← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 168

Sashe 68

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani mummunan faɗuwa gaban shi yayi saboda jin muryar, inda tafin hannun shi ya jimƙe wayar gam ya rintse idanu, take tsigar jikin shi suka tashi duk kwantancen gashin dake hannun shi ya nemi miƙewa, samun kan shi yayi à yanayin da kai tsaye ya kasa iya fassarawa, dan bai san tashin hankali bane ya shiga na jin muryar mahaifin na shi? Ko kuma dai kewa ce cike da bege na mahaifin da ka jima baka haɗu da duk wani abu da ya shafe shi? Wannan ƙaƙƙarfan muryar da ya ji an sake ambaton "Hello, ina ji !"

Hakan ya saka shi buɗa idanu da sauri ya yanke kiran saboda jin kamar mahaifin nashi a hassale yake magana, sannan bai san me zai ce mishi ba bayan kwashe wannan shekarun da aka yi, bai san ta ina zai fara magana da shi ba, shin har yanzu mahaifin shi na nan da ƙudirin kalmar nan da ya faɗa ta sai yayi Ajalin shi? Ko kuma dai shekaru da kuma lokaci ya sa ya manta da abinda ya faru? Dafe gaban goshin shi yayi tare da feso iska daga bakin shi ya lumshe idanun shi ruf, a tausashe ƙwarai ya furta "Ba zan iya ba."

A ƙufule, kuma a hassale Aliyu dake zaune gaban shi shi ya tirsasa shi kiran mahaifin nashi yace "Za ka iya Jabir, za ka iya magana da mahaifin ka, mantawa kake da shi kaɗai ne ya rage maka ko? Jabir a ganin ka da mahaifiyar ka tana raye za ta bar wannan daɗɗiyar gabar ta ci gaba da wanzuwa a tsakanin ku ne?"

Da sauri Jabir ya É—ago ya kalli Aliyu da ya tsare shi da idanu, idanun shi tuni sukayi jajir abun ka ga jar fata, sai kuma ya tausasa kallon shi ga Aliyu ya girgiza kai yace" Ba gaba muke ba."

Wani sakaran murmushi Aliyu yayi yace" Ba gaba kuke ba? Me kuke to? Shekara goa sha uku ko gaisuwa ba t haÉ—a ka da mahaifin da ya haife ka ba, kuma ka ce ba gaba kuke ba? To e kake yi da shi?"

Shiru yayi sai wayar da yake ci gaba da kallo kawai yana sauke numfashi, cike da bada umarni Aliyu ya sake cewa" Ka kira Jabir, idan ba haka ba zan kira Abba na sanar da shi ka samu lambar mahaifin ka fiye da shekara ɗaya, amma ajiyar ta kawai kake a waya ka ƙi kiran shi."

Zubawa Aliyu idanun shi yayi, kallon da yake ma Aliyu shi kan shi sai ya kasa fahimta, hakan yasa Aliyu miƙewa yayi hanyar ɗakin su na bacci yana faɗin" Zan ƙarasa shirin kayan mu."

Saida ya ji Aliyu ya shige ɗakin ya sauke nauyayyar ajiyar zuciya, wayar ya sake kallo, Abba? Ba Ya so Aliyu ya faɗawa Abba komai, dan take zai bashi umarni kuma dole ya bi dan alƙawari ya ɗauka tsakanin shi da ubangiji kan cewa zai yi duk abinda bawan nan ya saka shi matuƙar bai saɓawa shari'a ba, ya yi niyya zai yi duk abinda ya umarce shi sau ɗaya ba sai ya maimaita sau biyu ba, dan haka ya sake sauke numfashi sannan ya sake tura kiran.

Nan ma ƙara ta dinga yi wayar har ta kusa tsinkewa kafin ya ji an ɗaga a zafafe yace "Oui ina ji, wa ke magana?"

Ɗaga bakin shi yayi zai yi sallama, amma sai ya ji kamar wani abu ya tokare mishi maƙoshi, hakan yasa ya kasa cewa komai yanzu ma, da yanayin nan na zafi da yasan Abban shi da shi yace "Ko ma waye ke kira idan baya ji ne ko nine bana jin shi dan Allah ya haƙura da kiran dan ba zan iya haɗa tashin hankalin da nake ciki da wannan shirmen ba."

Niyyar yanke kiran yayi, amma da Jabir ya ji mahaifin shi ya ambaci tashin hankali sai shima nashi hankali ya ɗan miƙe tsaye saboda rashin sanin ma me ke faruwa to? Hakan yasa shi saurin faɗin" *Aba*."

Tsit! Dukansu sukayi sai numfashi suke saukewa, shi dai duk canzawar da mai muryar nan ya yi, duk da rashin tabbacin da yake da akan sanin mai muryar, ba zai kasa faɗin cewa kamar tattausan muryar ladabin yaron shi ba da ko wane lokaci muryar shi a nutse take fita, amma rashin tabbaci da kuma son ya gane shi ɗin ne ya tuna da shi yau ya kira shi? Ko kuma dai wani ne mai irin muryar ɗan sa Jabir, dan haka a tausashe cike da zaƙuwa da zumuɗi yace " *Jabir*? Kai ne?"

Shiru Jabir ya yi sai dafe goshin shi da yayi na wasu sakanni, da zumuÉ—i Aban nashi ya sake faÉ—in "Jabir? Kai ne? Ka yi magana mana in ji?"

Shi fa bai ɗauka akwai wani tausayi ko ƙauna tsakanin su ba, amma iko na Allah kawai sai ya ji yana lumshe idanu hawaye sun gangaro kan kumatun shi irin masu zafin nan dake nuna halin da zuciya take ciki, da sauri da kuma rashin yarda cewa hawaye ne yake ya goge tare da jan majina ya sake furta "Aba, ni ne."

Wani irin salati ya ji mahaifin nashi yayi da sam bai tsammaci zai yi shi, cike da kewa da nadama ya fashe da kuka a wayar yna faɗin "Jabir, dama za ka yafe min ka kirani? Ban taɓa tunanin za ka sake waiwayata, Jabir na jima da cire tsammani a kan ka, na ɗauka nayi asarar ɗana ɗaya tilo da na mallaka a rayuwata."

Sai kuma yayi shiru yna ci gaba da kuka, cikin rashin jin daɗi Jabir ya miƙe tsaye a tausashe sosai yace" Aba, ka daina kuka dan Allah, ka yafe min Aba, nayi kuskure nima da na tafi na bar ka kuma ban sake waiwaya ba, amma Aba ba dan *Abbana* ba da wataƙila fanɗarewata ta isa tasa na ƙi waiwayar ka har abada."

Cikin raunin murya kamar zaiyi kuka ya sake cewa" Aba ka yafe min, jibi zamu dawo ƙasar nan in sha Allah, zan sake neman afuwar ka akan ɓata maka da nayi."

Da farin cikin jin zai dawo ya ce" Jabir za ka dawo? Jibi jibin nan? Allah ya dawo da kai lafiya Jabir, Jabir baka min komai ba a rayuwa, ni ne na zalince ka na kasa riƙe amanar da Allah ya bani, ni ne mai laifi a nan dan ni ne silar komai."

Ajiyarp zuciya ya sauke yace" Aba baka da laifi, kai ka haife ni, kuma ka isa ka min komai idan nayi ba daidai, laifina ne."

Da farin ciki Aban yace" Ba komai Jabir, ni na jima da yafe maka, amma dai da gaske za ka zo ko? Za ka zo in ganka Jabir? Na san ka girma sosai yanzu, wataƙila ni ka biyo ko kuma Maman ka, zan so ganin haka."

Yadda yayi maganar da tsantsaar gaskiyar shi kenan yasa Jabir yin wani bahagon murmushi, ɗan ɗaga idanun shi yayi ya kalli madubin dake jikin ƙofa, a ranshi ya ayyana _" Ni ɗan Mamata ne Aba, kama da ita nake sak."_

A zahiri kuma cew yayi" Zan zo Aba, in sha Allah."

Shiru ne ya ɗan biyo Da sakanni inda kowa da abinda yake saƙawa a ranshi, kafin daga bisa Jabir ya nisa yace" Aba, ina aunty? Da Uzeifatu?"

Duk da a waya ne ba sa ganin fuskar juna, amma daga yadda ya bashi amsa da" Suna nan, lafiya lau." Ya fahimci ba ya da karsashi kuma akwai wani abu a ƙasa, dan haka ya sake tambaya da" Lafiya ko Aba? Na ji kana maganar matsala ɗazu?"

A sanyaye ya bashi amsa da" Ba komai Jabir, Allah ya maka albarka, sai jibin idan kun taho, amma dan Allah ka ci gaba da kirana har sanda za ka zo."

Ƙwarai ya gasgata ɗari bisa ɗari akwai matsala, wataƙila babba ce da bai kamata su tattauna ba a waya, dan haka zai jira har ya koma gidan, dan haka ya amsa mishi da in sha Allah zai ci gaba da kira, sannan ya ce a gaida kowa da kowa sannan suka aje wayar, wata ajiyar zuciya ya sauke mai nauyin gaske tare da jin wani irin sanyi a ƙasan ranshi da ma zuciyar shi mai kama da na ka sauke kayan da suka fi ƙarfin ka a kai.

Aliyu duk yana jin abinda ke faruwa, dan haka saida suka gama sannan ya fito tare da nuna bai san da sun yi waya ba yace "Jabir, Abba nake ta kira wallahi wai wayar à kashe, Abba kuma ai baya kashe waya ko?"

Kallon Aliyu yayi gaba É—aya da kulawarsa tunda ya ji ya ambaci Abba d baya wasa da lamarin shi a sanyaye yace "Abba ba ya kashe waya ai."

Sai kuma ya ji gaban shi yayi wata sanyayyar faÉ—uwa, da sauri ya shiga neman lambar Abba a wayar shi, kira yake shima amma kashe, hankalin shi ne ya fara tashi, yasan ba ya kashe waya komai rintsi, sannan kuma yana fama da matsanancin tension, dan haka hankalin shi da tunanin shi ya fi bashi ba lafiya ba.

Aliyu dake kallon shi yana aika kiran wani bayan wani ne yace "Ko za mu kira Hajia babba mu ji lafiya?"

Zuba masa idanu Jabir ya yi bai ce komai ba, amma sai Aliyu y aga kamar Jabir na aika mishi saƙo ne da idanun shi cewa _"Ka manta Hajia girma ya gama cimma ta, ta yadda take fama da matsalar idanu ga kuma ta ƙafafu, sannan ga ciwon sugar da ya sako ta gaba shima, yau lafiya gobe ba lafiya?"_, sai kawai Aliyu ya hankalta yace" Hakane fa, to ko Umma (Hajia Asiya Maman Aliyu) za mu kira?"

Sai kuma yayi saurin girgiza kan shi yace" Um um, abar maganar Umma, ina kira sai ta yarfo maganar da za ta sa ka ksa ganewa, ga maganar aure da take min kullum."

ÆŠauke duban shi yayi daga kan Aliy cike da miskilanci bakin shi ya furta " Maaama."

Take kuma ya ɗora wayar a kunne alamar har ya aika kira wa lambar ta Ummu, ƙara wayar ta dinga yi ba'a ɗaga da wuri ba, hakane yasa Jabir kai da kawowa a tsakiyar falon cike da ƙaguwar ta ɗaga ya ji ina Abban shi? Sannan me ke faruwa?
Chapter 68 · 0% Book details