← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 168

Sashe 87

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A daƙile cike da gadara Hajia ta dube ta tare da ɗaga hannu tace "Bar shi kawai Nuriyya."

Sai kuma ta kalli inda Nabila take zaune kanta ƙasa har lokacin, Fahad dake ta zabga murmushi yana tsaye ne ya kalli Hajia da tunanin ko akwai wani tanadi da ta ma Nabilar da ya sa ta dakatar da Mama Nuriyya, zaune yayi kusan Nabila yana duban su Hajia da Mama Nuriyya yace "Mamiena, aunty Nur, aunty Fa'iza, ga Nabila."

Murmushi kawai Nabila tayi tana ƙara sadda kan ta ƙasa, Mama Nuriyya ce ta sake yin murmushi tace "Ma sha Allah, Nabila, sannun ku? Tubarkallah da ita kuwa."

Cike da jin daÉ—i Fahad yace "Nagode aunty Nur."

Murmushi ita ma tayi tace "Ba komai, Allah ya tabbatar mana da alkairi."

Da wani sabon farin ciki ya sake amsawa da "Ameen aunty Nur."

Shiru É—akin ya É—an É—auka na sakanni, hakan ya ba Fahad damar kallon Hajia da ba ta ce komai ba sai kallon Nabila yace "Mamie... Ga Nabila."

Ƙafa Hajia ta ɗora kan ɗaya tana ci gaba da kallon Nabila tace "Na gani, Nabila ko?"

Sai kuma tayi murmushi ta kalli Nabila tace "Ki É—ago kan ki mana, mu ne fa, ko baki gane mu bane? Jiya ai kin zo nan muka gaisa ko? Kuma naga jiya ba haka kika zo mana ba."

Wulwula idanu Nabila tayi da kanta ke ƙasa gabanta ya fara faɗuwa, Fahad ma dai jikin nashi ne ya fara wani yanayi saboda sam bai tsammaci haka zai iya faruwa ba. Kallon shi Hajia tayi tace" Fahad, ka samu Bilal a ɓangaren shi, ka ce ya zo ina son magana da shi."

Kallon Hajia ya yi, sai yake jin baya da nutsuwa ko kaɗan, amma sai ya kasa musa mata musamman ma da ya yi alƙawarin zancawa, dan haka ya miƙe ya tafi zuciyar shi ba daɗi yana kuma jin kamar akwai wani abu, saida ta ga ficewar shi ta saki wani murmushi. Zama Hajia ta gyara sosai cikin wata dakakkiyyar murya tana kallon Nabila tace" Ke! Nabila."

Yadda Hajia ta kira sunan ta ya fi ƙarfin ta share, dole ta ɗago kan ta ta dubi Hajia har ta amsa da" Na'am."

A kausashe Hajia ta furta" Kalle ni da kyau, bana buƙatar sadda kan ki a yau, ki kalle ni kamar dai jiya sannan kiyi magana da ni kan ki tsaye, ni ce mahaifiyar Fahad, amma ban da mahimmanci gare ki, tunda har kika iya zuwa min gida jiya kika yi abinda kike so."

Da yatsa ta nuno ta tana mai sake kausasa murya tace" Kina ji, bana son auren ki da Fahad, gaskiyata ce nake faɗa miki, ba kuma iya ni kaɗai ba, har da mahaifin shi da ma duk wani dake gidan nan, idan kika auri Fahad a haka to sai dai idan za'a yi ɗaya cikin biyu, imma ki fuskanci ƙiyayya da muzgunawar mu, ko kuma dai kuyi nesa ku auri juna ba tare da albarkar mu ba, dan haka nake so in shaida miki ki fita a harkar Fahad, dan ba zamu yarda ki aure shi ba, mu ba mahaukata bane da zamu yarda haka ta faru bayan kun gama lalacewa a waje, dan haka ki cire shi a rayuwar ki, ki manta da shi gaba ɗaya."

Tana gama faÉ—a kuma mai aikin nan ta dawo, shine ta kalle ta tace "Kice Fatima ta zo."

*Fati* na fitowa ta same zaune tare kuma da baƙuwar fuskar d ba ta sani ba, dan haka a nutse ta ƙaraso tsakiyar falon, duk dai ba wani girma ne ta gani a fuskar Nabila ba, amma da ladabi ta kalle ta tace "Sannu, ina wuni ?"

Wani kallo Nabila ta mata irin ba ka hayyacin ka, gashi dai tana ji, kuma tana gani ma, kum har abinda Hajia ɗin ta faɗa ta fahimci abinda take so ta fahimta, amma dai jikin ta ya ƙi yarda da saƙon, sai take ji da kuma gani kamar Fahad ya kawo ta ne dama dan a faɗa mata haka. Hajia ce ta katse mata tunani sanda ta nuna Fati da yatsa sannan tace "Kinga wannan? Ƴar ƙanin mahaifin Fahad ce, ita ce zai aura nan da kwana shida masu zuwa, ki dube ta da kyau ki gani, shigar ta, kamalar ta, nutsuwar ta, tarbiyyar ta ba, ke har ma da nasabar ta duk mun gamsu da su, dan haka nake sake jadadda miki Nabila ki fita harkar Fahad, ba ta yadda zamu yarda ya aure ki, ku haihu yaran ki watarana su tambaye mu _da gaske maman su ƴar shaye-shaye ce_? Ban shirya ba wa ɗan uban kowa wannan amsar ba, dan haka can ki ƙara ta da tsiyar ki, yanzu tashi ki fice min a gida kafin Fahad ya dawo."

Saida Nabila ta runtse idanun ta, kuka wanda za ta iya kira da kuka, irin kukan nan da ake cewa daga zuciya yake, shi ta ji tana yi a lokacin, ƙwarai hawaye da take jin ana faɗa masu zafi, ba ta sani ba ko rasuwar mahaifin ta tayi kuka irin haka, dan gaskiya bata da cikakken wayon da za ta fahimta, amma dai bayan shi bata taɓa kuka irin wannan ba, tun daga irin dukan da Yaya Luƙman da ma Yaya Mujjittafa suke mata, zuwa faɗan da Mama da Ummu ke mata, har kan faɗa da cin mutumcin juna da suke da Fahad, zuwa ga ranar farko ma da ya fara keta mata mutumci, duk babu ranar da ta ma irin kukan nan da take jin yanzu yana taho mata kuma ba alamar tsayawa.

A hankali ta buɗa idanun ta sauke kan ƙafafun Fati dake tsaye tana kallon ta da tunanin dama ita ce budurwar Fahad ɗin? To me yasa Hajia ke faɗa mata haka? Ai kamar bai dace ba ko? Hakan yasa Fati ta ji ta tsargu sosai, sai take fatan Allah ya sa dai ba iya wannan dalilin bane kawai ya sa aka gayyato ta gidan nan, dan tunda ta zo bayan gaisuwa da wasu tambayoyi bakin su bai ƙara haɗuwa da na Hajia ba, dan magana ta gaskiya ahalin Ahlan akwai wani abu da ake kira wai shi *isa* da *gadara* gare su, ba dan komai ba sai dan kuɗi da Allah ya basu, shiyasa duk alaƙar su wallahi ba ta shiga shirginsu sai in da dalili mai ƙarfin gaske.

Ƙwarai Nabila kan dogaten ƙafafun Fati ta fara sauke duban ta, zuwa surar ta dake cikin wani shanɓareren hijab mai hannaye, fara ce tass da ita fiye ma da Fahad, kuma ba za ka ce mata mummuna ba gaskiya, dan tana da idanu da matsakaicin baki, gashi fuskar ta ma ba kwalliya sai kamala da kuma tabon sallah dake manne a goshin ta ya yi baƙi. Ƙwarai wannan ta fi dacewa da Fahad, ƙara lumshe idanu tayi wasu hawayen suka sake zubowa har wasu na korar wasu, jiki a sanyaye ta miƙe da wani irin ƙwarin guiwar jin ta haƙura da Fahad kenan har abada, ko da kuwa shi ne autan maza, ko kuma soyayyar shi za ta kashe ta.

Ba ta waiwaya gare su ba, ba ta kalli kowa a cikin su ba ta kama hanya tana share hawaye, tana kai wa ƙofa Fahad na shigowa suka haɗe, ba tare da ta goge hawayen ta ba take kallon shi kamar yadda yake ta tsare ta da idanu yana aika mata da tambayar kukan nan fa? Ina kuma za ta je? Cikin sanyayyar mrya yace "Beela, me aka miki kike kuka? Ina za ki je ?"

Cikin kakkausan murya amma a tausashe tace "Ba komai kawai, ka je wajen Maman ka tana neman ka."

Raɓa shi tayi za ta wuce da azama da yanayin tashin hankalin da ya fara ziyartar shi na hango wasu abubuwa dake bayyane, tura shi kiran Yaya Bilal da shia yaje can ya tsare shi da wasu maganganu marasa kan gadon da basu shafe shi ba, zuwa yanzu da yake ganin Nabila na kuka haka, tattausan riƙo ya ma hannun ta yace "Me ye? Me aka miki? Faɗ..."

Fizge hannun ta tayi, sannan ta sa hannu da ƙarfi kuma cikin ɓacin rai ta tura shi gefe har ya kai wa bango karo, sannan ta nuna shi da yatsa tace "Kar ka sake taɓa jikina Fahad, ka fita a rayuwata dan Allah, daga yau ka manta da wannan tantiriya kuma fitsararriyar Nabilan da ka sani a rayuwar ka, nima daga yau ba zan sake ta'ammali da mai irin sunan ka ba ma bare na tuna da kai a rayuwata, dan haka ka rabu da ni ka je ga zaɓin iyayen ka."

A haukace ta taka ta fice daga falon, sai kuma ta tuna wata magana da bata faɗa mishi ba, hakan yasa ta juyowa ta dawo da ƙarfin tsiya, yayin da shi ma Fahad ya sake aniyar bin bayan ta, hakan yasa suka kusa yin karo da junan su, nuna shi ta yi da yatsa tana wani bahagon murmushi tace "Kasan me? Ni shashasha ce, da nayi tatoo saboda kai har na rubuta sunan ka, sannan na aske gashin kaina duk saboda kai, sannan na canza suffata ta asali duk dan ka ji daɗin mu'amala dani, amma daga yau komai ya ƙare, na manta da cewa ɗan duniya ba ya auren ƴar duniya kamar sa, sai dai mace irin waccen..."

Ta faÉ—a da nuno inda Fati ke tsaye, sannan ta É—ora da" Amma ka sani, mu ma iyaye ne suka haife mu, kuma da tarbiyyar mu kuke ganin mu, ku kuke ruguza mana komai, daga baya kuma ku watsar da mu, amma ba komai, mu zamu muku alkairi, sannan akwai ranar da zaku ji kunyar abin nan da kuka aikata, *Fahad Saheeb Ahlan*."

Taɓe baki tayi ta sake wucewa kamar iska za ta kwashe ta zuwa sama ta fice a gidan, inda Fahad kuma ya tsaya jin ba'asin me ya faru? Mama Nuriyya à ranta ta ji cewa yarinyar nan duk abinda ta faɗa da Hajia ne take ba Fahad ba, kuma gaskiya ta bata tausayi yarinyar sosai.
Chapter 87 · 0% Book details