← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 168

Sashe 11

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai lokacin ya tuna bai ma leƙa dan gaishe da matan nasa ba kamar yadda yake yi, yasan kuwa biyu daga ciki za su ce amaryar da yayi ce ta hana shi zuwa gaishe sun. Ɗan gefe ya mayar da hannun Jabir sannan ya tare ta yana mata murmushi duk dan su zauna lafiya, shine ya fara da "Mamie Hayat barka da safiya? Har kin shirya za ki fita kenan?"

Yatsina fuska tayi tana ƙare masa kallo tace "Umm! Ina kwana ?"

Sai kuma ta kalli Jabir tana taɓe baki tace "Wannan kuma wanene? Mai aiki ka ɗaukowa amaryar ta ka?"

Ba tare da ya daina murmushi ba yace "A'a, ba mai aiki bane, wataƙila ma ya zama ɗaya daga cikin yaran gidan nan."

Sake taɓe baki tayi har da girgiza kai tana ayyana _"Sarkin kwashe-kwashe."_

A fili kuma hanya ta kama dan zuwa inda motar ta take mai gadi ya wanke ta sai walwali take, da kallo ya bita kafin y sake riƙe hannun Jabir ya shiga da shi inda suka fito. Ummu na tsaye da mamakin ina Jabir ɗin da kuma Alhaji sai gasu sun shigo da sallama, amsawa tayi tace "Dama fita kuka yi?"

Sakin hannun Jabir yayi yace "Shine ya tafiyar sa, Shiyasa na fita na dawo da shi."

Sai kuma ya kalli Jabir yace "Me yasa ka tafi wai? Ba ka yarda dani bane?"

Gumtse bakin shi yayi saboda ƙwallan dake cika masa idanu, da ƙyar ya buɗa baki cikin muryar kuka yace "Bna so na ske zama a garin nan, shiyasa na tafi."

Da azama da kuma son ƙurewa yace mishi "To ina za ka je?"

Saida ya ja majina ya haɗe wani kukan sannan yace "Ban sani ba, ni dai ko ina ne ma zan je, tunda Abbana baya ƙaunata, ya ce sai ya yi ajalina idan ya kamani saboda kawai nayi ga-ruwa dan na samu abincin da zan ci..."

Sai kuma zuciyar sa ta karye ya fashe da kuka tare da durƙushewa ya kifa kanshi a kujera yana faɗin" Ni na gaji da dukana da yake yi, ba wanda yake so na da shi da ahalinshi, ban san me na yi wa duka danginsu ba da basa ƙaunata, tafiya kawai zanyi na shiga duniya idan na zama babba na dawo."

A hankali Alhaji Kabir ya zauna kan kujera ya dafa shi, cikin sigar rarrashi da tausayawa yace "Jabir, so kake ka shiga duniya? Idan ka kangare sai ka dawo masa gida a matsayin gagararre? Ko kaÉ—an ban goyi da bayan ka akan haka ba, dan haka ka sake wata shawara ka ji."

Cikin shasheƙar kuka Jabir ya ɗago yace "Idan ma na koma yanzu ba zai haƙura ba, cewa yayi fa ajalina zai zama, dan kawai na nemi abinci? Baya hira dani, baya min dariya, baya min komai da uba yake ma ƴaƴansa, ɗinki kawai ke shiga tsakanina daa shi shima kuma daga ƙaramar sallah ne zuwa wata ƙaramar sallah, sallahn da ta wuce ma cewa yayi ni na haƙura aunty ta ce wai dole ya ma Uzeifatu kaya masu tsada, haka ina kallo su sukayi ni kuma na saka tsofaffin kaya, dan Allah wane uba ne yake wa ɗan sa haka ABBA?"

Kallon shi Alhaji Kabir yayi yace" To idan baka koma wajen shi ba Jabir ina zaka je yanzu? Ba ka da Kakani ne ko wasu Æ´an uwan?"

Cikin sasheƙa da sigar tausayawa kanshi yana jan majina yace" Ina da su, amma duka ba sa ƙaunata, har kakanina ma da suka haifi Mamata ba sa sona."

Da yanayin tashin hankali Alhaji Kabir yce" To wai me yasa? Me ka musu da ba sa sonka?"

Saida ya share hawayen dake zubo mishi sannan yace" Kakata da ta haifi Babana wai bata so ya auri Mamana ba, shiysa bata son ta nima kuma haka, Kakanina kuma da suka haifi Mamana sun yi hushi ne da Abbana saboda bayan rasuwar Mamna ya karɓeni pouta ce shi zai kula dani saboda baya so tarbiyata ta lalace, suma shine abinda ya ɓata musu rai suka ce har abada ba su ba ni, idan mun haɗu a titi na gaishe su zasu amsa, idan ban gaishe su ba kuma ba ruwansu dani suma."

Jiki a sanyaye Ummu ta zauna kan kujera tana faÉ—in" Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! To su duk basu damu da yadda rayuwarka za ta kasance ba? Kowane manufar sa ce kawai ta dame shi?"

Kallon fuskar Ummun yayi, a sanyaye ya jinjina mata kai alamar ohon musu! Alhaji Kabir ma da ranshi ya gama ɓacewa ƙwarai da gaske ne ya dafa kan Jabir yace" Jabir, ba kana karatu ba?"

ÆŠaga kai yayi yace" E."

Jinjina kai yayi yace" Kuma ai nasan kana da buri ko?"

Nan ma gyaÉ—a kai yayi har da É—an murmushi yace" E."

Shima da fara'a yace" Uhum! FaÉ—a min naji me ye burin ka ?"

Saida ya faÉ—aÉ—a murmushin shi ya kalli fuskar kamalar Alhaji Kabir sannan yace" A rayuwata, ina so naga na zama *malami* mai faÉ—akarwa, sannan ma ina so na *dogara* da kaina."

Daddaɓa kafaɗar shi yayi da jin daɗi yace" Da kyau Jabir, yanzu ka san me zamuyi?"

Girgiza kai Jabir yayi alamar a'a, dan haka ya ɗora da" Ka fara cin abinci, zuwa dare idan na dawo zamu sake tattaunawa da kai, lokacin na gama yanke hukuncin abinda ta kamace ka, amma ka sani ba zamu bari rayuwarka ta lalace ba, mun godewa Ubangiji da ya tseratar da kai a baya da yunwa ko takura basu saka fara wasu mugayen halayen ba har ka zaɓi kayi sana'a dan ka ciyar da kanka, amma daga yanzu b zamu bari ka sake zubar da hawaye ba, kaji ko?"

Jinjina kai yayi a É—arare yana kallonshi yace" Amma ABBA bana son zama a nan, Abbana zai iya ganina wata rana."

"In sha Allah ba zai ganka ba, Jabir idan har ka amince da abinda nake tunani a kanka, mahaifinka ba zai sake ganin ka ba a ƙasar nan sai bayan wasu shekaru."

Jinjina kai kawai yayi inda Alhaji Kabir ya tashi, UMMU ma kawo masa abincin tayi sannan ta bi bayan Alhajin, sai dai duk son ta da Sanin me yake shirin aikatawa bai gaya mata ba, ya dai ce ta jira har ya dawo za ta ji kuma za ta gani.

*ME CE CE DAMUWAKI*?

Rashin ni'ima?
Rashin gamsar da mai gida?
Bushewar gaba?
Zubewar nono?
Cikowar nono ?

*Kina buƙatar...*

Fatarki tayi laushi?
Tayi santsi?
Ta kwanta luf?
Kina walkiya da annuri tamkar amarya?
Sabulu kike so ko haÉ—in shafawa ki wanke ko mai na shafawa?
Ki wadatu da sahihin ƙamshin haukata mai gida?
Humra da zaki saka mijinki bacci bai shirya ba?
Humra da zata tayar da sha'awarsa?
Kulaccha da zata saka mijinki ya kasa yi miki tsara a fannin ƙamshi?
Kulaccha da zata gagari manyan mata suffanta kalar sunan turarenki?
Turaren wuta irin na asali barebari?
Turaren da zaki fesa à zanin gadonki har ya rike mai gida ya kasa tashi?
Turaren da zaki zuba ga ruwan wankan mai gidan ki?
Turare don yaranki?

_Idan duka kina buƙatar ɗaya daga cikin kayan nan, to ki tuntuɓi wannan lambar ta WhatsApp *+227-82-21-91-74* wanda suk gwada sun san ingncin kayanmu, ba buƙatar ɓata lokacin cika muku baki._

Wani abun farin ciki kuma, duba da yanzu ba kowace mace ke son shan garin magani ko matsi ba, akwai haÉ—i irin su *tsumi*, *ruwan tsumi*, *tukunya*: dayawa sun san tukunya, don da itace muke tutiya, kuma tukunyar nan akwai na ruwa dana dafawa a nama, sannan akwai kankat wato haÉ—in *kayan marmari*.

*Garaɓasa*

Ga waÉ—anda sukayi nisa kuma haÉ—in kayan marmari ba zai kamacesu ba, duba da kafin sakon yaje garesu zai fara lalacewa, don haka ga sauki ya samu, madadin kuÉ—in mota da zaki yi, zaki biya 1000k kacal don a sanar dake yadda zaki had, ba iya guda kawai ba, dama sauran haÉ—i irin na kayan daya shafi na marmari da É—anye, musamman ma *sirrin kankana* da kuma *cucumber*.

*JANNAT HOUSE.*🧕

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HARUN*

*MURA'ATU ULTIMATE COLLECTIONS* shin kin zuba tagumi ne uwar gida da amarya da tunanin ta inda zaki haɗa kayan kitchen ɗinki? Ko kuma fabrics kike da buƙatar canzawa na kece raini a cikin sa'o'inki? Shin kina so ki san a inda gawurtattun mata ke haɗa nasu perfumes ɗin? Ko lausasan zanen gado da kyawawan electronics gama hawa kike da bukata? To Matso kusa, zan faɗa miki inda ba ke kawai ba, hatta mai gidanki zaki iya rakawa dan siyo nashi electronics ɗin da sauransu, wato *MUC* mun shahara a saida Kayan *kitchen*, *fabrics* na kere sa'a masu quality, *bedsheets*, *electronics*, *beauty products*, *perfumes* da *kayan kwalliya* . Bugu da ƙri Hajia ta akwai data tare da *katin waya* ta kowane network and *catering services*, da wannan nake cewa daku, sai an gwada akan san na kwarai. *MUC* 🤝🤝🤝🧕BAMU DA SA'A.

Ga mai buƙatar tuntuɓarsu, ga lambar WhatsApp: 07038274166

Call: 07038274166 & 07031057802

Location: Kano with nationwide delivery.

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*5*

Hasken da ya fara mamaye gari da kuma wata irin yunwa da ƙishin ruwa da suka sako shi gaba yasa shi ƙarasawa jikin wani tabkeken gida da kai daga gani a waje da ido kasan gidan wanda suka tara abun duniya ne kamar su kaɗai ke nema, cikin sa'a yana kawowa daf da gidan sai ya samu fanfo, da sauri ya ƙarasa ya kunna fanfo ya fara wanke hannayen shi sannan ya tarasu ya sha ruwan sosai da burin su cika masa ciki ko yunwar nan za ta bar shi yayi tunanin abun yi.
Chapter 11 · 0% Book details