Sashe 107
Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kamar an tura Mama faɗawa tayi kan kujera inda ta tashi ta fashe da kuka mai tsuma zuciya tana rufe da fuskar ta, da kulawa Yaya Luƙman ya zauna kusa da ita sai malam Adam da ya bi bayan su Abbu yana musu ban kwana, cike da tausayawa Yaya Luƙman yace "Mama, lafiya ? Me aka yi na kuka kuma?"
ÆŠaga kan ta tayi ta kalle shi cikin kuka tace "Me aka yi kuma? Kai baka ga abinda ya faru bane?"
Sai ta sake haÉ—a tafukan hannayen ta da fuska tana kuka tana faÉ—in "Allah! Ya Allah! Hasbunallah wani'imal wakil, ashe dama tarayya Nabila da Fahad sanadin haÉ—uwar Æ´a da uwa ne? Ashe tarayyar su za ta zama alkairi ga dubbanin mutane?"
Da sauri Yaya Luƙman yace "Mama, ya zaki faɗi haka? Dan sun nuna sun san ta ai bai zama lallace ƴar su bace, basu da hujjar da zasu tabbatar mana ita tasu ce, Mama kawai mu manta da maganar nan, wallahi Ummu ƙanwata ce, kuma babu wanda ya isa ya rabamu da ita."
A hankali Mama ta ɗaga kan ta tana duban shi da murmushi a fuskar ta tace" Luƙman, Ummu ƴar su ce, suna da hujja, kuma shekaru tara da suka wuce na san da haka, amma..."
Sai kuma ta sake fashewa da kuka sosai har da haɗa kanta da hannun kujera tana faɗin" Luƙman gara na rasa ku, gara na rasa ku kai da Nabila da na haifa da na rasa Ummu, ka sani ina ƙaunar yarinyar saboda babu wanda ya kai ta ƙaunata a cikin ku, sannan Ummu tana son ku fiye da yadda ni da na haife ku nake son ku, ta ya zan jure rabuwa da ita bayan duk wannan shekarun, Mama take kirana, ba zan iya ba, ba zan iya ba Luƙman, dole na faɗa musu gaskiya, amma ba zasu raba ni da ita ba."
Rasuwar mahaifin shi kawai ta saka shi kuka, bayan haka ba wani abu da ya sake saka shi zubar da hawaye, amma sai gashi yanzu yana zubar da su wanda ya ma kasa tantance yana kuka ne dan mahaifiyar shi tana yi? Ko kuma yana kuka ne dan tunano abinda ke neman tunkaro su? Ba fa zai iya rabuwa da Ummu ba shima, ya fi so ta ci gaba da zama da su anan matsayin ƙanwar sa wacce ya fi so, Ummu da ko saɓani ya samu da iyalin sa ita ke musu sulhu, kuma ko shine bai da gaskiya kai tsaye take faɗa masa gaskiya Yaya baka kyauta ba, ba zai juri rabuwa da ita ba gaskiya.
*Duk* wannan bidiri da aka yi Sa'ad na waje cikin mota yana jiran su, dama ya ce ba zai shiga ba tunda kai tsaye ba neman auren bane, har yana musu raha da idan yarinyar ta amince to zai fara zuwa zance wajen ta kafin angon ya zo, hakan yasa har Yaya Bilal ya ranƙwashe shi a kai yana cewa _"Yarinyar Baban ka ce fa."_
Shi kuma yayi dariya yace _" Ai bana ɗaukar Fahad Baba, sai dai Abbu."_ Abubuwan da suka faru yasa sun ma manta tare da shi suke, bare su ce a kawo masa ruwa ya sha da abun taɓawa da aka kawo musu. Bi saki hannun Mama Nuriyya ba saida ya shigar da ita mota Abbu ma ya shiga baya ya zauna sannan ya ce Sa'ad ya tafi shi kuma shiga ɗaya motar.
Ba ta masa gardama ba, amma ji take kamar ya hanata ganin ƴar ta ne, saida suka fara tafiya S'ad na tambayar Abbu ya ya? A taƙaice kawai ya ce mishi "Zamuyi magana daga baya."
Jin haka kamar da ita suke sai ta fashe da kuka da iya ƙarfin ta, hakan yasa da sauri Abbu ya jawo ta jikin shi yana daddaɓata da faɗin "Shiiiiiii! Ya isa haka mana ƙawata, ba gobe zamu dawo ba? Zamu dawo gobe ki tafi da ƴar ki."
Ba Ta saurare shi ba sai kukan nan da take yi, Sa'ad da duk ya ji ba daÉ—i ne ya tambaye su "Abbu lafiya? Me ya faru dan Allah?"
Jim Abbu ya yi kafin ya kalle shi yace "Wata muka gani sak Hajia a ciki, komai nasu iri É—aya da Hajia bayan shekaru da suka bambamta su, mtsss!"
Sai kuma yayi ɗan gajeren tsaki ya kalli Sa'ad sosai yace "Sa'ad, naji a jikina kamar akwai wani abu tsakanin mu da yarinyar nan, Allah kaɗai ya fi mu sanin sirrin dake ɓoye, amma da wuya a ce wannan ba haɗa jini da ita ba."
Shiru Sa'ad yayi yana nazarin maganar sa, basu sake magana ba sai kukan Mama da suke ta saurare har suka isa masaukin su wanda da gidan Sa'ad É—in suka so zuwa dan su duba Eesha da ya ce bata da lafiya, amma halin da suke ciki ya sa ma ba wanda yayi wannan maganar.
********************
Saida kowanen su ya ci kukan shi kafin Mama ta wanke fuskar ta ta ƙwanƙwasa ɗakin Nabila cikin dakusashiyar murya tace "Ummu, fito yamma tayi sosai ki wuce gidan ki, maza fito daga ɗakin nan kafin na sa a ɓalla min ƙofar."
Cikin waa irin murya Ummu dake kwance ta amsa da "Ina zuwa Mama."
Saida ta sai ta nutsuwar ta tare da gyara jikin ta sannan ta fito, fitowar ta kuma daidai da shigowar Yaya Luƙman, yana ganin ta yace "Yawwa Ummu, Alhaji ne ya kira ni yanzu ya ce muje na sauke ki gida."
Da mamaki ta kalle shi tace "Kai kuma Yaya? Amma ai da mota ta na zo, kuma ya sani."
Ba alamar wasa yace "Haka dai ya faÉ—a, kuma kinsan mai gidana ne dole na kaiki gida."
Raɓa su Mama tayi ta wuce tana faɗin "Maza ki shirya to ki tafi."
Jiki a sanyaye ta shiga haɗa nata-ya nata dan tafiya gida, saida ta gaa shiryawa Kuwailat ta fito suka ma Mama sallama suka tafi Yaya Luƙman ya mayar da su. Ƙofar gida suka same shi daf da magrib, Ummu shigewa sukayi shi da Luƙman kuma suka gaisa kafin yace mishi "Kayi mamaki da na ce ka kawo ta ko? Duk da ta tafi da motar ta."
Murmushi Luƙman yayi yace "Ban yi wannan tunanin ba Alhaji, kawai nayi abinda ka ce ne."
Murmurmshin jin daɗi yayi yace "Luƙman, dama ina son magana da su Mama ne, da ni naso zuwa da kaina, amma sai na ga rashin dacewar na je gidan akan wannan maganar, shiyasa nace ka zo dan ka min alfarmar sanar da su, idan zai yiwu har da malam Adam, saboda yana ɗaya daga cikin wanda suka bani auren Ummu."
Kallon shi Yaya Luƙman yayi yace" Allah dai yasa lafiya?"
Murmushi yayi har da dafa kafaÉ—ar shi yace" Kar ka damu ba komai, kai dai ka sanar da su."
Jinjina kai yayi yace" Shikenan, amma kamar wane lokaci zan faÉ—a musu?"
Saida ya sauke ajiyar zuciya yace" Idan zai yiwu ko zuwa anjima ma."
Sake jinjina kai yayi yace" Shikenan, in sha Allah zan sanar da su."
Murmushi ya masa tare da yin godiya sannan sukayi sallama shi ya nufi masallaci shi kuma dan komawa, sai dai jikin shi a sanyaye yake yana jin kamar ba lafiya ba.
Tana zaune dai ne kan salayya, azkhar ɗin da ta saba yi yau tunani ya sa ta kasa kammala su, tunani ne barkatai ke zuwa mata kwanya na abinda ya faru, gaba ɗya ma ta manta da tana da damuwa, lallai ita kanta sha'awa kwanciyar hankali da ƙoshi ke kawo ta. Tana wannan halin Alhaji ya sallamo ɗakin ta, da mamaki ta kalle shi tare da amsa sallamar, kwana huɗu kenan rabon da ya leƙo ɗakin nata, daga ganin fuskar shi kuma ba wannan jarababben hushi yasa ta fara jin kamar akwai salama tare da shi.
Sai dai nata yanayin ita ma ya addabe ta, dan haka ta sadda kanta ba ta ce mishi komai ba sai ma azkhar din ta da ta fara yi dan ya gane ba haka kawai take zaune ba, zaune yayi bakin gado yana kallon fuskar ta da fara'a yace "To ya? Baƙin sun samu karɓuwa a wajen Nabila kuwa?"
Kallon shi ta sake yi, hakan na nufin ya huce kenan? Ƙwarai kuwa, tunda ai da ko kallon inda take ba ya yi, cikin nutsuwa tace "Har yanzu dai, amma zanyi magana da ita, in sha Allah za ta amince."
Cike da gamsuwa yace "Allah ya aminta, gwara ta amince kam, kinga ai sai na É—aura mata aure, matsayina na mijin auntyn ta."
Murmushin jin daÉ—i tayi tace "Gaskiya ne, in sha Allah ma zata amince, kawai aji ne take so ta ja musu."
Murmushi yayi bai ce komai ba, shiru ne ya ɗan biyo baya na daƙiƙu kafin ya sake kallon ta yace "Ki tashi kiyi wanka ki fito falo, akwai hirar da zamuyi."
Kallon shi ta sake yi, sai kawai farin ciki yasa ta jinjina kai tace "To."
Miƙewa sukayi a tare ita ta nufi ban ɗaki bayan cire hijabi da tayi shi kuma ya fita daga ɗakin yana jin hakan kawai shine maslaha. A falo ma shi da Kuwailat suka dinga hira har sallah isha'i Ummu bata fito ba, saboda kwalliyar da ta tsaya tsarawa duba da yau ya daina hushi da ita, kuma dai ai ta iya hausa sosai, da ya ce tayi wanka tasan me yake nufi, dan haka tana fatan ganin sauyi akan komai, indai har sauyin nan ya tabbata to zata nemi izinin shi ta bar ƙasa na wata ɗaya ta huta kafin ta dawo.
Saida tayi sallah isha'i sannan ta fito ita ma, Kuwailat na idar da sallah ta kalle ta tace "Mamie, nifa yunwa nake ji, me zamu ci?"
Kallon ta tayi tana zama tace "Kin dai ga ban dafa komai ba, amma abinda zki ci zaki faÉ—a min."
Wani irin zama tayi cike da sangarta tana faÉ—in "Mamie indomie da kifi."