← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 168

Sashe 25

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi Alhajin yayi yace "Nima Haka Jabir, kuma madadin godiyar ka ina so ne ka dawo min nan da cikar burin ka, ka fahimta?"

Jinjina kai yayi cike da ƙwarin guiwa yace "In sha Allah Abba."

Ƙara dafa kanshi yayi sannan ya kalli Khamis dake musu murmushi yace "Nagode Yaya Khamis."

Hannu Khamis ya bashi suka gaisa yace "Ka kula Jabir, duk da nasan ma Aliyu zai kula da kai, ku maida hankali ga karatun ku."

Nan ma kai ya jinjina yace "In sha Allah yaya Khamis." Da haka suka bar shi a gidan mota zuciyar shi ba komai a cikin ta sai ƙaunar mutanen da suka taimake shi a rayuwa har suka zame mishi wani ɓangare na rayuwa wanda zai iya kiran su da *Ka fi ɗan uwa*, dan ba wanda ya tallafe shi a rayuwar shi sai su, kuma jigon hakan ita ce *auntynsa* Ummu Kulsum.

*Bayan wata É—aya*

Kiran d ya shigo wayar ta gashi kuma tana cikin falon tare da mutane, kuma wayar sirri ce da ba zata iya amsa ta a gaban su, da sauri ta miƙe bayan ta kalli mijin nata Bilal da bai fita ba sakamakon shagalin da za'a gudanar nan da awwani biyar na taya murnar ƙarin shekara da Kabil yayi fuskar ta ba fara'a tace mishi "Ogana, ina zuwa, zan ɗan amsa waya."

Babban mutum ne da fuskar shi ke wadace da annuri na riƙo da turbar addini da kuma sheƙin wadata, saida ya fara kanne mata ido ɗaya sannan yace "OK, amma ki dawo yanzu."

Ita ma kanne masa idon É—aya tayi sannan ta juya tana fadin "Yanzu."

Saida ta bi Nuriyya da ido wacce ke rungume da Kabil ƙam ƙam a jikin ta saboda Abida da zata fita da shi siyayya kafin lokacin yayi, tana ji kamar wani abu zai faru da shi ne, bata son rabuwa da shi ko na sakan dan shi kaɗai ya rage mata a duniya, idan tayi sake shi ma za'a iya raba ta da shi. Wani shaƙiyin murmushi ta yi mai tarin ma'anar da ita kaɗai ta san shi, tana kaiwa bakin ƙofa suka ci karo da Abida ta gama shiryawa ta shigo da fara'a tana faɗin "Yarimana, na barka kan.."

HaÉ—ewar da sukayi da Fa'iza yasa ta yin shiru suna kallon juna, wayar ta Fa'iza dake ci gaba da vibration yasa Abida kallon wayar, da sauri Fa'iza ta É—an juya wayar yadda Abida ba zata ga allon wayar ba bare har ta ga sunan da aka kira ta da shi, wani murmushin ko a jikina Abida ta sakar mata tace "Aunty ina zuwa kuma? Ko masu gyaran wurin sun iso ne?"

Fuska a haÉ—e kamar dai yadda ta saba zama a gidan kullum cikin haÉ—e fuska tace "Ba su bane, zan iya wucewa?"

Taɓe baki tayi tare da kauce mata a hanyar ta fita sannan ita ma ta shigo tana kallon Kabil dake san saukowa daga ƙafafun Maman shi, da sauri ta ƙaraso ta ɗauke shi tana kallon Nuriyya da idanunta duk suka cika da hawaye tace" Haba ƴar uwa, ba fa jimawa zamuyi ba, kuma ga kawun shi ma a tare damu ko?" Ta faɗa tana nuna Sabeer dake zaune ya ɗora ƙafa ɗya kan ɗaya yana danna wayar shi, jin ta ambace shi ya ɗago manyan idanun shi ya zuba mata, sai kuma ya kalli Nuriyya da duk tayi kalar tausayi yace" Aunty *Nur*, idan hankalinki bai kwanta ba, me zai hana mu tafi tare to?"

Da sauri ta miƙe tsaye tana murmushi tace" E, hakan ma zai fi, gaskiya na fi so mu je tare."

Murmushi Abida tayi tace" To shikenan, Muje ko?"

Sai kuma ta kalli su Hajia tace" Hajia zamu tafi, baku da saƙo?"

Alama Hajia ta mata da hannu kan ta zo tare da cewa" Zo muyi sirri." Dariya Abida tayi ta nufi Hajiar, tana zuwa ta durƙusa ta miƙa kunnen ta kamar yadda Hajiar ta buƙata.

Suna cikin magana da Hajia da babu wanda ke ji Fahad ya shigo falon da yanayin sauri, ba sallama, ba sannunku, ba kallon kowa kawai ya nufi hanyar da yasan ɗakin yana nan, Alhaji da Mukhtar da ke zaune shia daf da inda Nuriyya ta miƙe tsaye tana gyara kallabi n doguwar rigar ta dan tafiya da kuma Bilal duk suka kalle shi, Sabeer da ya ɗan fi su zafi ne ya kalle shi shima ya daka masa tsawar "Kai! Baka ga mutane bane zaka shigo mana ɗaki babu sallama?"

Dakatawa yayi baya ya turo baki, sai kuma ya shafa wata tarin suma da ta ci uwar ta breaker🚶‍♀️ya kalle su ɗaya bayan ɗaya yace "Salam, ina sauri ne Yaya, wani abu nake nema."

Kama hanya yayi zai sake wucewa Bilal ya miƙe yana kallon wani zanzaro da Fahad ɗin yayi, a hankali Bilal ɗin yake zagaywa inda Fahad yake wanda hakan yasa Fahad ja baya saboda a banza ma Bilal mutum ne mai jiki, gashi kuma duk cikin su shi ne ba shi da tsayi ga kuma ƙiba tubarkallah da ɗan tumbinshi luwai luwai, ganin Fahad na ja baya yasa Bilal cewa "Dakata nan, wallahi kana matsawa zan sa Sabeer ya ɗaure min kai na jefa ka a bayan gida, sai kayi sati baga hasken rana ba."

Cikin tashin balagar samartakar dake ɗibanshi da jin kamar za'a takura masa ya wani shiga jijjiga yana nuni da hannaye yana cewa "To wai ni dan Allah me na muku yanzu daga shigowa ta? Shikenan ni dan kun tsane ni ba damar na shigo sai kun ce nayi laifi, shiyasa ma na zaɓi nayi zamana a waje babu mai takura min, wallahi ni idan haka za'a ci gaba da yi min to kawai zan bar muku gidan, kunga shikenan kun huta da gani na."

Sabeer dake ji da fiye da tashi ƙuruciyar ne ya miƙe yana ƙoƙarin haurawa ta kujerar da yake zaune a zafafe yana faɗin" Kai Fahad, mu sa'anninka da ka tsaya a kanmu kana faɗa mana maganar banza?"

Miƙewa Hajia tayi duk hankalinta ya tashi amma kuma ta kasa magana dan ita kanta tasan Fahad baya kyautawa, sai dai kuma hukuncin da Sabeer ɗin ne zai masa bata so, dama dai Bilal ne tasan duk hargagin da zai masa ba zai masa marin da ya zarce biyu ba, amma Sabeer kuma zai ce ma sai ya saka masa ɗamara ko waya. Ganin Sabeer ya kai ga Fahad ya ɗaga hannu zai ɗauke fuskar shi da mari ya sa ta runtse idanu ta kai tafin hannun ta ta rufe baki kamar za ta yi kuka kuma ita dai bata hana ba, bare kuma Alhaji da ko kallon ɓangaren nasu ma baya yi dan shi idan ta shi ne su casa shi tunda shi ya ga ƙarfin shi ya ƙare baya iya wa da shi.

Tausassan murya cikin nutsuwa da kwanciyar hankali da kuma dattijantaka Abbu Mukhtar yace "Sabeer...kar ka taɓa shi."

Cak! Sabeer ya tsaya tare da juyowa yace "Amma Yaya Mukhtar..."

A dake sosai cike da mazantaka da bayar da umarni yace "Ya isa..." Sai kuma ya mishi nuni da idanu ta hanyar nuna masa Hajia da kamar za ta yi kuka, a nutse Sabeer ya kalle ta sai kawai ya juya ya kalli Fahad da ya cije leɓen ƙasa ya na jiran Sabeer din ya taɓa shi shima ya rama, jinjina kai Sabeer yayi tare da yin ƙwafa yace "Zamu haɗu da kai yaro."

Dawowa yayi kujera shi ya zauna, Bilal kuma ƙarasawa yayi kusan Fahad ɗin ya riƙo ƴan tsirarun gashin da suka masa tsatsaye a tsakiyar kai ya murɗe sosai yadda saida Fahad ɗin yayi ƙara yace "Zafi Yaya Bilal, kayi haƙuri dan Allah."

Cikin ɗaga murya Bilal ɗin yace "Me ye wannan? Na ce me ye wannan? Fahad za ka min aski ko sai na sa an maka ƙwal kwabo?"

Da sauri Fahad ya amsa da "Na yi, nayi wallahi Yaya."

"Kayi alƙawari?" Bilal ya tambaya ba tare da ya saki gashin ba, da sauri ya amsa da "Na yi yaya Bilal."

Sakinshi yayi shi maya dawo ya zauna wurin shi, lokacin kaɗai Hajia ta zauna ita ma suka ci gaba da maganar su da Abida haro ta ciro kati a ƙaramar post ɗin ta ta miƙa ma Abidar.

Ga mai son shiga grp É—in *RUBUTACCIYA* kuma wanda ta shirya comment to ta yi min magana akan wannan lambar *+227-82-91-21-74*.

*Alhamdulillah.*
29/07/2023, 09:55 - MOM LATEEF: 👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨
*RUBUTACCIYA*
👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨👩‍❤️‍👨

_NA_

*SAMIRA HAROUNA*

_SADAUKARWA GA_

*MRGY. HAJIA FATIMA ZAHRA*
_(Allah ya jiƙanta da rahama)_

_Bismillahir- rahamanir-rahim._

*12*

Jikin motar Sabeer ta maƙale tana amsa kiran idanun ta kuma akan ƙofa dan tana so taga mai shiga da fita kar a ritsa ta, ba wani alamu dake nunawa na nesa wayar da take ta rashin gaskiya ko wacce ke buƙatar sirri ce take amsawa da "Na ji, naji DG, na gaya maka akwai abinda nake shiryawa yau ɗin nan, in sha Allah kuɗin ka cass a asusun ka, amma kar ka manta da wani abu..."

Sai kuma ta shiga yanayin gargaÉ—i har tana nunawa da yatsa dan san samun tabbaci tace "Ina kammala biyan ka kuÉ—in ka aikina kawai za ka shiga, dan kasan yarjejeniyar mu haka ta ce."

Daga can ɓangaren DG ya amsa da "Ba ki da matsala Hajia, ai rashin biyana kuɗin gaba ɗaya ya jinkirta aikin, da izuwa yanzu fa kun gama sabawa."

Ajiyar zuciya ta sauke tace "Shikenan, da zaran wannan harƙallar da na haɗa ta faɗa, zaka ga saƙona a asusun ka, sannan..."

Gyara tsayawa tayi ta ci gaba da cewa "Daga yanzu zuwa sati ɗaya ka da ka kirani a wayata, idan buƙatar yin magana da kai ta taso zan kirana da kai."

Daga wurin DG cewa yayi "To idan kuma ni nake so nayi maganar dake fa?"

A ɗan kausashe tace "DG, ka daina min abu mana kamar wani wanda ya aureni ko yake shirin mallakata, ni fa na zaɓeka ka min aiki kuma biyan ka zanyi ba kyauta ba, sannan na faɗa maka yau idan ban biyaka cikon kuɗin ka ba gobe zan biyaka, dan abinda nake shirin aikatawa ya fi ƙarfin ahalin Ahlan su tsaya ɓata lokaci dan sun fi ƙarfin abinda zan nema, dan haka ka daina ƙoƙarin gwada ikon ka a kaina, ka gane?"
Chapter 25 · 0% Book details