Sashe 57
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ganin ta ƙi magana sai kawai ya jefar da zabgegiyar wayar da yake dukan ta da ita ya fito daga ɗakin tare da kulle ta daga ciki, yana zuwa ya ba mama makullin yana faɗin "Ki aje wannan mama, dan girman Allah kar ki bar yarinyar nan ta fita, wallahi Mama yau zan nemawa yarinyar can miji gobe sai an ɗaura auren ta, idan an kai ta ɗakin miji ta kashe kanta in za ta iya."
Nabila dake ji da saurare tasowa tayi jiki na mata rawa na raɗaɗin duka, amma a haka ta haɗa kanta da ƙofa tana cewa" Wallahi ba zan kashe kaina ba, amma shi wanda ka aura min sai na kashe shi, na rantse da Allah sai na kashe ko ɗan uban waye, idan ya so Kaga ni da kai duk sai a kama mu, tunda kaine silar mutuwar koma waye."
"Ke! Ni kik..." Ya faɗa tare da juyawa a zafafe zai sake komawa ɗakin, da sauri Mama ta riƙe hannun shi tana girgiza mishi kai, cikin sigar tausayi da kukan da tasha tace "Kar ka zma ajalinta Luƙman, bar ta da halin ta."
Jinjina kai yayi sannan ya sake miƙawa mama makullin ta karɓa, yana faɗin "Zan nemi yaron nan Fahad a duk inda yake, na gaji da iskancin da yake mana, ko ɗan waye shi wallahi zan masa kashedi akan ƙanwata, dan b..."
Bai ƙarasa faɗa ba Nabila daga ɗaki ta fashe da kuka irin mai ihun nan tana faɗin "A'a fa Yaya Luƙman, wallahi kar ka je ka zubar min da mutumci a idanun saurayi, kar ka same shi dan girman Allah, wallahi ajina zaka zubar."
Kamar zai mutu dan takaici haka yayi, sai kawai ya jinjina kai yana ci gaba da duban Mama yace "Ni zan wuce Mama, saina dawo."
Jinjina mishi kai tayi tace "Allah ya tsare."
Da "Ameen." Ya amsa sannan ya fita, shiru Nabila tayi ba ta sake magana ba, hasalima É—akin ta ta shige tare da tunanin hanyar da zata sake barin gidan, dan ya É—auke wayar ta ita wannan damuwa bace, kar dai ta haÉ—u da Fahad tasan zai siya mata wata, dan haka fitar ta ce kawai gaban ta.
Kiraye-kirayen sallah ya sa mama tashi ta ɗauro alwala, tana buɗe falon ta shiga ba ta gan ta ba, ɗakin ta ta kalla ta gane tana ciki, a sanyaye ta taka zuwa ɗakin, dake ba ƙofar rufewa labulen kawai ta yaye, kwance take ruf da ciki tana ta tunanin hanya duk da kuwa bacci take ji sosai, kamar yanzu ne ta fara ganin ta da wannan shigar haka ta sake bin ƙafafun ta dake sanye da takalmi ƙafa ciki farare, zuwa sarƙar dake ƙafar ta wacce ta fito sosai, dan wando dake jikin ta irin wanda ake tattarewa ne ya fito da ƙwabri sosai kamar dai irin wandon fulani, har zuwa kan ƙugun ta da aka yi sa'a rigar ta ɗage mata sai ta ga wannan zane mai kamar kore mai duhu alamar na gasken ne, ba wai rashin jigidar da ta san ta da ita bane matsalar, yadda ta ga kamar an zana hoton fuskar wata dabba, a hankali ta dinga cira kanta har zuwa kan damatsenta da suka fito fili sakamakon rigar siraren hannaye ne da ita, a hankali ta sake sauke duban ta kan wani zanen dake tsakiyar wuyan ya, duk da bata san me aka rubuta ba, amma dai nan rubutu ne aka yi da irin waccen abun da aka yi na farko.
Girgiza kai Mama tayi idanun ta na sake cika da ƙwalla saboda ganin askakken kan ta, yarinya mai gashi kuma gashin ma mai kyau Nabila take da, amma ta aske kan ta haka ya zama kamar na maza, wannan wane irin zamani ne aka shiga da maza ke barin ɗabi'ar su suna komawa ta mata, mata kuma na barin ta su su koma ta maza? Allah kawai zai mana maganin wannan matsala. A tausashe tace mata "Tashi kiyi alwala kiyi sallah."
Juyowa tayi ta fara kallon Maman kafin ta tashi zaune tana faɗin "To." A matuƙar sanyaye kamar dai ta nutsun.
Juyawa Mama tayi ta fita da ƙudirin idan sun idar da sallah ta zaunar da Nabila kamar yadda ta saba sannan ta mat nasiha ko Allah zai sa a dace, dan haka Mama ta shinfiɗa sallaya a falo ta kabbara sallah, Nabila kuma jiki a sanyaye ta fito falon ta kalli Mama dke sallah, ƙofa ta ƙalla t ga a buɗe, sai tayi murmushin ganin Mama har tayi halin na ta na mantuwa, ta bar ƙofar buɗe bayan an ce ta kulle ta kar ta fita, ko kuma dai yarda da ita ne yasa tayi haka tana gani ba zata fita ba? Ai kuwa Mama tayi kuskure, dan gaskiya fita zata yi ba kuma ta sa ranar dawowar ta ba.
Dama dai da takalmin ta a ƙafar ta, dan haka tana fita cikin sanɗa ta tura ƙofar gidan sannan ta fice ba tare da tasha wahala ba, tana fita da sauri da kuma waiwayen bayanta har ta isa bakin titi, kayan dake jikin ta sam bata ɗauke su a matsayin wani abu ba bare ta damu, dan haka ta samu adaidaita ta shige tare da faɗa mishi inda t nufa, hannu ta sa aljihu tana lalubo kwalin sigari dake aljihun wandon ta, abun kunnawa ta fara nema amma bata samu ba, tsaki taja tare da zago kara ɗaya na sigari tana faɗin "Shashanci, nasan ma na jefar da shi a can..."
Sai kuma tayi ƙwafa tace "Yaya Luƙman, wallahi ina ɗaga maka ƙafa, ka kiyayi ranar da zaka kaini bango."
Mai adaidaitar ta kalla tace "Abokina zan samu maƙyasta?"
ÆŠan juyowa yayi ya kalle ta, ikon Allah? Sai ya rasa amsar da zai bata wallahi.
Shi bai taɓa kwatanta rayuwar hayaƙi ba, akan me za ta tambaye shi? Tana mace, ba kunya ba tsoron Allah? La'ilaha illalah ! Girgiza mata kai yayi ba tare da ya ce mata komai ba, hakan ya hassalata tace "Ka ji ɗan rainin hankali, idan babu ka ce babu mana, me ye na tsayawa kana ƙare min kallo."
Tsaki taja tare da maida karan sigarin a aljihun ta tana ci gaba da kallon gari ta matsu su kai wurin sahibin nata ta sanar da shi abinda aka mata.
********************
Bacci take mai cike da mafarkai da shu'umin yanayin dake neman sakata yin ihu a cikin baccin ta har tana haɗe ƙafafun ta alamar abinda ke faruwa a mafarkin yana ratsata. Da sauri Kuwailat ta shigo riƙe da wayar Maman nata, tana zuwa da sauri ta daddaɓata tana faɗin "Ammie, Ammie gashi, Abba ne yake kira."
A nauyaye, a kasalance matuƙa ta buɗa idanun ta, kafin ta dubi Kuwailat ɗin dake tsaye a kan ta tana miƙo mata wayar, da ƙyar ta yunƙura tana tashi zaune tana furta "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un!"
Bata karɓi wayar ba sai kanta data dafe da ta ji ya sara mata da mugun ƙarfi, a tausashe ta ci gaba da nanata sunan Allah a bakinta dan ta ji daidai, da sigar ƙaguwa Kuwailat a ladabce ta sake faɗin "Ammie, ki karɓa kar ta tsinke, Abba ne."
Kallon fuskar yarinyar ta sake yi wacce take kama da ita kamar tayi kaki ta tofar, a hankali ta sa hannu ta karɓi wayar, sai dai kafin ta ma duba ta tabbatar Alhajin ne kiran ya yanke, hakan yasa tayi wani tsaki ta aje wayar kan gado tare da kallon Kuwailat a mugun raunane tace "Kuwailat, ban faɗa miki bana son kina tashina kai tsaye idan ina bacci kuma da hargagi ba?"
Sunkuyar da kai Kuwailat tayi kafin ta tausasa murya tace "Kiyi haƙuri Ammie, wallahi gani nayi Abba ne ke kira, wataƙila zai gaya miki ranar da zai dawo ne, kin san fa munyi kewar shi..."
Ta ƙarashe maganar da sigar tausayi, ƙura mata idanu Ummu tayi, taɓe baki tayi a hankali tare da gyara zamanta a kan gado tana gyara rigar baccin da kasala da damuwa yasa ta kasa cirewa gashi har azahar ta gabato, nauyayyar ajiyar zuciya ta sauke tare da sake duban wayar da aka ƙara kira.
Magana ta gaskiya *haushin Alhaji Kabir* take ji sosai, bata sani ba tana aikata zunubi ne haka? Amma fa abun daga zuciyar ta ne yake, ta kasa dakatar da hakan, fisabilillah a ce tana da miji, amma kuma sha'awa na neman halaka ta a cikin gidan nan, baya da lokacin ta saina harkokin shi, idan ma yana gidan tare da ita to ba tsiyar da yake tsinana mata, ai da ba haka yake ba, me yasa yanzu ya zama haka? Me yasa ya ke ƙin kula ta sai ya ga dama? Idan ma ya zo matan a sakanni kaɗan ya kawo nashi ruwan ya tashi ya bar ta? Ita abun ma ya fara fin ƙarfin ta, shekara sama da uku haka na faruwa, har yanzu ta zama sai yawan ɓacin rai da damuwa da kasala dake mugun damunta, dan haka ma yanzu bata wani damu da dawowar shi ba, indan ma ya zo ba abinda zai mata ai, wataƙila ma ranar da zai dawo ba ranar girkin ta bane, dan haka ba buƙatar ta san zai dawo ɗin.
A yangance ta É—aga kiran ta É—ora wayar a kunne sai kuma tayi shiru, Alhaji Kabir da shi kam har yanzu Ummu na nan a yadda take a zuciyar shi da fara'a da farin cikin abinda zai sanar da ita yace "Ummun gidana, hala girki kike ina ta kira baki É—aga ba?"
A taƙaice kamar wacce bata son maganar tace "Umm, ina wuni?"
Da sautin fara'ar shi ya sake amsawa da "Lafiya lau Ummuna, ya kike ?"
"Alhamdulillah." Ta faÉ—a bata sake cewa komai ba, fahimtar kamar tana cikin damuwa yasa shi rage karsashin dake tare da shi yace "Ummuna, kina lafiya?"
Saida ta zuro da ƙafafun ta daga kan gadon tana kallon ƙofar da Kuwailat ta bar mata a buɗe wacce ta fita tun da taji suna magana tace "Me ka gani? Lafiyata lau."
Da rashin kuzari ya sake faÉ—in "To ai naji kamar kina cikin damuwa ne."