← Book details Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 168

Sashe 126

Rubutacciya Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Jibril* tunda Ummu ta shigo ya ƙare mata kallo, duk da ba wata shaida dake nuna masa ba matar aure bace, amma dai kuma alamun na nuna mishi kamar bazawara, sai kuma Fahad ya tabbatar masa ta hanyar faɗin sunan suruki da ya yi, dan haka ya ci gaba da ƙare mata kallo da dukkan wani motsin ta.

Kan teburin da ta aje abincin mai kujeru huɗu ta nufa, wanda dole tasa ta raɓa ta tsakiyar hanya da kujerar da Jibril yake, abun ka ga wanda ya san sirri' mace, wanda ya san sirrin duniyanci take ƙamshin nutsatsiyar kulacchar da take anfani da ita da kuma turaren kaya ya dokar masa kai tare da jin wani irin mugun yanayin da ya saka shi gyara zama ya ɗan saci kallon ta, garin haka kuma Ummu dake wuce tana gyara kallabin abayar ta sai kuma ya ji sautin nan na cacas cacasss! Jigida, ya san mecece jigida da kuma sirrinta a jikin mace, hakan yasa ma yake tunanin a cikin turaren da yaji a jikin ta wataƙila ɗayan daga jigidar yake fitowa?

Har Ummu ta dawo Jibril na cikin wani irin yanayi na shauƙi da cin burika akan wannan santalele kuma gonar audigar, cikin farin ciki da raha angayen suka ci abinci, inda Ummi ta bar musu tare da Nabila da Naja'atu suna ta hira.

*RANAR BIKI*

Cike da gajiya da rashin sanin madafa ta ɗaga wayar Fahad da safiyar nan bata san kira na nawa bane ya mata, cikin kaushin murya da kuma zafi zafi Fahad yace "Kinga Ummulele, faɗa min gaskiya zaki kawowa baƙina abincin nan ko kuma a'a?"

A ladabce tamkar wanda ya isa haihuwar ta Ummu tace "Abbuna kayi haƙuri, wallahi ka ga Mujittafa ne ya ke ta ce min gashi nan a hanya amma har yanzu shiru, yanzu haka gani ƙofar gida neman cikin yaran unguwar mu sai na basu kuɗin adaidaita su je su kai."

Cikin ƙufula Fahad yace "Haba jama'a, tun safe ba wanda ya ci komai, gashi Jabir ne yasan can kuma sun tafi tarban wasu baƙin mu, waɗanda kenan duk baƙi ne da ba zasu iya kai kansu can ba, kuma nace zan je sun hana wai bai dace ba, to na barsu ne da yunwa?"

Ɗan shiru Ummu tayi tana sauraren faɗan da yake yi, shi kam dai ai yayi sa'a a rayuwa da duk da dai shekarun su ɗaya amma Allah ya bashi girman da yake iya yi mata faɗa, ya zatayi ita kam? A sanyayr tace" To Abbu ko na zo da kaina na kawo muku? Dan ni dai gaskiya na gaji da ɓata min rai da Mujittafa ke yi."

A sanyaye shima yace" Tun tuni da haka kikayi ma, sai kin zo É—in."

Da sauri jin yana neman kashe wayar tace" To Abbu ina ne gidan?"

A tsanake yace" Gidan Jabir ne."

Saida ta ji wani tuƙuiƙi ya kamata na takaicin da bai sake ta ba har yanzu na abinda yaron nan ya mata sannan ta taɓe baki tace" Ban san ina ne gidan shi ba, kawai ka kwatanta min."

A nutse ya kwatanta mata gidan, sai ta ji ai duk tsohuwar unguwar su ne inda suka taso, kawai dai ƴar tazarar kaɗan ce, a taƙaice ita ma ta amsa da" Sai na zo." Sannan ta kashe wayar ta koma cikin gida, saida ta canza kayan jikin ta dan har ta saka wanda suka dace da manyan tukanen da zasu ɗora a wuta dan girkin rana, sannan ta saka mayafin ta tare da ɗauko kwandon abinci bayan yara sun saka mata manyan kulolin a mota da makulli ta fito da sauri da zuwa yanzu zata dawo.

A kwatancen da ya mata ram ram ta iso sai gata ƙofaro gidan, daga ganin motar da ta san Jabir na hawa kwanakin nan wacce bata san Alhaji da ita ba gata kuma sabuwa ce dal ta faka ta tsaya, a nutse ta fito daga motar tana riƙe gyalen ta da kallon ƙofar gidn tana kula ayyana _"Lallai Jabir, hala Alhaji ne ya msa kyautar gidan nan? Fitsararren yaro."_

Kwandon ta É—auka sannan ta nufi gidan tana kiran lambar Fahad, jim kaÉ—an ya É—aga yace" Yane É—iyar?"

A mugun tausashe tace" Gani ƙofar gidan."

Da sauri yana tasowa dan tarban ta yace" Shigo mu haÉ—e, ina ciki nima."

Ta ƙaramar ƙofa ta shiga tana yin sallamar da ita kaɗai ta ji abar ta, amma Jibril da Yusuf dake farfajiyar ma basu ji ba, saidai suna ganin ta hankulansu suka koma kan ta, a nutse ta gaishe su suka amsa, Jibril dake ta shafar gemu yana kallon ta da fara'a yace "Ta gaban goshin Fahad namu, sannan... Ta gaban goshin duk wani masoyin Fahad."

Kallon shi tayi, ummmm ! Zubin shi dai akwai kamala, kamar yadda daga kallon fuska kuma baka bambamce na ƙwarai da akasin haka, murmushi dai ta mishi saboda ganin Fahad na fitowa tace" Nagode abokin Abbu."

Sai kawai ta raɓa su ta nufi Fahad da tuni ya kai hannu zai karɓi kwandon tare da cewa" Ƴar, ba dai shikenan abincin ba?"

Dariya tayi tace" Abbu kuÉ—i fa ka bayar masu yawa a maka abinci, na baka iya wannan ai kayi shari'a dani, sauran na mota a manyan mazubai yake."

Da dariya Fahad yace" Ki ce sai maza É—auko sauran?"

" Gaskiya." Ta faɗa tana jinjina kai, kwandon ya karɓa zai juya yana faɗin" Ina zuwa?"

Da sauri ta riƙo hannun shi tana faɗin" Abbu dakata, na faɗawa Hajia nan fa tare da kai muke amma bata yarda, gani take ana barin ka da yunwa."

Dariya yayi yana gyara tsayuwar shi da maida hankalin shi kan wayar Ummu da take saitawa tana kiran Hajia a kiran da zasu ga juna kai tsaye, ba jimawa ko Hajia ta É—aga dan dama sun yi da ita zata kira ta, ta na ganin fuskar Hajia da ko kwalli bata shafa ba saboda har yanzu bata kammala ida takabar ta ba tace "To Hajajju, gani ga autan naki, kin ganmu ? Kin tabbata yanzu MaraÉ—i ba babban birnin da autan ki zai gagara haÉ—uwa dani bane?"

Dariya Hajia tayi ta kalli Fahad tace "Autana, ya hidima? An É—aura aure lafiya ko? Ina su Alhaji (Abbu Mukhtar)."

Fahad dake murmushi yace "Duka lafiya lau Mamie, kinga zan kira ku anjima, yanzu zan kaiwa baƙi abinci, su Alhaji kuma suna ɗaya masaukin Abbu (margayi)."

Da gamsuwa Hajia tace "To shikenan, ka ranƙwashe min kan matar nan ta kusan ka."

Da dariya Fahad yace "Mamie Æ´ar tawa ? Tunda na zo nan ita ke bani abinci."

Da mamaki Hajia tace "To? To ina dattijon (Jabir) da na haÉ—aka da shi?"

Murmushi Fahad yayi tare da ɗan waiwayawa bayan shi ya kalli ƙofar ɗakin yace "Yana ciki Hajia, yanzu ya shigo, ai shi wannan oga ne akan taimakon da yake mana, saidai Rabbi ya biya shi, hatta ruwa ya wadatamu da su yadda bama nema mu rasa."

Sai kuma ya jinjina kqi yace "A gaskiya Hajia ta bakin ki, Jabir dattijo ne."

Taɓe baki Ummi tayi tana rayawa a ranta _"Hmmmm! Bak san halin shi bane, wai kamar Jabir ne zai dinga mata rashin kunya, kuma ya ce shi dole malami ne."_

A zahiri kuma Hajia ce tayi murmushi tace" Na san zai iya fiye da haka, shiyasa na msa godiya tun kafin ma ranar ta zo."

Da fara'a Jabir yace" To Mamie, sai na kira."

Sallama sukayi ya shiga ciki yana kallon su Jibril dake ta satar kallon Ummu yace" Kai Yusuf, dan Allah kuje Ummu ta buÉ—e muku ku É—auko sauran abincin nan."

Jibril ne ya fara faÉ—in" Ba damuwa." Sai kuma ya kalli Ummu da ke sallama da Hajia yace" Ran ki shi daÉ—e muje ko? Idan ban takura ki ba fa."

Murmushi Ummu tayi ko ba komai magana da girmamawa ai tana birgeta sosai, kai ita fa ko goba zata siya ka mata magana da ladabi zata iya siye kwandon gobar, amma idan ka mata magana a gatsau haka yadda har hankalin ta bai kwanta ba, to fa gaskiya zata fasa siyan ko É—aya ne tayi tafiyar ta, ai girmama na gaba ma daÉ—i gare shi, hausawa suka ce wai *bin na gaba bin Allah.*!

Haka suka bi bayan ta ta buɗe musu motar suka ɗauko manyan kulolin suka shiga da su, ita kam bata sake shigowa ba a waya kawai ta kira Fahad ta shaida masa ta wuce, amma dan Allah kwanukan nan inji Mama kar komai ya ɓata, godiya ya mata ta wuce abun ta zuwa ta su hidimar.

*Duk* abubuwan dake ta faruwa Jabir da bai jima da shigowa ba yana hangen su ta ƙofa, duk da akwai hayaniya a falon saboda akwai maza dayawa, amma dai hankalin shi na Allah ya sa Maama ba sai ta shigo har ɗakin nan ba, tunda dai ai gashi nan ƙarara Maama ta rage jin tsoron Allah yanzu, gashi kuma ta ƙi ma fahimtar ba daidai take aikataxa ba bare ta sabin ta imanin ta.

Har ta fita yana kallon ta cikin doguwar rigar shadda kalar kore da ya ƙona sosai, sai zaren da aka mata aikin dashi kalar orange haka ma ɗan kwallin ta da takalmi, gashi yau ma dai babu kwalliya a fuskar ta dan aikin da zasu yi yasa take so da anyi sallah azahar zata tafi wajen kwalliya wacce rabon da ta shafa kwalli a idanu ma ta manta, kwalliya kuma mai sunan kwalliya da ta cika duniya zata iya cewa tun haihuwar matar Yaya Luƙman wacce yaron na nan shekarar sa uku da watanni.

Tunda ya ga sun fita da su Jibril bai kawo komai a ran shi ba, sai dai yaji zafi ganin ita ce gaba su suna baya, duk da doguwar rigar ta bata bayyana surar ta ba saboda mai zubin babban riga ce ta maza, alla shi dai akan me za ta shiga gaba? Yana tsaka da wannan tunanin Fahad ya dube shi yace "Dattijo, ina zamu samu manyan farantai?"

Kallon Fahad yayi ba fara'a yace "Me ya sa ba ka tambayi Maama ba?"

Kallon Jabir Fahad yayi yace "E to, d..." Da sauri Aliyu ma da yau duk kai da kawon da shi ake yi yace "Kai ka kira mana sai ka sanar da ita."
Chapter 126 · 0% Book details