← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 168

Sashe 91

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dafe kai Nabila tayi tace "Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un ! Baban Fahad ? Wayyo Allah jarir..." Sai kuma ta tuna da ba zata sake kula shi ba, dan haka sai ta taɓe baki tace "Allah jiƙan shi da rahama."

Daga haka ba ta ce komai ba, amsawa Ummu tayi da "Ameen Ya Allah."

Sannan ta sake kama hanyar fita tana faÉ—in "Ki kwanta ki huta, sai da safe."

Kallon ta Nabila tayi tace "Saida safe kuma? Aunty ni kaÉ—ai zaki bari anan?"

Ba tare da ta juyo ba tace "Abinda yake ci na ya cinye ki."

Wani murmushi Nabila tayi ta bita da kallo, saida ta fice ta sauke ajiyar zuciya, ta ji daɗi da ba ta mata faɗa sosai ba irin wanda take nuna ta da yatsa kamar za ta mare ta, amma da ta mata gajeruwar nasiha ta sake ƙarfafa mata guiwar ta kama kan ta sosai.

********************

Saida Fahad ya share awa biyu kafin ya farfaÉ—o, Ja'afar ne tare da shi sai kuma Sabeer da bai jima da shigowa ba dan duba shi kamar yadda Hajia ta umarce shi, dafe kan shi yayi da yaji yana masa ciwo, a hankali ya buÉ—a idanun shi ya kalli Sabeer yace "Yaya, wai da gaske Abbu ya rasu? Yaya Sabeer Abbu ya rasu?"

Jiki a sanyaye Sabeer ma dake fatan ina ma ya suma ya dawo É—in nan ya É—aga masa kai tare da cewa "Abbu ya rasu Fahad, ka mishi addu'a kawai."

Kuka mai ƙarfin gaske Fahad ya fashe da shi daga kwance yana girgiza kai, cike da rashin jin daɗi Ja'afar yake ta daddaɓa kafaɗar shi yana faɗin "Kayi haƙuri Fahad, ba kuka zaka yi ba, addu'a za ka ma Abbu, Allah ya mishi rahama."

Sabeer ma dafa kafaɗar shi yayi yace "Hakane, kayi haƙuri Fahad, Abbu ba kukan mu yake buƙata ba, ka masa addu'a kawai shi ya fi so yanzu."

Girgiza kai Fahad yayi cike da takaici da nadama yace "Ba zaku gane bane Yaya Sabeer, ina tsoron kar Abbu ya tafi da hushina, idan har ya rasu yana hushi dani ya zan yi kenan? Ya zan gudanar da rayuwata alhalin mahaifina ya rasu da baƙin cikina? Inna lillahi wa'inna ilaihi raju'un! Yaya Sabeer ya zanyi."

Cikin rarrashi Sabeer ya riƙe hannun shi yace" Haƙuri zaka yi Fahad, bana tunanin Abbu zan tafi da hushin ka a zuciyar shi, duk da dai ka masa ba daidai ba, amma ka nemi gafarar ubangiji akan haka, shi mai gafara ne kuma mai jin ƙai."

Cikin kuka ya sake girgiza musu kai yace" Ba zaku gane abinda nake ji ba, na ɓatawa Abbu rai fiye da kima, na faɗa masa magana son raina, na bijirewa umarnin sa akan mace, jiya jiya na yi musayar yawu da shi, yau sai a ce min babu shi? Bayan tun jiya ba saka shi a idanu na ba."

A tausashe Sabeer yace" Haka Allah ya so Fahad, wataƙila kuma akwai abinda yake nufi wanda mu bamu san shi ba, kamar yadda na faɗa maka kawai ka yi ta istigfari."

Kuka Fahad ya ci gaba da yi yana faɗin" Wallahi Allah ni nasan Abbu da ɓacin raina ya rasu, to ina zan gan shi bare na nemi yafiyar sa? Ubangiji kuma ba ya yafe laifin wanda aka cuta har sai idan shi ne ya yafe laifin, a jerin manyan laifuka na duniya kuma a gurin Allah daga shirka sai saɓawa iyaye, kuma duk wanda bai bisu ba ba zai taɓa ganin daidai a rayuwar sa ba."

Girgiza kai Fahad yayi yace" Kar ka ce haka Fahad, in sha Allah ma Abbu bai rasu da hushin ka ba, kai dai kamar yadda na faÉ—a maka kawai kayi ta istigfari kana neman gafarar Allah, in sha Allah zai yafe maka, sannan za ka iya zama yaron kirki idan kana so Abbu yayi farin ciki da kai, kar ka manta daga yanzu duk abun kirki ko na tsiyar da muka aikata za'a bijarar wa Abbu da shi har da kamashon shi, idan na gari na tsiya ne shima haka za'a tashe shi a nuna masa aikin sharrin da yaran da ya bari duniya suke yi sannan a rubuta masa nashi kason."

Kallon Sabeer É—in ya yi, e abinda ya faÉ—a ya kama hankalin shi, dan haka sai ya gyara kwanciyar shi tare da tashi zaune yana faÉ—in" Da gaske Yaya Sabeer? Idan na aikata aikin alkairi Abbu a za'a iya bashi ladar?"

Cike da tabbaci yace masa" Sosai ma, kamar yadda kuma duk zunubin da zaka sake aikatawa musamman ma da dukiyar shi sai a raba muku shi tare."

Da sauri ya girgiza kai yana share hawaye yace" A'a, ba zan sake aikata wani zunubi ba, in sha Allah Abbu lada zai dinga samu, ina fatan Allah ya sa bai rasu da ɓacin raina ba."

Jinjina kai Sabeer yayi d gamsuwa yace "Allah ya sa ƙanina, idan kayi haka da ka faranta mana rai dukanmu, musamman ma Mamie."

Jinjina kai Fahad yayi yana ɗaura niyyar ba fa zai sake ɓata musu rai ba, ba kuma zai sake aikatawa wani abun da za'a nuna shi a ce ɗn margayi Saheeb ne, sannan burin da ya rasu da shi ma zai cika masa shi na auren Fati, zai yarda ya aure ta kuma zai yi biyayya ga umarnin sa ta hanyar ba wa Nabila haƙuri ta manta da shi, amma ba zai sake gigin ɓata musu ba, kar a zo mahaifiyar da ta rage musu ita ma baƙin cikin shi ya kashe ta, ba zai iya jura ba idan haka ta faru! Kuma wallahi da ya san Ajalin Abbu na kusa, da ba wai zai fara masa ladabi bane na iya kwanaki biyu da y zo garin nan, da zai fara ne shekaru da suka wuce dan kawai shi ma yayi farin ciki da shi.

*******************

Tana shiga É—akin ta same shi kwance idanun shi na kallon sama alamar akwai abinda yake tunani, har ta rufe É—akin ta zauna kan gadon tana cire abayar ta bai kalle ta ba, tana gama cire ta ta aje gefe sai rigar baccin ta da ta bayyana, juyawa tayi ta kalle shi tace "Barka."

A hankali ya kalle ta, sai ya ƙaƙaro murmushi dan baya so ta tambaye shi me yake tunani? Ba lallai abinda yake tunani ya mata daɗi ba tun yanzu, ga kuma matsalar ƙanwar ta da yake so ya zaunar da ita ya nuna mata rayuwa, idan ba haka ba daga ina ƴar nan take a wannan lokacin? Alamu sun nuna balaguro tayi, sam ba ya jin daɗin ko da haɗewa da ita cikin gari ne y nuna ta a matsayin wacce ya sani, ko da yake abun ba iya nan ya tsaya ba, tunda ya taɓa ganin wani abokin shi tare da ita, aka ce masa wai soyayya suke yarinyar kuma na bashi wahala, amma ba ta ma son su haɗu, to idan dattawa masu shekaru irin na shi zasu dinga kula yara kamar Nabila, ta ya kenan za'a yi ƙoƙarin canza su suma su zama na gari? Idan masu hangen nesa da hankali kuma waɗanda ake girmamawa ne abokan taɓarar su, kenan yaushe za su shiryu? Wa ye zai musu nasihar gyara kayan ka? Wa zai musu faɗa ya ce haka bai dace ba?

Bai ce maa komai ba saida ya tashi zaune ya matso kusa da ita, É—an jawo ta yayi jikin shi yana shafa lallausan fatar ta da duk sati take murje ta da kayan gyaran jiki na gidan Hajia Fussam musamman ma irin su dukkhan, wanda shi ya fi komai birge ta ko dan sahihancin itacen da take haÉ—awa, cikin nutsatsiyar murya yace "Me ya faru a asibiti? Me suka ce yake damunki?"

A nutse ta sake kwantawa jikin shi tana sauke numfashi, kafin daga bisani ta numfasa cike da tausayawa kan ta da baƙin ciki da Takaicin abinda likitan nan ya mata tace "Ba komai, sun ce matsala ta ba babba bace tunda ina da miji, kawai ruwa ne ke son fita daga jikina."

Jim! Dakatawa yayi daga shafar dantsen ta da yake yi, ɗan girgiza kai yayi yana jin wai me yasa wannan matsalar ke neman sako shi gaba? Shin idan aka kai irin wannan ƙadamin ba haƙuri ake yi da komai bane? To me yasa sai ita za ta damu kan ta? Bayan hakan na iya jefa ta halaka idan ba ta cire haka a ran ta ba? Ɗan jaye ta yayi daga jikin shi ya kalli fuskar ta yace "Abinda ya saka ki ciwon mara kenan?"

Sunkuyar da kai tayi à kunyace ta ɗaga alamar e, jinjina kai yayi yace "To, yanzu ban san ya kike so nayi ba Ummu, raunin ba daga ni bane, daga shekaruna ne, shin ke da a haka kike? Ba yarinya ce ɗanya sharaf ba? A lokacin auren mu har gani kike ina takura miki da yawan buƙata ta, saboda a lokacin ke baki damu da abun ba kuma buƙatar ki madaidaiciya ce, nima kuma à lokacin ina da buƙatar sosai kuma an iya ji dake, amma sannu sannu shekaru duk suka mayar da mu haka, ki dubi ƴan uwan ki ki gani, kaf cikin su babu wacce yanzu ke kawo kanta ɗakina da sunan tayi bacci kusa dani, saboda su sun san jiya ba yau bace, kuma munyi girman da ya kamata mu aje duk wannan abubuwan gefe, amma ke..."
Chapter 91 · 0% Book details