Sashe 105
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mama da ta ga Mama Nuriyya na kuka sai gaban ta ya faɗi saboda tunanin da tayi, hakan yasa ta ƙaƙaro murmushi ta kalli Ummu da tsarguwa yasa tayi tsaye ta ma rasa ina za ta nufa, kallon da mutanen ke mata mamaki yake bata kuma yana neman hassalata, haka kurum mutane huɗu su tsare ta da idanu kamar mai laifi, kuma fa kowa da gaske kallon ta yake ba ko ƙyabtawa, abun takaici kuma daga matan har maza, hakan yasa suka sa ta fara tunanin to ko dai iskancin Fahad dama daga gida ya samo asali? Me ye a jikin ta da suke mata wannan kallon ƙare dangin? Wata alama suka gai da ta nuna ita wata ce? Ko kawai sun yi niyya ne dai? Dan ita dai tasan ba kyawun ta bane ya ɗauki hankalin su, dan duka matan biyu alamu ya nuna sun yi tashen kyau girma ne kawai, amma hakan ma bai ɓoye kyan su da tsari da kuma kula da jikkunansu ba, haka kuma tasan ba hasken fata bane, dan Mama Nuriyya jajir take wacce kana gani ka ga buzuwa ta asali, sauran ne ma duka suke da duhun fata, shima ba irin wanda ya munana ba.
Da fara'a Mama tace mata "Ƙaraso mana Ummu, ga Kuwailat can zata kawo abun sha."
Saida Ummu ta ɗan sake matsawa ta kalli fuskar Abbu Mukhtar, a wani irin sanyaye ta ji gaban ta ya faɗi haka, kamar wacce ta hango wani abu a fuskar shi sai ta ɗan tsaya jim tare da karkata kan ta tana ƙara haɗa idanu da shi... To! Idanun ta ta ɗaga ta kalli Mama Nuriyya dake kusa da shi, ita kam ta gane ta dan wayayyar mace ce da har status tana ɗora kan ta da Ahalin ta, abun mamaki... Irin yanayin da ta ji akan Dattijon nan haka take jin shi yanzu daga kallon fuskar aunty Nur, ba tare da sanin ta ba kawai ta ji ta saki murmushi, wato irin abun nan ne da ake faɗa wai *ƙauna daga kallon farko*, kafin sakannin yanzu tsarguwa take ji da haushi haushi na kallon wuce ƙa'ida da suke mata, amma yanzu sai ta ji wata ƙauna da ba ta taɓa sanin tana ma aunty Nur ba da mutumin dake kusa da ita wanda ta fi tunanin mijin ta ne.
Ƙara takawa Ummu ta yi da niyyar zami kusan Mama, amma sai Mama Nuriyya da ita kawai zuciyar ta da ƙwaƙwalwar ta ke ta faɗa mata ke fa *ƴar ki ce* kawai ta miƙe ta sha gaban Ummu, wani kallo take ma Ummu kamar mai shirin saka hannaye biyu ta mata irin ɗaukar nan ta jarirai, daga sama har ƙasa take kallon ta da murmushi da kuma kuka a fuskar ta, shauƙi kuma da farin ciki ya sa ta kasa cewa uffan sai ƙarewa Ummu kallo kawai take.
Hakan yasa Ummu dake ta doka murmushi ta riƙo hannun Mama Nuriyya tace "Aunty Nur, dama na faɗa ai zan iya gane ki a zahiri, ina wuni?"
Hawaye kaɗai ke mata zarya a kumatu, sai kuma ta juya ta kalli Abbu Mukhtar da shi ma fa idan aka bar shi cewa zai yi wannan yana da alaƙa da ita, to amma lamuri irin wannan ai bka saurin nuna kan ka, sai a maka wata fasara ta daban, hakan yasa burin shi bai wuce kar ta kwafsa musu ba, dan tunda ya ga ta tare ta yasan t ji abinda ya ji ne, dama kuma samun Aisha ya rage mata raɗaɗin rashin Kuwailat, shine ma har sai ka ga kamar ta manta da ita, to da alama dai yanzu za ta tuna, wannan kuma idan wannan ita ce ta haife ta, to zai ga yadda za'a raba su kam.
A kiÉ—ime ta kalle shi da yanayin da shi kaÉ—ai ya gane me take nufi tace "Kan gani aboki? Wannan ba Kuwailat bace? Aunty Ummu, ke ce Kuwailat ko?"
Ta ƙarashe maganar har da sake matsawa daf da Ummu, duk ƙauna da soyayyar nan da Ummu ta ji tana mata yanzun nan, da girmamawa da ganin mutumcin da take mata na haɗuwar waya, sai ta ji tana mata wani kallon anya kuwa? Me take nufi to da wannan maganganun da basu da makama?
Da sauri Abbu ya taso ya kama ta ya mayar ya zaunar da ita tare da yi mata raɗa "Ki nutsu ƙawata, kar ki sa muji kunya dan Allah, neman aure muka zo, idan muka gama zamuyi waccen maganar, kin ji ko?"
Dan dai ya kwantar mata da hankali ne ya faÉ—i haka, sai kuwa ta jinjina kai tana murmushi tace "Da gaske? To shikenan, amma wallahi wannan Kuwailat ce, baka ga kamaninin Hajia ba."
Murmushi ya mata yace "Na gani, sosai ma, ke dai ki nutsu, zamuyi magana, wannan ai Kuwailat É—in mu ce ma da gani."
Murmushi tayi irin na ya yarda da ita ɗin nan har da gyara zama tana ci gaba da kallon Ummu da duk jikin ta yayi sanyi take ji abu irin dai na shaƙuwa mai ƙarfi tsakanin ta da mutanen, haka ma Kuwailat da ta fito daga madafa ta aje ruwa da lemu a faranti tana sake gaishe su sannan ta shige wajen Nabila, ƙara gaisawa aka yi sosai kafin Yaya Bilal ya kalli malam Adam yace "Malam, ni sunana Bilal, ni Yaya ne ga shi Fahad mai son Nabila, wannan mai ɗakina ce Fa'iza..." Ya faɗa da nuna Fa'iza da ta yi murmushi ta sadda kan ta, sai kuma ya nuna Abbu yace "Wannan ma ƙanena Alhaji Mukhtar, ga iyalin sa nan..."
Gyara zama yayi ya ɗora da "Hajia ce ta wakilta mu kan mu zo mu ba wa iyayen Nabila haƙuri kan duk abubuwan da suka dinga faruwa, duba da rayuwar da yaran nan sukayi, amma bamu taɓa zama muka tattauna dan dawo dasu hanyar da ta dace ba, to daga bisani sun yanke shawarar aure sai kuma su iyayen namu suka nuna ƙin amincewar su, sun ce mu faɗa muku ba komai yasa suka ƙi amincewa a wannan lokacin ba sai dan rashin sanin niyyar tasu ta yin auren, sannan kuma basu san ko suna da ƙudirin shiryuwa ba, wannan kawai shine dalilin da ya sa suka ce a'a, bayan rsuwar mahaifin mu ƙanin shi ya zauna da mahaifiyar mu sun yi magana sosai, anan suka fahimci ai ita Nabila har ma shi Fahad ɗin ya umarce ta da ta yi istibra'i, hakan ne yasa suka janye makamai su suka kuma yarda su auri junan su tunda suna so."
Numfashi ya ja sannan ya sauke su ya sake kwantar da murya yace" Abu mafi mahimmanci da ya kawo mu ne shine bayar da haƙuri, takaba da Hajia ke yi yasa ta ce mu mu zo, ba dan haka ba da kan ta za ta zo, dan Allah muna baku haƙuri akan abinda ya faru, sannan ku taya mu ba wa ita yarinyar haƙuri, dan mun san ba'a kyauta mata ba, mu ma kuma ba yadda zamuyi ne tunda su suka haife mu, amma magana ta gaskiya bamu ji daɗin abinda suka ma Nabila ba."
Gyaran muryar da malam Adam yayi alamar zaiyi magana yasa Mama kallon shi, ita ba ta da damuwa idan ya ce sun haƙura kuma sun yafe, amma dai ba ta so yayi gaggawar amsa buƙatar su, gaskiya ta ji ba daɗin abinda Nabila ta faɗa mata sun mata, kuma yanzu ta gasgata tunda gashi har suka yi tattaki da kan su suke neman a yi haƙuri, sun san basu kyauta ba kenan? To a yafe ɗin, amma dai amincewa buƙatar su sai an ji ta bakin Nabila ba gaskiya.
Kan ta na ƙasa ta ji malam Adam yace "Wannan ai ba komai bane, shi dama sha'ani na yara ya gaji haka, kuma tun farko da mu manya mun shiga maganar, ina ga da duk abun bai kai ga haka ba, kuma laifi ba naku bane ku kaɗai har da mu, dan ni kaina dake aminin mahaifin ta ina ga da shi mai iya neman ku ne dan kuyi maslaha tsakanin su, dan haka mu dai daga gare mu ba komai wallahi, fatan mu dai Allah ya ƙara shirya mana su, idan kuma har akwai wani abu da ubangiji ke nufi da tarayyar su tun farko, to Allah ya bayyana mana alkairin da ke ciki."
Da ameen ɗakin amsa har da Ummu da ta ɗan kawar da fuskar ta, wallahi duka mutanen nan kallon ta suke ta yi har yanzu, ba ma kamar aunty Nur dake ta mata murmushi ba ta ko san kawar da duban ta daga gare ta, Abbu Mukhtar ne ya gyara zama shima yace" Alhamdulillah, gaskiya mun ji daɗi da wannan karamcin da kuka mana, yanzu buƙatar mu gare ku bata wuce amincewar ku wajen ƙulla alaƙa tsakanin Fahad da kuma Nabila."
Shiru aka yi na sakanni, malam Adam da bai san me ye ra'ayin mahaifiyar Nabila kan haka ba ya kalle ta, haka Yaya Luƙman ma Mama yake kallo dan bai san matsayar su kan haka ba, Ummu kuma da tasan yadda aka yi cikin nutsuwa da ladabi duba da ita ce ƙarama a duk taron ta dube su da fara'a a fuskar ta tace "Zamuyi farin ciki da hakan, sai dai zamu ji ta bakin ita Nabila, dan a baya tayi ƙorafin ba zata yi aure yanzu ba, dan haka zamu so muji yadda ta yanke."
Yaya Bilal ne yayi murmushi, wallahi sak maganar ta irin a nutsen nan yadda Hajia ne take yi, shiyasa fa Hajia ko faɗa ba ta ma yara irin mai hargagin nan, ya salam! Wannan kama jama'a? Da tsufan shi da komai amma yarinyar nan ta gane irin kallon da yake mata, kar dai tayi wani tunanin a kan shi ma? Da ƙyar dai ya saita nutsuwar shi yace "Wannan ai ba matsala bane, dama dole ne mu ji ra'ayin ta akan haka, ba damuwa."
Miƙewa Ummu tayi tace "Bari na kira ta."