙarfe goma ban rufe ƙofa ba?"
Duk ratatun masifar nan da take idanunshi a lumshe suke, ga gajiya a tare dashi, ga matsanancin bacci, ga kuma rashin son hayaniya a rayuwarsa, cikin nutsuwa ba tare daya buɗa idanunshi ba yace" To aunty, kiyi haƙuri dan Allah, ba zan ƙara ba daga yau."
Wani dogon tsaki taja tare da faɗin" Ka ma ƙara mana, dan yau ba za'a kwana min gida ba, ko ka koma inda ka fito, ko kuma ka kwana a nan."
Jin takon tafiyar ta alamar tana komawa ciki yasa shi saurin cewa" Aunty Dan Allah? Dan girman Allah ki buÉ—e min, wallahi ba zan sake kai magriba a waje ba."
Bata kula da tsiyarshi ba, hasalima sai ji yayi tana rufe ƙofar ɗakinta sannan ta kashe wutar waje, wanda hakan yasa ɗan hasken ma da yake gani ya ɗauke, ajiyar zuciya ya sauke yana tunanin mafita, ina zai je? Wa ya sani? Wa zai bashi wurin kwana? Idan ya kwana nan a tsaye kenan? Cikin gidan ma ya aka ƙarata da miyagun ƙwari bare kuma nan farfajiyar da duk shukoki suka fito tamkar wata gona saboda damina da ta soma wucewa ma.
*Dalilin* zaman da yayi a farfajiyar gidan a wannan dare saida ya kashe wani ƙwaro da ake kira namijin kunama har guda biyu, sanin cewa duk inda aka ganshi to tabbas kunama na kusa yasa bai yi zaune ba sai kai da kawo, sai ya gaji ne yake jingina a bango har sai bacci yayi kamar zai ɗaukeshi sai ya farka. Abun ka ga bacci ɓarawo sai da ya zaunar dashi nan ƙasa ya ɗora takalmin shi ya zauna ya haɗa kai da guiwa, a cikin baccin nan daya kwashe shi mai daɗin gaske saboda gabatowar asuba kawai yaa zabura yana salati tare da miƙewa tsaye yana duƙawa da sosa damtsen ƙafarshi da ya ji an tsikareshi.
Duk dubawarshi bai ga wani abu ba da zai ce shine ya cijeshi, kuma gashi ba cizon cinnaka ba, jin an fara kiran sallah sai kawai ya juya ya bar gidan, fanfon gidan su Ummu ya je yayi alwala ya nufi masallaci, sai dai har lokaci yana sosa ƙafarshi saboda tsira masa da take.
*Bayan Kwana HuÉ—u*