← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 168

Sashe 48

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shigar shi ke da wuya Aisha ma ta shigo falon, bayan kyau da ta ƙara da sheƙi da fatar ta keyi wacce Mamanta ta ɗorata a salon shafa mayuka masu gyara jiki kamar dai ita, har da ƙiba ta ƙara ga kuma wayewa da ta samu a ƙanƙanin lokacin nan. Sanye take da abaya kalar ja mai duhu mai duwatsu sosai da kallabinta ta yane kanta da shi, sai takalmi masu tudu da sukayi kala da rigar tana goye da jakar makarantar ta a baya sai babbar wayar ta a hannu, cikin nutsuwa tayi sallama kusan mutanen falon suka amsa. Idanun Mama Nuriyya na kanta har ta ƙarasa kusa da ita tana kallon inda Abida ke zaune kan kujera Hajia Kaka ta gama mitar ta ƙi zama kan katifa wai ita ai a ƙasar waje ta haihu duk ba buƙatar wannan al'adun, da fara'a Aisha tace "Aunty ina wuni, ya baby?"

Saida ta ma Aisha wani kallo mai kama da harara, kafin ta kawar da kanta a yatsine ta amsa da "Lafiya lau, gaya nan yana ta bacci."

Ba tare da damuwar komai ba Aisha ta maida duban ta kusa da mamanta tace "Mamie, na gama shiryawa zan tafi, sai na dawo."

Hannunta Mamie ɗin ta riƙo a hankali ta jawo ta kusa da ita sannan ta rumgumata jikin ta, cike da kulawa da ƙauna ta shafa bayan ta tana faɗin "Ki kula da kan ki Eesha, dan Allah ki dawo da wuri."

Ɗagowa Aisha tayi a tsanake ta zuba idanun ta a fuskar maman nata cike da ƙauna ita ma tana murmushi tace "Zan dawo Mamie, in sha Allah."

Sake tallabo kumatunta tayi da hannaye biyu ta manna mata sumba a goshi sannan ta sake ta, murmushi Aisha tayi tace "Nagode Mamie, saina dawo."

"A dawo lafiya." Mamie ta faÉ—a tana kallon Aisha data nufi inda Hajia ke zaune, tana zuwa ta É—an rumgume Hajiar tana faÉ—in "Mammie sai na dawo."

Da fara'a Hajia ta shafa bayan ta tace "A dawo lafiya, ki bige mana jarabawar."

Dariya Aisha tayi tana ficewa a falon bayan tabbacin da ta bata na zata ci in sha Allah, a ƙofar falon ta samu dreba na jiran ta ya faka motar yana zaune ciki, fitowar ta tasa da sauri ɗaya jami'in da Abbu Mukhtar ya ɗauke shi kawai dan fita tare da Aisha a duk inda zata je saboda a kullum gani yake za'a ƙara raba shi da ita ya buɗe mata mazaunin baya ta shiga ya mayar ya rufe sannan shi ma ya buɗa gaba ya zauna, a hankali yake tura hancin motar har suka fita daga makeken gidan.

*******************

Ƙara riƙe rigar shi tayi gam tana girgiza kai cike da shagwaɓa tace "Ni dai wallahi a'a, haka kawai kana so a ce ina saka aiki, kawai ni ka bari zan yi da kaina, idan wani ya gani fa to?"

Murmushi kawai Alhaji keyi yana kallon ƙafafun da take ta dirawa ba ta ko jin nauyin cikinta da ya tsufa yake wata na takwas yace "To ni nace wani ya ganni ne? Kuma me ye a ciki dan na taimakawa amaryata? Ke baki ga halin da kike ciki bane."

Turo baki tayi gaba tana faÉ—in "To ai dai zan iya da kaina ko."

Girgiza kai yayi shi ma yace "Ban yarda ba, ina zaki iya É—aukar wannan katifar ki kai falo?"

Cikin jin haushin da tunda ta ɗauki ciki ya zama sabon ta ta saki rigar shi ta ja baya tana ɓata rai tace "To shikenan, na fasa kwana a falo ma."

Dubanta yayi da kyau sai ya matsa da niyyar jawo ta jikin shi, ƙara ja baya tayi tana faɗin "Karka taɓani ni, kawai ka bar shi."

Sake matsawa yayi kusanta dan yasan le hakan ke nufi yace "Wai har kin yi hushi?"

Da sauri ta kalle shi ta galla mishi harara sannan ta juya a hankali ta shiga takawa zata bar É—akin, murmushi yayi ya bi bayan ta yace "Kinga to zo É—aukida kan ki, shikenan?"

Ba fa alamar wasa tace "Ka bar shi fa nace na fasa." Dariya yayi ya bi bayan ta har suka isa falo ta zauna kan kujera tare da miƙe ƙafafun ta, tsugunnawa yayi gaban ta yana kallon fuskar ta ya riƙe hannun ta yace "Haba mana Ummu, kiyi haƙuri kin ji, indai nine na daina gardama dake daga yau, shikenan?"

Ƙala bata ce mishi ba kuma bata saki fuskar ta ba alamar ta huce, jinjina kai yayi yace "Shikenan tunda ba zaki haƙura ba, bari na kira Mama na sanar da ita kina hushi dani..."

Duk da ya kai ƙarshe da sauri ta kamo hannayen shi ta hana shi tashi tana turo baki tace "Shikenan to na daina hushin, kasan da Mama na iya ɗauke fuskata da mari ba ruwanta fa."

Komawa yayi ya durƙusa yana shafa cikin ta da bai da wani girma sosai, ko dan tanada tsayi ne? Ko kuwa dai girma ne abinda ke cikin ta baya da? Amma ba dai rashin ci ba, dan alhamdulillah tana ci sosai sai dai idan bata ga abin cin ba. Cikin rarrashi yace "To yanzu na ɗauko miki katifar?"

A hankali ta ɗaga kai alamar e, miƙewa yayi yana murmushi ya nufi ɗakin, ƙarar da wayar shi tayi yasa shi da ita suka kalli wayar, agogo ta kalla dan ita dai tasan dare yayi sosai, shaf ta manta da mai kiran shi a kullum a wannan lokacin, saida ya dawo yana ɗaukar wayar tare da cewa "Ke ma dai, har sai kin kalli agogo? Bayan kinsan Jabir ne."

Sai kuma tayi murmushi tace "Hakane fa?"

Ɗaga wayar yayi suka shiga gaisawa a tsanake shi da Jabir wanda tun tafiyar shi kafin Alhaji Kabir ya kwanta bacci sai ya kira shi ya mishi saida safe, haka kuma gari na wayewa a nan zai kira ya mishi ya tashi lafiya ko da can wajen su dare ne, hakan yasa Alhaji Kabir na ƙara ƙaunar Jabir ɗin, shaƙuwa kuma ta sake shiga tsakanin su kamar dai ɗa da uba.

Ganin hirar tasu na yin tsayi dan a yadda ta kula labarin abubuwan dake faruwa game da karatun shi yake bashi, kuma cikin nutsuwa da bashi kula yake sauraren shi, inda ya kamata ya bashi shawara sai ya bashi, inda kuma taimako zai mishi sai ya ce zai yi kaza, saida suka gama hirar su tsaf kafin ma Jabir ya ba wa Aliyu wayar ya gaisa da mahaifin nashi shi ma, lokacin kuma har Ummu ta ɗauko katifar ta fara shinfiɗa, dan kwana biyun nan ne bacci a gado baya mata ɗaki, shine wata mata a wajen awo ta bata shawara ta jaraba kwana a katifar ƙasa.

******************

Wani sabon mamakin ne ya sake lunluɓe tsohuwar har ta riƙe haɓa tana kallon shi tace "Mu'azu, da gaske wai takanas ta Kano ka ɗauko hanya ka zo nan dan kawai ka ga ko Jabir yana nan? Bayan ni na faɗa maka ban gan shi ba nima."

Sunkuyar da kai yayi a ladbce yana shafa kanshi yace "Ba haka bane Ayya, wallahi na damu ne sosai da ɓacewar Jabir ɗin, abu kamar wasa fa kun ga har ana neman shafe shekara da barin shi gida, shine da muka yi magana da aminina Alhaji Hisham yake faɗa min ko dai yana wajen ku, ta yiwu kuna son horani ne, shine kawai sai naga bari na zo bazata, wataƙila haka ɗin ne."

Taɓe baki tayi tace" To ai ko in gaya maka ka tabka asarar kudin mota Mu'azu, dan Jabir kasan ko karan hauka ya cije shi ba zai zo inda nake ba, dan haka ka je can ka nemi inda ɗan ka yake."

Tana gama faɗa masa haka ta miƙe tayi ɗakin ta tana mitar ba dai Jabir ba Alka, kar ma ya ɓata mata rai tana zaman zamanta mana, da kallo ya bita, sai zuciyar shi ke raya mishi wai ita da gaske bata damu da ɓatan yaron shi ba? Yaro kamar Jabir mai nutsuwa da hankali, a ce an neme shi ɓat an rasa, kuma shi ba ƙaramin yaron da za'a ce ya ɓata hanyar zuwa gida, kenan yanzu idan ya fahimta dai *shi ya rasa Jabir*? Tunda gashi hatta da kakanin shi babu wanda yake ko da kiran shi ya ji y nan ina ? Ko da yake laifin shi ne.

********************

Tsaf ta kammala jarabawar t ta fito tana goya jakar ta a baya, har ta tunkaro mota jami'in tsaron nan ya buɗe mata ƙofa kanta a ƙasa tana duba wayar ta, saida ta zo daf da motar ta ji muryar da ta jima bata ji ba, muryar da take yawan hana ta sukuni, muryar da zata iya cewa tayi kewar mai ita sosai, kuma muryar wanda take jin haushi idan ta tuna abubuwan da ya mata, idan ta auna su a sikeli sai ta ji ranta ya ɓace ƙwarai, sai ta dinga ganin komai kawai ya tafi ne yadda ya tsara shi.

Cikin wannan tattausan muryar tashi yace "Barka da fitowa."

Tsayawa tayi saboda jinin jikin ta da taji duk ya tsinke gaban ta kuma ya faÉ—i, saida ta É—auki sakanni a haka kafin ta iya É—aga kanta sannan t kalli inda ta fi jin sautin. Saida ta wara idanunta saboda ganin Sa'ad tsaye ya jingina a mota ya harÉ—e hannayen shi yana mat wani irin kallo mai ma'anoni da dama, murmushin da bata san da zuwan shi bane ya kubce mata, ba wani abu da y canja a tare da shi, sai ma kamar ramewa da ta ga yayi kaÉ—an, amma dai magana ta gaskiya yana nan a dogon shi kuma kyakkyawa, baya ga haka ya ci ado cikin É—anyen boyle kalar bleu mai haske ya mishi kyau sosai musamman ma É—inki daya kasance irin na Æ´an zamani.

Tuna cewa tana hushi dashi yasa ta kawar da duban ta izuwa gefen shi kaɗan tana haɗe fuska irin ohon nan, Sa'ad kuma daya fahimci ma'anar sai y saki murmushi ya fara takowa inda take, lura da hakan yasa jami'in nan saurin shiga tsakanin su yana ƙoƙarin tare shi, a daƙile tace da shi "Ka bar shi, na san shi."
Chapter 48 · 0% Book details