← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 168

Sashe 2

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ga dai ƙofar gidan a zai ɗibi ruwan a rufe alamar sun kwanta, ba zai yarda ya koma babu ruwan nan ba, dan haka gwara ya tashesu dan ya ceci kanshi daga dukan mutuwar da za'a mishi a gidan nan, dan haka a nutse kamar yadda halayenshi da ɗabi'arshi suka zama masu sanyi ya dinga bubbuga ƙofar tare da yin sallama, dan ko da firgici ya sa sun saka tasowa sallamar tashi zai iya saka wani daga cikin mutanen gidan ya ɗauki muryarsa musamman ma dai mai gidan malam *Sule* da yaron gidan *Mujittafa*.

*LOKACIN* da yake buga ƙofar nan daga cikin manyan gidan masu hankali da sanin ta kamata duk idanunsu biyu, sun sa ƴarsu gaba ne suna tattauna wata matsalar tasu da ta kunno musu kai a daren nan, wanda su dai iyayen suke ganin ba dan ƴar ta tsaya kai da fata kan cewa za ta iya ba, to fa da ba zasu lamunce b dub da wasu dalilai.

Maganar son auren *Ummu Kulsum* da Alhaji Kabir wato mai gidan da suke ciki zaune ya zo musu ya zo musu da ita ta girgiza su, mutum kamar shi? Mai tarin dukiya da alfarma da kuma suna, sannan mai shekarun da suka ninka ninkin ba ninkin na Ummu Kulsum, sannan mai mata uku cif sannan wayayyun mata, yana da yara da jikoki bila adadi, a hakane zai ce zai auri Æ´ar su mai shekara sha bakwai a duniya. Ina! Wannan abu ne da gaskiya da kamar yiwuwar shi.

*Mariƙin* (Ba su ne asalin iyayen ta ba) na Ummu da ya ji ana ci gaba da buga ƙofar ne ya miƙe yana dafa kafaɗar Ummu Kulsum ɗin cikin rarrashi yace "Kinga daina kukan, da safe zamuyi magana kin ji, n ji ana buga ƙofar gida ne zan je na duba."

Cikin sanyayyar muryar ladabi Ummu Kulsum dake daf da *uwar marayu* kamar za ta fashe da kuka tace "Baba, wallahi na gaya muku da zen aure shi, na yarda ina sonshi Baba, idan ma shi ne ya zo ku ce masa na amince zan aureshi."

Tsura mata idanu yayi takaci na baibayeshi kamar zai wanke mata fuskar ta da tafi, sai dai kafin ya ce mata wani abu uwar marayu data gane me kallon shi ke nufi gareta ta ja hijabin Ummu har saida tayi kamar za ta kwanta a jikin ta, cike da son ta dawo da ita hayyacinta cikin É—aga murya tace "Wai ke kanki É—aya kuwa? Ya daga ji magana kawai za ki wani damemu da kina sonshi za ki aureshi, wannan É—in tsaranki ne a aure ko shekaru? Kin ma hango abinda muke hango miki ne? To bana ciki da iskanci."

Sai kuma ta kalli malam Sule dake kallonsu tace "Malam, ka je ka duba Kaga waye a daren nan? Na ji har yanzu bugawa ake, Allah dai yasa lafiya."

Ajiyar zuciya ya sauke ya nuno Ummu da yatsa yace "Ki ce ta shiga taitayinta."

Yana fita Ummu da ta bishi da idanu tayi saurin duban Maman nata, duk da ba ita ta haife ta ba, amma ita ta raineta tun tana jaririya, yadda aka bata tarihinta shi ne, an ce a *bola* aka tsince ta an jefar da ita, shi ne *Amina* ta ɗaukota ta kawo ta gidan ta ta raineta har yanzu da take shekaru *sha bakwai*, sun bata tarbiyya iya iyawarsu, basu bambamta ta da yaran da suka haifa ƙwaya biyu ba rak a duniya, hasalima *Lukman* ne kawai gaba da, bayan ta fara tafiya suka haifi *Nabila*.

Hannun uwar marayun ta kamo ta riƙe tana jijjigawa cikin taushin muryar da ya zam halittarta ce take faɗin "Mama, ai kinsan ban taɓa neman abu a wurin ku na rasa ba ko? Mama ina son Alhaji Kabir, ina so na aure shi Mama, dan Allah ki wa Baba magana ya amince."

Hannu uwar marayu ta ɗaga na damanta, kafin Ummu Kulsum ta ankara ta zabga mata shi a fuskar ta ranta a matuƙar ɓace, da sauri ta dafe kuncin ta tare da kallon maman nata tana zazzare idanu, cikin ɓacin ran da ba kasafai suka fiya gani na uwar marayun ba ta miƙe tana gyara ɗaurin kallabinta, ɓangare ɗaya kuma cikin faɗa take kallon Ummun tana cewa "Ummu dama a tarbiyar da na miki akwai ranar da zaki iya tsare ni da mahaifin ki kina mana magiyar mu miki aure? Dama ban sani ba har kin yi buɗewar idanun da zaki nemi yi mana kuka kina faɗa mana gaba da gaba kina son Alhaji Kabir sannan a aura miki shi? Ba ki ji kunya ba don Allah? Ummu idan ni kin ɗaukeni ƙawarki, shi Babanki abokin wasan ki ne?"

Girgiza kai ta yi cikin shasheƙar kuka duk da bata fara hawayen ba tace "A'a wallahi Mama, ba raina ku nayi ba, kiyi haƙuri."

Cike da bayar da umarni uwar marayu tace "Da kyau to, idan Babanki ya shigo ki gaggauta bashi haƙuri, sannan maganar auren ki da Alhaji Kabir babu ita, dan baku dace da juna ba ko kaɗan, kin gane."

Ƙurawa uwar marayu ido tayi tana kallon ta zuciyar ta fal da tunanin _"Me yasa ba zata fahimce ta ba? Me yasa ma dukansu ba zasu fahimta ba?"_

Ita ma *ba son shi take ba*, yadda taji suna tattauna matsalar a tsakanin su da butulcin da suke shirin yi masa matsayinshi na wanda ya dubesu ya basu masauki, gidan nan da suke ciki hada wutar lantarki ga kuma ruwa, ko ɗaya ba sa biyan ko sisi na wannan abubuwan, dan ruwa ma gabaɗaya unguwar anan ake ɗiba, sannan ga jarin da ya ba wa Baban nasu yake juyawa har suna samun abinda suke ci. Ita kanta ko da suka tsince ta suka kawo ta anan gidan ta gansu, a ƙalla shekarar su goma sha tara a gidan nan, bai taɓa cewa ku tashi ina buƙatar wurin ba, shi dai kawai ana kawo masa wasu kayayyakin da suka shafi kasuwancinsa ana aje masa a mangazar (store) dake cikin gidan.

Hakan yasa take ganin bai kamata a ce yau ya zo musu da butun son aurenta ba à ce sun ƙi amince masa, ita dai a yadda ta san ba su suka haife ta ba, ba za ta yarda Hakan ya zamar musu matsala ba, dan tana ji a ranta idan har basu amince ba, to zai iya tashinsu daga nan ɗin, kuma ko da m halayen da suka sanshi da su na karamci basu barshi ya tashe su ba, to ai da kunya suma su ci gaba da zama, to idan sun tashi in zasu koma? Baban su bai d halin da zai iya biyan kuɗin hanya da wuta da ruwa, Hakan kuma zai sa rayuwa ta sake tsananta a gare su ta musu zafi fiye da yanzu.

Uwar marayu na shinfiÉ—a a fargajiyar gidan malam ya dawo, da kulawa take tambayar shi "Malam waye yanzu a daren nan?"

Saida ya sauke numfashi ya bata amsa da "Wallahi yaron nan ne Jabir, ruwa ne ya zo É—auka."

Da mamaki a fuskar ta sosai tace "Ruwa kuma? Yanzu a daren nan?"

A kasalance yace "Wallahi kuwa, ya É—auka ya tafi, na bar mishi fanfon a kunne, dan ya ce Babanshi ya ce sai ya cika musu komai da ake zubawa ruwa gidan."

Ita ma ajiyar zuciya ya sauke tana girgiza kai sanda take ƙoƙarin ɗaura gidan sauro tace "Bawan Allah, to ko da safe fa anan ya ɗibi ruwa."

Girgiza kai yayi cike da jimami yace "Ke dai Allah ya kyauta, amma wannan mahaifi nashi kam sai du'a'i, dan yanzu haka in da kin ganshi wallahi da alama dukanshi ma yayi, dan har fuskar shi ta kumbura, ya ce min kanshi ke ciwo idan ina da magani na bashi, ni kuma na san ba lallai a samu ba a cikin gida, sai dala ashirin na bashi na ce ya si ya sha."

Cike da tausayawa uwar marayu tace" Bawan Allah, Allah ya jiƙan mahaifiyarshi, shi kuma Allah ya wa rayuwarsa albarka."

"Ameen." Ya faÉ—a yana cire takalmin shi ya bi ta kan shinfiÉ—ar ya shiga cikin É—akin, kusa da Ummu ya sake yin zaune yana kallon ta cike da kulawa yace "Kuka kike yi Ummu Kulsum?"

Da sauri ta girgiza kai tace "A'a Baba, dan Allah ka yi haƙuri ka yafe min, na san na ɓata maka rai ɗazu."

Girgiza mata kai yayi yace "A'a Ummu, ni baki min komai ba wallahi, sai dai ina so ki sani cewa, ke da Alhaji Kabir baku dace ba, Ummu Kulsum ni kaina Alhaji Kabir ya haife ni, saboda babban ƴar sa ma ta girmeni nesa ba kusa ba, kenan kinga akwai tawaya sosai idan aka ce a haɗaki aure da shi, ba zaki mori ƙuruciyarki ba Ummu Kulsum, ni kuma abinda bana fata kenan, ina so yadda na reneki cikin kulawa da kyautatawa, na haɗaki da wanda zai san mutumcinki sannan ya dace dake, ta yadda ko bayan raina ruhina zai samu salamar cewa na barki a hannun da ya dace."

Ta gamsu ƙwarai da abinda ya faɗa mata, dan haka ta jinjina kai tace" Nagode Baba, nima dama ban hango abubuwan da kuka hango min bane, kawai dai Naji ina so na aure shi ne saboda kirkinshi da nagartattun halayenshi, amma tunda baku amince b na haƙura."

Zuba mata idanu yayi yace" Ummu, da gaske abinda yasa kike so ki aure shi kenan?"

Jinjina kai tayi tare da kallon shi tace" E Baba, daga gare ku nake jin kuna yabon halayensa da kirkinshi, ni kuma sai naga dama ana son mutum ne don kyawawan halayenshi, sannan ko mutum ya girmeka zaka iya zaman aure da shi indai kana da tabbacin zai girmamaka sannan ya mutumtata iyayen ka."

Shiru yayi na wasu daƙiƙu, sai kuma ya jinjina mata kai yace" Ummu, kin tabbata tsakani da Allah kike son Alhaji Kabir?"

Sadda kanta tayi ƙasa tace" E Baba."

Sai kuma ya sake jinjina kai ya miƙe yace" Shikenan, idan sun sake waiwayarmu da maganar zan faɗa musu ra'ayinki, amma idan sun yi duba da abinda na faɗa musu tun farko na nuna ƙin amincewa ta, to nasan ba zasu sake dawowa ba sai dai ya aiko mana ɗan aike cewa mu bar masa gida."
Chapter 2 · 0% Book details